2025-03-25@13:20:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2464
«Dokar ta baci»:
Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za...
Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa...
Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon...
Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar....
Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar...
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri...
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri...
“Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya. “Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi. Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba...
Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan...
Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a...
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mutum 2,000 sabbin kamuwa da cutar SIDA duk rana a faɗin duniya. MDD ta ce tana wannan gargaɗi ne sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin ƙasashen duniya ƙarƙashin Hukumar ta USAID. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a...
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran fursunonin da suka tsere. Haka kuma, an buƙaci dangin waɗanda suka tsere da su mika kansu ga hukuma domin guje wa hukunci mai tsanani. Wannan ba shi...
Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun...
Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai...
Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti...
Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci. “Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza. “Ba abinci, ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam. A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin. Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan...
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon...
Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota. Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin. Matasa...
“Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida. Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama...
Wasu fusatattun matasa sun daka wawa kan kayan abincin tallafin azumi da ɗan Shugaba Nijeriya, Seyi Tinubu zai raba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa bai kai ga zuwa jihar ta Gombe ba, amma kayan abinci da zai raba tuni sun isa jihar. Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar...
Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu...
Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa zai iya...
Babban kamfanin fasahar nan na Amurka wato Apple, ya sanar da shirinsa na zuba jarin da ya kai kudin Sin yuan miliyan 720, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 100.31, a fannin samar da makamashi mai tsafta da ake iya sabunta amfani da shi a kasar Sin. Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Litinin din nan,...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; An kai hari nau’i biyu, da ya hada amfani da motar take mutane da kuma bude wuta daga bindiga. Harin da aka kai a kusa da yankin “Yukna’am Iliyat” dake gabashin garin Haifa, ya yi sanadiyyar halakar wani dan share wuri zauna da kuma jikkata wani guda daya....
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar...
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba. Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba. A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin...
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan sadaukarwarsa, da gaskiya, ...
Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace. A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye...

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata...
A cewar takardun kotun, gwamnonin suna neman a bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasa ya zartar ya saɓa wa sashe na 1 (2), 5 (2), da 305 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Sun kuma kara da cewa, shugaban kasa ba shi da wani iko ko kadan na dakatar da...
Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun maka Shugaba Bola Tinubu a Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara. Gwamnonin sun garzaya kotun ne domin neman fatawa game da abin da sashe na 305 na kundin mulkin ƙasar ke nufi. Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha Juventus za ta...
Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta bai wa Majalisar Dattawa haƙuri. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Natasha ta ce tana na kan batunta, kuma ba za ta taɓa bai wa majalisar haƙuri a kan gaskiyarta ba. Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa...
Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal...
Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke...
Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin. Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya Mista Fanwo...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sake farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu da aka daɗe da watsi da ita domin bunƙasa noman rani da nufin samar da wadataccen abinci a Kudancin Borno da ma Jihar ta Borno gaba ɗaya. Zulum ya yi wannan alkawarin ne a yayin wata ziyarar...
Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar...
Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi. Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan...
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana...
Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23...
Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU:...