2025-04-02@23:05:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2796
«zakkar fidda kai»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare...
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su. Ya kara da cewa, masu garkuwa da...
Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato...
A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar...
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta. Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa. Shugaban ya yi...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da...
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...
Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su. “An sako wadannan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi...
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata,...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin...
Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban...
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman...
An yi jana’izar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda dubban jama’a suka halarta. Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, sun halarci jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi. Basakkwacen da ya yi ridda...
Wani basakkwace, Musa Abubakar, wanda a bayan nan ya yi ridda saboda zullumin ’yan bindiga masu kai hare-hare da ta’adar garkuwa da mutane, ya sake karɓar addinin Musulunci. A ranar Asabar ce mutumin tare da matansa biyu suka sake karɓar addinin Islama bayan ridda da suka yi a kwanan baya. Tinubu zai tafi ziyarar makonni...
A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ƙwazo da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi...
Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki. Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito. Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa...
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time...

Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya ya tube shugaban kamfanin man fetur ta kasa NNPC Mele Kyari, da majalisar gudanarwansa, ya kuma maye gurbinsa ta Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga a safiyar yau Asabar a shafinsa X. Onanuga shugaba ya tube shugaban kamfanin na NNPC da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin...
A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron...
Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe...
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang...
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin...
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa. “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi. Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu. Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne. Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne. Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda...
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar. Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa...
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi. Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti...
A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha Muna kiran Natasha ta...
Ƙungiyar ta Kano Pillars ta tabbatar da hakan a shafinta na X da rubutun “Barka Da Dawowa Koci”. A halin yanzu, Kano Pillars na matsayi na takwas a teburin NPFL, da maki 44 bayan buga wasanni 31. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su. Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya. Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar...
Sanata Natasha Akpoti wadda a kwanan nan Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta. Hakan na kunshe ne cikin wani sakon mayar da martani da Sanata Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook. Muna...
Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi. Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar...
Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi. A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci. Masana harkar man fetur sun yi...
Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a...