2025-03-12@06:43:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 171

«Hamayya»:

    Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sha nanata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare fiye da kima, kuma Amurka na neman yin ciniki bisa adalci da daidaito. Sai dai kuma, da yake mayar da martani a yau Litinin 10 ga watan Maris, yayin wani...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari. Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma...
    Rahotanni sun bayyana cewa, ya kammala yunkurin komawa jam’iyyar SDP.   Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na nan dan jam’iyyar PDP na gaskiya.   Yayin da yake bayyana rahotannin a matsayin “karya”, ofishin...
    Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci...
    3- Rubewar hakora 4- Barazanar kiba 5- Barazanar ciwon zuciya da jijiyoyin jini 6. Barazanar ciwon siga (nau’i na biyu) 7- Haddasa kumburin jiki 8- Barazanar ciwon kashi da gabbai (rheumatoid arthritis) 9- Ciwon daji ko kansa da dai sauran makamantansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya. Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na...
    Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin...
    Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar. A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar...
    A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon fashewar wata tankar mai da ta tashi a Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata filayen noma a cikin unguwanni. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƙaramin Rami da ke ƙaramar hukumar Mashegu da misalin ƙarfe 6:30...
    An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar. Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a. SOHR...
    Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Faransa biyo bayan kalaman Emmanuel Macron na baya-bayan nan game da kayyade makaman nukiliya. Moscow ta dauki wadannan kalamai a matsayin barazana kai tsaye, yayin da Paris ke kare matsayinta ta hanyar jaddada bukatar kare Turai, Wanda ya nuna yadda ake samun rashin jituwa sosai kan...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban...
    Ban da wannan kuma, muhimmancin wannan adadi na bayyana a bangaren iyawa da hazikanci na dan Adam. Rahoton ayyukan gwamnati na bana ya ambaci wannan abu sau da dama, ciki har da yawan amfani da na’urori dake iya sarrafa dimbin bayanai da hazikancin koyo mai zurfi da daidaita dimbin ayyuka masu sarkakiya, da kuma iyakacin...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana...
    ’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda. Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari. Da...
    Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata —...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata —...
    A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga...
    Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu  a kasar. Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen  50...
    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar...
    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a...
    Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba. Badr Abdul’adhy,  ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar...
    Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in...
    Kakakin Majalisar dinkin MDD Stephane Dujarric ya bada sanarwan cewa yana makaranta a Gaza fiye da 100,000 suka fara karatu a makarantu a yankin a ranar 23 ga watan Fabrayrun da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’in MDD yana fadar haka a jiya Alhamis kwanaki huda da fara karatu...
    Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin...
    Kasar Sin ce ke da kusan kashi 30 cikin 100 na karuwar tattalin arzikin duniya a bara, wanda ya yi tasiri matuka ga tattalin arzikin duniya. Gudunmawar da kasar Sin ta bayar ta sake tabbatar da matsayinta na kan gaba a fannin tattalin arziki, kuma ta nuna muhimmiyar rawar da take takawa wajen ciyar da...
    Sanata Natasha Akpoti ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio da neman yin lalata da ita. ’Yar Majalisar Dattawa daga Jihar Kogi ta bayyana cewa mijinta ma shaida ne a kan yunkurin Akpabio ne yin lalata da ita. A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a,...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.   Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.  ...
    Wadanda Suka Yi Nasara Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo,...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.   Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.   Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da...
    Taron lakca karo na 22 na kasar Sin da aka yi jiya Laraba a birnin Alkahiran Masar, ya hada malamai Sinawa da na kasar da jami’ai sama da 200, inda suka tattauna don gane da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika, wajen daukaka zamanantar da kasashe masu tasowa. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika da...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar. Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira. Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Kotu...
    Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa  gabashin Afirka zai zama  sama da sauran  yankunan nahiyar a cigaba. Ana hasashen cewa  a cikin  rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga (...
    Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a...
    Sarkin Moroko, Mohammed na shida, ya buƙaci ƴan ƙasar su kaurace wa layya a bana wanda al’ummar Musulmi masu hali ke yanka dabobbi, musamman rago a matsayin nuna godiya ga Allah bisa rayawa da ni’imomin da ya yi wa bayinsa.Sarkin ya ce sanarwar tasa na da alaƙa da karancin raguna da ake fuskanta a ƙasar...
    Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a cikin dare inda suka ƙona wuraren ibada da gidaje da makarantu da shaguna a ƙauyen Kwapre da ke yankin Sabuwar Yadul a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Gabanin Sallar Isha’ a ranar Talata ne mayaƙan suka far wa yankin da hari, inda suka yi ta cin karensu...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ya hori Kiristoci masu niyyar ziyarar su zama jakadu na gari tare dayin addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba idan sun isa can.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bankwana da masu ziyarar su 162 da zasu tashi zuwa Isra’ila.   Gwamnan ya jaddada muhimmancin da’a a...
    Iyalan Malcolm X, bakar fata fata kuma daya daga cikin jagororin  musulmin Amurka da aka kashe a ranar 21 ga Fabrairun 1965, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya bayyana bayanan da ke da alaka da kashe shi, kamar yadda shafin Arabi 21 ya ruwaito. Iyalan Malcolm X sun gabatar da bukatar ne a...
    Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga  ma’aikata da...
    Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Trump ta kasar Amurka tana tsara wasu tsauraran matakan kayyade samar wa kasar Sin sassan na’urorin hada laturoni na semiconductor, da kara matsin lamba ga kasashen kawacenta, tare da bukatarsu da su tsaurara dabaibayi a kan sha’anin samar da fasahar matattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin....
    Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi  hadin kan al’umma don gina kasa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kaucewa cin hanci da rashawa ba. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC)...
    Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana...