2025-02-22@15:22:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 958
«Gwamntin»:
Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwan daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas. Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don...
Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa...
Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25 yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A...
“Babban shugaban sojoji da Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro (NSA) suna aiki ba dare ko rana wajen tabbatar da wannan matakin, kamar yadda kuke gani muna sanya kumaji ga dukkanin rundunoni. “Sannan, an janye takunkumin hako ma’adinai a Zamfara, sannan wannan dalilin ne ya sanya muke ganawa a yau domin duba dukkanin bangarorin,...
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da...
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ci gaba da kokarin da rundunar ‘yansandan Jihar Imo ke yi na dakile ayyukan ta’addanci a jihar, jami’an shalkwatar sashen Okigwe tare da hadin gwiwar mazauna unguwar Ogii a ranar 3/02/2025, sun kama wasu mutum uku da aka samu da kokon mutum, kaza da fararen kaya a kan...
Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta...
Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya wa al’ummarta kudin wutar lantarki a kowane wata. Shugaban Hukumar, Alhaji Bishir Sabi’u na cewa nan gaba za a kammala aikin layin da aka ware musu na musamman na Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (TCN). Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa karamar...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa sun sabawa ka’idojin dokokin kasa da...

Tsohon Ministan Yakin Isra’ila Ya Ce Sune Suka Ba Da Umarnin Kashe Fursunoninsu Da Ake Tsare Da Su A Gaza
Tsohon ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ba da umarnin sojojinsu su kashe fursunoni yahudawa da masu tsaronsu a Gaza Tsohon Ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da aka kora Yoav Gallant a jiya Alhamis ya yi bayani kan matakan da sojojin mamayar Isra’ila suka...
Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi...
Wannan ya hada da kilomita 65 daga Legas zuwa Ogun da wani karin da zai tashi daga Kalabar ta Akwa Ibom, wanda titin zai ginu a karkashin ‘Engineering, Procurement, and Construction’ (EPC) da tsarin za su kula da shi na tsawon shekaru goma bayan ginawa. Majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 470.9 domin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun...
Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan...
A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe,...
Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki kan hanyoyin da za su yaki ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya ta hanyar amfani da darussan da aka koya a wajen wani bada horo da ya gudana a Sakkwato. Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana haka a Sokoto a wajen...
Gwamna Sani ya bayyana zargin da kungiyar ta yi a matsayin maras tushe, yana mai jaddada cewa “Mafi yawan ‘yan siyasar da ke irin wadannan kalamai na iya zama suna magana da kansu ne kawai,” in ji shi. “Mun kasance a cikin jam’iyya daya a wani lokaci, kuma dole ne in ce na yi mamakin...
Akalla manoma da ma’aikatan gona 1,000 ne gwamnatin jihar Kwara ta horas da su akan aikin gona da sarrafa ragowar amfanin gona don inganta amfanin gonakin da makiyaya ke amfani da su. Da yake jawabi a karshen horon, a Ilorin, wanda Synergy Impact Limited ya shirya, tare da tallafin gwamnatin tarayya, bankin duniya da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama. A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar...

Shugaban Kasar Amurka Ya Sanya Hannu A Dokar Yin Tir Ta Kotun ICC Saboda Sammacin Kama Natanyahu Da Tayi
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya rattaba hannu a kan doka wacce ta yi allawadai da kutun kasa da kasa ta ICC saboda laifin fidda sammacin kama abokiyar Amurka firai ministan HKI da ta yi, sanadiyyar kissan kiyashin da ya yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump ya na...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa taron G20 a kasar Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ronald Lamola ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu na cewa “kasarmu yentacciyar kasa ce, kan tsarin...
Babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Burgediya Janar Hussain Salami ya bayyana cewa a dai dai lokacinda manya-manyan kasashen duniya suke amfani da takunkuman tattalin arziki, mafi muni a kan wasu kasashe, a lokacin ne kuma, dakarun IRGC suke yunkuri don kare kammu daga makiya. Sannan samar da ci gaban da muke bukata don...

Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Kasarsa Bata Neman Yaki Sannan Bata Nemam Mallakar Makaman Nukliya.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen duniuya, don haka ne ta haramtawa kanta mallakan makaman nukliya wanda yake kissan kare dangi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi...
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025. A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON...
A ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Adamu, ta ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji. An ƙaddamar da tsarin ne a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Gombe. Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya An tsinci gawar...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya...
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata matsin lamba kan kasar ta Donald Trump za ta cutura. Iran dai ta caccaki matakin da shugaban AMurka ya dauka ind aya sanya hannu kan umurnin sanya sauraren matakn matsin lamba kan Tehran a game da shirinta na nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana a wani sako...
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa. Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun...
Kwamitin Sake Duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Majalisar Wakilai, ya bayar da shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi 31 domin ƙara yawan jihohin ƙasar nan daga 36 zuwa 67. Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ne, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya jagoranta a ranar Alhamis....
Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO. Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya. Adorni ya ce, ” ‘yan...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce. Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya...
Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza. Umarnin Katz ya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump na tilastawa Falasdinawa Gaza barin zirin da kuma sanya Amurka ta mamaye yankin da yaki ya lalata. “Na umurci IDF da su shirya wani shiri...
Ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT reshen Jihar Ebonyi ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ƙananan hukumomi bakwai na jihar sakamakon rashin biyan albashin watanni. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da: Ebonyi, Edda, Ezza South, Ezza North, Ivo, Ishielu da Ƙaramar Hukumar Ohaukwu. Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar...
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas. Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh...
Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka...
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ishaq Yunus Almadany, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin 44 Army Reference da ke Kaduna. An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti Tinubu ya sauke shugabar Jami’ar Abuja, ya yi sauye-sauye a jami’o’in...
An tsinci gawar mai shari’a Azuka, Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Anambra. An gano gawar Azuka da aka sace a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2024 a kan gadar 2nd Niger Bridge, a cikin Anambra, ranar Alhamis. Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa Yadda matar...
A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi. A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da...
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta hana ‘yan wasan da sukai sauyin jinsi (transgender) shiga wasannin mata. Ya bayyana cewa wannan dokar zata kawo ƙarshen “cece ku ce da ake yi kan wasannin mata” tare da tabbatar da kariya ga ‘yan wasa mata daga fuskantar rashin adalci. A...
An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya,...
An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya,...
Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan...