2025-02-22@07:19:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1142
«fina finan kasar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka kaddamar da munanan hare-hare a kan sansanin Jenin sannan wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden bama-bamai kan gidajen Falasdinawa. A gefe guda kuma, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun gudanar da arangamar da sojojin mamayar, a sansanin Askar da ke gabashin Nablus. Yayin da a birnin Nablus aka yi artabu mai tsanani tsakanin ‘yan gwagwarmayar na Falasdinu da sojojin mamayar Isra’ila. A halin da...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya kuma ce, kudin da Sin ta kashe a fannin tsaron kasa a bayyane yake, kuma yana da ma’ana da kuma dacewa. Game da hadin gwiwar Sin da Rasha, Guo Jiakun ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu bai shafi wani bangare na uku ba, kuma wani karin bangare ba zai yi tasiri kan hadin gwiwar ba. Bugu da kari, game da batun Amurka za ta kara...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48. Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Hotoro. Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano A cewar Hukumar FRSC, haɗarin ya rutsa da wata motar tirela ƙirar DAF ɗauke da kayayyaki da fasinjoji. Bincike na farko ya nuna cewa direban ya yi tuƙin ganganci saboda gudu wanda hakan ya sa motar ta kauce hanya ta afka ƙarƙashin gadar. Rahotanni sun...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya. Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya....
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci Birtaniya cikin shekaru 10, kuma karon farko da Sin da Birtaniya suka gudanar da muhimmiyar tattaunawa cikin shekaru 7, lamarin dake nuna kudurin bangarorin biyu na ci gaba ingantawa da daidaita dangantakarsu. 2027: Ganawar Kwankwaso Da Aregbesola Ta Haifar Da Cece-kuce A Fagen Siyasar Nijeriya Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9 Yayin taron, Sin...
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia domin halartar zaman taro karo na 38 na shugabannin ƙasashen ƙungiyar Afirka ta AU. Shugaban wanda ya sauka a birnin Addis Ababa a daren ranar Alhamis ya samu tarba daga mataimakin shugaban kula da harkokin ƙasar Ethiopian, Eshetu Legesse da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar da kuma mai kula da ofishin jakadancin Najeriya da ke Ethiopian, Ambasada Nasir Aminu. Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Daga baya Ambasada Tuggar ya yi wa shugaba Tinubu bayani kan taron da kuma wasu nasarorin diflomasiyya da ƙasar ta samu, zaman da ya kai har misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren Juma’a. Daga...
Cibiyar Ilimin Mata Ta Shirya Wa Sarakuna Da Malamai Taron Inganta Karatun Mata A Kaduna
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa “Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96. Za mu ci gaba da riƙe alƙawarinsa na fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci. Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya...
Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da...
Wasu fursunoni uku da ke tsare a gidajen yari daban-daban sun lashe Gasar Musabakar Al-Kur’ani da aka gudanar a Jihar Kano. Fursunoni sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shinrya a matsayin wani bangare na tsarin ilimin fursunoni. An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al’umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan yari. Mai magana da yawun hukumar gidajen yari a Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari. Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya Ya bayyana cewa furunan da ya lashe...
Duk da cewa, ana kara samun yin nomansa da yawa, ana kuma ci gaba da samun karancinsa, musamman saboda yadda al’umma ke kara bukatarsa. Kamar Ban Ruwa Nawa Bishiyar Dabino Ke Bukata? Dabinon da aka shuka, bai cika bukatar a dinga yi masa ban ruwa bayan an shuka shi ba, musamman a lokacin kakar damina. A Wane Yanayi Dabino Yake Girma? Dabino ya fi yin girma a yanayin zafi, haka nan kuma ya fi yin kyau a kasar noma ta kasar Amurka da ake samun rana mai zafi. Kamar Zufin Rami Nawa Dabino Ke Bukata? Yana girma a zurfin ramin da ya kai kafa daya zuwa kafa sha daya tare kuma da santi mita daga talatin zuwa arba’in da biyar,...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya. Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar. A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don...
Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa. Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu. Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu. Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa. An karvo hadisi daga Anas khadimin Manzon...
