2025-04-19@17:05:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 25

«Sanarwar ta»:

    Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya.   Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.   Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima....
    Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya Sanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu. Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu. Sunayen kantomomin ƙananan hukumomin Ribas  
    Ƙungiyar ta Kano Pillars ta tabbatar da hakan a shafinta na X da rubutun “Barka Da Dawowa Koci”. A halin yanzu, Kano Pillars na matsayi na takwas a teburin NPFL, da maki 44 bayan buga wasanni 31. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.  A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar. Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa. Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin. Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan mayar da martani, da karfafa tsarin gudanar da ayyuka masu nasaba, tsakanin ofisoshin sassan majalisar gudanarwar kasar Sin, da karfafa matakan aiwatar da sassan dokar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi. Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana. Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas  Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka. “Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira. “Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar. Kamfanin Dangote...
    Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa. Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare dake karkashin ikon ‘dakarun’yan Houthi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama. Sanarwar ta kara da cewa, “Kowane matakin soja da za a dauka na iya tsananta halin da ake ciki, zai kuma haifar da mummunan tasiri, tare da gurgunta yanayin kwanciyar hankali a Yemen, kana zai kara kamarin kalubalen halin jin kai a kasar.” ‘Yan Houthi dai sun yi barazanar karin kai...
    Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar. A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan.   Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya (FRCN) da kuma gidan talabijin na Najeriya (NTA) Kaduna a ofishinsa da ke Kaduna.   Injiniya Dan-Mulki ya jaddada babban nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ta FERMA na tabbatar da cewa titunan gwamnatin tarayya sun kasance masu kyau domin saukaka zirga-zirga a fadin kasar nan. Ya bayyana muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen yada labarai, domin wayar da kan...
    Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka  wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da  Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar. “Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar  batun biyan mafi karancin albashi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya. Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin. Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo...
    Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
    A kwanan nan ne dai aka gudanar da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU karo na 38, inda aka zabi ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar AU na tsawon shekaru hudu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya taya shi murna a yau 17 ga wata, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da Youssouf, da sabuwar hukumar gudanarwa ta AU. Yayin da yake amsa tambayoyi a gun taron manema labaru na yau, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin tana kallon dangantakarta da AU daga mahanga mai muhimmanci kuma na dogon lokaci. Yana mai cewa “A halin yanzu, zaman lafiya da...
    An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU. An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar. Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49. Dan shekaru 59 da haihuwa, wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Djibouti zai gaji Moussa Faki Mahamat na Chadi wanda wa’adinsa na biyu kan shugabancin kungiyar zai kare a ranar 15 ga watan Maris. Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta AU sun hada da rikicin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango da Sudan da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya...
    Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa “Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96. Za mu ci gaba da riƙe alƙawarinsa na fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci. Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’. Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata. Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya...
    A ranar Lahadi ne mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka bayar da sanarwar dakatar da mai koyarwa, Usman Abdallah mako uku, sakamakon rashin kokarin kungiyar a baya bayan nan a bana da kuma nuna halin rashin hakuri ga magoya bayan kungiyar a lokacin da aka tashi daga wasan da kungiyar ta tashi canjaras da kungiyar Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano. A wata sanarwa da aka fitar a shafin sada zumunta na facebook, kungiyar ta ce kociyan ya nuna halin rashin da’a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ba kuma halayyar da ya nunawa magoya baya ba ta dace ba saboda a matsayinsa na mai koyarwa dole ne sai...
    Kasashe 79 na duniya sun yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kakabawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC takunkumi, suna masu cewa matakin na raunana tsarin dokokin kasa da kasa. Wadannan kasashen  da suka hada da Canada, Jamus, Faransa, Afirka ta Kudu da kuma Mexico, a wata sanarwar hadin gwiwa na cewa irin wadannan matakan na kara barazanar rashin hukunta masu manyan laifuka. Har ila yau a cikin sanarwar, kasashen 79 sun jaddada cewa takunkumin da Amurka ta kakabawa kotun ta ICC na iya yin illa ga sirrin bayanan da suka shafi wadanda abin ya shafa, da shaidu da kuma jami’an shari’a, wadanda ‘yan asalin wadannan kasashe ne. Sanarwar ta zo ne...
    Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da naɗa sabon shugabanta, Farfesa Adamu Ahmed. Majalisar Gudanarwar jami’ar ce ta zaɓi Farfesa Adamu Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Kabir Bala. An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo An sanar da zaɓen Farfesa Adamu da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar wannan Larabar a yayin zaman Majalisar Gudanarwar jami’ar wanda Mahmud Yayale Ahmed CFR ya jagoranta. Farfesa Adamu Ahmed dai malami ne a sashen nazarin tsara birane na jami’ar ta ABU. Ya taɓa riƙe muƙamin Darektan Cibiyar Bunƙasa Jami’ar kuma a yanzu shi ne Uban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano.
    Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
    Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta tsaurara matakan sanya idanu akan hanyoyin shigowa ƙasar sakamakon sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Uganda. NCDC ta gargaɗi ’yan ƙasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda saboda ɓullar cutar Ebola da aka tabbatar a ƙasar. EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum Shawarar NCDC na zuwa ne bayan sanarwar Ma’aikatar Lafiya ta Uganda a ranar 30 ga watan Janairun 2025 kan ɓarkewar wani nau’in cutar Ebola mai suna Sudan a gundumomin Wakiso da Mukono da kuma Mbale na ƙasar. Ko da yake sanarwar NCDC ta ce ba a samu wani rahoto ba game...
    Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje. Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf kan zargin almundahana. A safiyar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, inda bayan an karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta aikata laifin. Daga nan ne lauyansa O.I Habeeb, ya buƙaci umarnin kotu na tsare shi a ofisoshin EFCC zuwa lokacin zai shigar da buƙatar beli. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe...
    Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko.   CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka hada kai da masu ruwa da tsaki don inganta tsaro a lokacin taron.
۱