Jami’ar Tarayya ta Lafia ta yi bikin rantsar dalibai 8,000 da suka sami gurbin karatu a sassan 76 a tsakanin tsangayoyin jami’ar 12. Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya sake jaddada matsayar hukumar a kan duk wani nau’i na rashin da’a da kuma shiga kungiyoyin asiri. Shugaban jami’ar wanda mataimakin shugaban jami’ar na sashen koyarwa, Farfesa Alemchi Chuku ya wakilta ya ci gaba da cewa basu da hakuri ga duk wani nau’i na rashin da’a kuma za su yi kakkausar suka ga munanan dabi’u. Ya kuma bukaci sabbin daliban da su mutunta juna da kuma ma’aikatan jami’ar da malamai na jami’ar domin ganin zamansu ya kasance mai amfani. “Ba...
Ana fargabar mutane da dama sun rasu bayan wata tirela ta murƙushe su a Gasar Muhammadu Buhari da ke yankin Hotoro a a Jihar Kano. Tirelar ta kife ne bayan da ta kwace a ƙarƙashin gadar, a hanyarta ta zuwa Kudancin Najeriya daga Yankin Arewa maso Gabas. Wani ganau ya bayyana cewa kimanin mutane 20 da kaya ne ke cikin motar a lokacin da ta kife, inda wasu daga cikinsu suka rasu suka jikkata.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...
Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar. Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a hedikwatar Hukumar da ke Ilorin. Ta ce matakin zai hada da inganta ababen more rayuwa, samar da lantarki ta amafani da hasken rana, da samar da wuraren zama na ma’aikata, da samar da ruwan sha da samar da kayan aikin asibiti na zamani a duk wuraren da ke amfana da cibiyoyin kiwon lafiya na farko. Farfesa Elelu ya bayyana cewa shiga tsakani na...
Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen. Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ta bayyana cewa, Dakta Abubakar Labaran ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu sosai wajen kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da niyyar ganin ba macen da ta mutu a lokacin haihuwa. Ya yi karin haske kan gyare-gyaren da aka...
Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar. Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), ofishin kula da magunguna masu muhimmanci, da gidauniyar REDAID Nigeria Foundation., a Jalingo. Danburam ya bayyana cewa, wani bincike da aka yi kwanan nan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 18 a kananan hukumomin Ardo-kola, Bali, da Takum, ya nuna cewa kayan gwajin cutar kanjamau sun kare a cibiyoyin. “Rashin kayan gwajin zai kawo cikas ga kokarin...
Makiyaya sun koka bisa abin da suka kira tsangwama da tsana da wasu manoman tabar wiwi ne suke nuna musu tare da yi musu barazanar ƙone gidajensu a inda suke zaune shekaru aru-aru. Makiyaya Fulani sun yi ƙorafi ne bayan manoman tabar wuri sun kafa musu ƙahon zuƙa a inda suke zaune a yankin Oja-Badun da ke Ƙaramar Humumar Eleyele a Jihar Oyo, daura da garin Ogumaki na Jihar Ogun. Shugaban Fulanin yankin, Alhaji Muhammadu Wakili ya shaida wa Aminiya cewa, jagoran manoman tabar wiwi a yankin ya sa wa Fulani makiyayan karan tsana, bayan da suka bai wa jami’an tsaro bayanan cewa, suna noma tabar wiwi a yankin. Ya ce lamarin ya kai ga ’yan sanda sun kama yaran...
Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace. Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata....
Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na kwamitin kudi da manufofin gwamnatin tarayya (FGPC) da ya gada, da kuma Naira biliyan 4.04 cikin 51 na ayyukan gaggawa (EIPs) da ya gada daga gwamnatin da ta shude, adadin da ya kai Naira biliyan 51.96. Shiyyar Arewa maso yamma ta biyo bayansu da ayyuka 44 da aka yi watsi da su, wanda jihar Zamfara kadai ke da ayyuka 33 da ba a kammala ba....
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya kasarsa suna neman murkushe al’ummar kasar ta hanyar takunkumi da barazana. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da masana da masu fada aji na lardin Bushehr da ke kudancin kasar a ranar Alhamis , inda ya ce “Makiya suna son mu ulakanta a gabansu ta hanyar takunkumi da barazana, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, kuma za mu magance matsalolinmu ta hanyar dogaro da jama’a.” Ya yi kakkausar suka kan irin matakan da Amurka ke dauka a kan Iran wadanda suke karo da juna, yana mai cewa shugaban Amurka Donald Trump na ikirarin cewa yana son tattaunawa da Iran amma a lokaci...
Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu. Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa. 2003. Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau. 2007 Sai dai tun ba a je ko’ina ba,...

Amurka ta kakaba wa babban mai shigar da kara na kotun ICC takunkumi kan binciken laifukan yakin Isra’ila
Amurka ta kakaba takunkumi kan babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da binciken da kotun ta ICC ke yi kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra’ila a Gaza da sojojin Amurka. Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakabawa Karim Khan takunkumi a matsayin martani ga umarnin shugaba Donald Trump na ranar 6 ga watan Fabrairu, wanda ya bukaci a sanya masa takunkumi. Trump ya yi iƙirarin cewa kotun ta ɗauki “haramtakan da ba su da tushe balle makama” akan Amurka da Isra’ila. Kamar yadda aka ba da umarnin, shugaban na Amurka a yanzu yana da iko mai yawa na daskare kadarorin da kuma sanya takunkumin tafiye-tafiye kan ma’aikatan ICC da iyalansu. Za...
Manyan jami’an Philippines sun sake ikirarin shirin sayen makamai masu linzami dake cin matsakaicin zango na Amurka tare da hada su da batun tekun kudancin Sin. Hakika matakin na Philippines ya damka muradun kasar na tsaro a hannun kawayenta na yammacin duniya. Dabarar Philippines ta dogaro da kasashen yamma ba za ta samar da tsaro a kasar ba, sai ma akasin hakan. Saboda jibge makamai masu linzamin ya shafi tsarin tsaro na kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN. A daya bangaren, Philippines na yunkurin cin gajiyar tekun kudancin Sin ta hanyar samun goyon baya daga kasashen dake wajen yankin, inda take ci gaba da takala da tada rikici da ma amfani da batun a matsayin wata dama ta...
Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA). A duk duniya, OCHA, wacce ke kula da CERF da Asusun Kula da Ruwa na Kasa (CBPFs) irin su Asusun Ba da Agajin Gaggawa (NHF), tana jagorantar matakai don taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance annoba kamar ambaliyar ruwa, fari, da kwalara. A watan Oktoban 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 domin a kara kaimi wajen magance ambaliyar ruwa da kuma magance muhimman bukatu a jihohin Borno da...
An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara. Kana an kalli liyafar ta talabijin har sau miliyan 189, karuwar kaso 12 idan aka kwatanta da bara. Baya ga haka, kallon liyafar kai tsaye ta kafofin zamani, ya kai sau miliyan 270, karuwar kaso 47 idan aka kwatanta da bara. A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke...
“Ba wai kawai sun fatattake su ba ne, sun kwace makamansu, kuma tun a wancan lokacin, har yanzu, zai yi wuya ka ji wani labarin mahara a Tafawa Balewa, don haka, shawo kan kalubalen tsaro, dole sai an saka duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin lamarin. “Tsammanin sojojin Nijeriya, ‘yansanda, ko DSS, za su kare kowane dan Nijeriya ko kowace gwamnati, Hakan ba zai yi wu ba,” in ji shi. Ajayi ya kara da cewa, dole ne kasar ta samar da matakan tsaro domin rage nauyi a kan tushen tsare-tsaren tsaron kasa.
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka shafi huldar kasa da kasa ga shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta. Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin. Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025 Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ya ce Adesola ɗaliba ce da ke ajin farko (ND1) a Sashen Koyon Aikin Jarida na makarantar. A cewarsa, tana kan ɗan acaba domin zuwa makaranta lokacin da babbar motar ta yi awon gaba da babur ɗin a kusa da kofar shiga makarantar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta. “Da muka samu labarin, tawagar makaranta da suka haɗa da shugaban tsaro...
Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Amince Da Tiriliyan 54.9 Kasafin Kuɗin 2025
Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 wanda ya kai Naira Tiriliyan 54.9. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya gabatar da kasafin kuɗin, inda aka duba shi dalla-dalla kafin a amincewa da shi. Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe A majalisar wakilai, ’yan majalisa sun yi nazari kan kasafin kuɗin mataki-mataki kafin su amince da shi a ranar Alhamis. Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ne, ya gabatar da shi a zaman majalisar. Bayan tattaunawa da kwamitocin majalisar, an kaɗa ƙuri’ar amincewa da kasafin kuɗin ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen. Sabon kasafin kuɗin ya ƙunshi...

Malaman Yahudawa Fiye Da 300 Sun Rattaba Hannu Akan Takardar Kin Amincewa Da Shirin Donald Trump A Yankin Gaza
Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan. Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da...
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki. Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025, sakamakon rashin biyan mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da shugabannin ƙananan hukumomi suka yi. An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf Shugaban Ƙungiyar NUT reshen Abuja, Kwamared Mohammed Shafas, ya bayyana cewa ƙungiyoyin sun yanke shawarar sake komawa yajin aikin ne saboda gazawar shugabannin ƙananan hukumomi shida...
A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci...
Kwamandan sojan na Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
Babbar Kotun Jiha ta 5 a Gombe, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a A.M. Haruna, ta yanke wa wani matashi mai suna Abdullahi Suleiman hukuncin sare masa hannu, bisa samunsa da laifin sare hannun wani yaro mai suna Khalifa Abubakar, ɗan shekara 14 da adda. Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, shekarar 2022, a garin Moddibo da ke Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba, a jihar ta Gombe lokacin wani bikin aure da ya rikiɗe ya koma rikici da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da angon ya kori duk wanda ke wajen saboda hayaniyar da ta kaure. Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ A lokacin fitar...
Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi. Yusuf, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce an shirya masa tuggu ne saboda dalilan siyasa. Da yake magana yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje, ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama,...
Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi. Yusuf, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce an shirya masa tuggu ne saboda dalilan siyasa. Da yake magana yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje, ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama,...

Ranar Kafar Rediyo ta Duniya: Minista Ya Buƙaci Gidajen Rediyo Da Su Faɗakar Da Jama’a Kan Sauyin Yanayi
A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli. “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.” Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga...
Alƙalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aikewa wanda ake ƙara takardar umarni ta wasu hanyoyin sannan ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
Mutanen Najeriya suna bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa. Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da Giga 15, akan Naira 6,000 bayan da a baya take naira 2,000 ( wato daga dala 1.33-3.99) da hakan yake nufin cewa an rubanya farashin sau uku. Shi ma kamfanin Airtel ya kara yawan kudaden cajin nashi da kaso mai yawa. Wannan Karin da kamfanonin su ka yi, ya bakanta ran masu amfani da su, musamman a wannan lokacin da ake fama da yanayi mai...
An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano. Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi. Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin. Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: ...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati. Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan yara 220 da ke karɓar albashi a matsayin ma’aikatan gwamnati. Gwamna Lawan Ya Shaidawa Bankin Duniya Cewa Sun Yi Nasarar Yakar ‘Yan Bindiga A Zamfara Babu Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Tsarinmu – Gwamnan Zamfara Rahoton kwamitin ya tabbatar da cewa an tantance ma’aikata 27,109, yayin da 2,363 suka kasance ma’aikatan bogi, 1,082 sun dace su yin ritaya, 395 na aikin kwantiragi, 261 ba su...
An shiga ruɗani bayan da wasu sojoji sun lakaɗa wa wasu ’yan sanda da ke bakin aiki duka a Ƙaramar Hukumar Okpe da ke Jihar Delta. Rikicin jami’an tsaron ya samo asali ne bayan ’yan sanda sun yi kamen wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. ’Yan sanda sun tsare motar matasan ne a yayin wani samame, inda suka kama ɗaya daga cikinsu da loud da wiwi, bayan sauran sun tsere. Suna tsaka da tafiya da shi zuwa ofis ne suka bi ta wani shigen bincike na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, suka umarce su da su sake shi. Bayan ’yan sandan sun ƙi amincewa suka nemi a bi ƙa’ida ba ne, rikici ya ɓarke a tsakaninsu. A...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take da shi shi ne abin da ake magana a kai a yau, kawayen juyin juya halin Iran suna alfahari da shi, yayin da makiyan Iran suke kara shiga cikin tsoro. A ganawarsa da safiyar yau Alhamis tare da tawagar malamai, kwararru da jami’ai na masana’antar tsaron kasa, Jagoran juyin juya halin ya dauki ranar 22 ga watan Bahman a matsayin biki mai girma da tarihi...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karbi bakuncin tawaga daga kasar Saudiyya karkashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata shugaban hukumar Saudiyya mai kula da ciyar da Alhazai. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta zo ne domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da dansa ya rasa. Sheikh Fallata ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu. Tawagar ta kuma yabawa tare da karrama Gwamna Namadi bisa kulawa da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar Alhazai. A cewar tawagar, jihar Jigawa ta yi fice mai ban sha’awa a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jiha Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yabawa tawagar bisa karrama gwamnan jihar ta...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shiga Tattaunawa Karkashin Matsin Lamba
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da...

Kungiyar Hamas Ta Bukaci Al’ummar Duniya Ta Goyi Bayan Al’ummar Falasdinu Kan Batun Neman Korarsu Daga Kasarsu
Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a duk fadin duniya da su fito domin gudanar da gagarumar zanga-zanga da tarukan goyon bayan al’ummar Falasdinu gami da hadin gwiwa a dukkanin birane da wuraren taruwar duniya, domin jaddada yin watsi da yin Allah wadai da shirin korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Laraba ta ce: Ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi masu zuwa...
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula, mutane da dama suna gudun hijira da kuma samun karuwar matsalolin bukatun jin kai. Tondlana ya nuni da cewa: Akwai matsalolin tsaro a Sudan saboda hau-hau-hawar farashin kayayyakin bukatu saboda rashin zaman lafiya a kasar. Dangane da yanayin yunwa da aka shelanta a wasu yankunan, ya yi gargadin cewa lamarin na kara ta’azzara saboda fadan da ake fama da shi a yankunan da suka hada...
Rundunar sojin saman Ukraine, ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hare-hare cikin dare. Hare-haren sun fi ƙamari a yankunan Odessa da Kharkiv, a cewar sojojin. Rundunar sojin saman ta kuma ce ta samu nasarar kare wasu hare-haren daga ciki, yayin da ta tabbatar da kakkaɓo 85 daga cikin jiragen. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Nato ke taro a birnin Brussels, inda ake sa ran batun yaƙin Ukraine ne zai mamaye agjandar taron.
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana kokarin samar da sauki da kuma tsarin zuba jari mai inganci wanda zai iya karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje da na cikin gida zuwa jihar. Wakilin Gwamnatin jiha kuma shugaban karamar hukumar Wamako Alh. Umar Ahmad Dundaye ya bayyana haka ne a wajen rabon magunguna da kamfanin siminti na BUA ke gabatarwa a kowace shekara ga asibitocin al’umma goma sha shida da ke yankin. Ya ce gwamnatin jihar Sokoto tana karfafa duk masu zuba jari da ke da alaka kai tsaye ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar. Ya ce gudunmawar BUA a fannin kiwon lafiya na jihar na daya daga cikin alfanun da jarin jihar ke...
Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025. A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka hada da wasu manyan ‘yan ta’adda. Ta ce aikin na inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin. Sanarwar ta bayyana cewa, a tsawon wannan lokaci, sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama da suka hada da sarakuna irin su Kachalla Na Faransa, Dogon Bakkwalo, Auta Gobaje da Dan Mai Dutsi da dai sauransu. Ya bayyana cewa, an kawar da da...
Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da wani gagarumin shiri na kara yawan kudaden shiga na jihar zuwa sama da Naira biliyan 100 nan da shekarar 2025. Shugaban hukumar Dr. Zaid Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin da hukumar ke bitar ayyukan hukumar na shekarar 2024 da kuma tsare-tsarenta na shekarar 2025. A cewar Abubakar, KIRS ta bullo da tsare-tsare na matsakaita da kuma na dogon lokaci domin bunkasa kudaden shiga na jihar. Shirin tara kudaden shiga na matsakaicin zango na nufin tara sama da Naira biliyan 100 a shekarar 2025, inda ake sa ran za ta haura Naira biliyan 200 a shekaru masu zuwa. Musamman ma, gwamnatin jihar tace tana son...
A karo na biyu a kasa da wata daya wasu ’yan bindiga sun mika makamansu ga sojoji, a wani kokari na samar da zaman lafiya. Aminiya ta ruwaito yadda a a ranar 19 ga watan Janairun 2025, ’yan bindiga suka sallama makamansu da mutanen da suka yi garkuwa da su, a wani zaman sulhu da aka yi da su a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina. Sojoji da jami’an hukumar tsaro ta DSS da sarakunan gargajiya da mazauna sun halarci zaman na ranar Lahadi a ƙauyen Kofa da ke kid da garin Batsari. A wannann karoj manyan ’yan bindiga irin su Umar Black, Abdullahi Lankai da Jijjige da Musa Dan Gandu da Abu Radda, da sauransu, waɗanda d suka...
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da haka Hausa rasuwar Haruna Zago a asibiti. A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban Hukumar REMASAB
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba idan ba Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar ba. Qassem ya ce, “Matsayinmu a fili yake, kuma ba za mu amince da barazanar Amurka da Isra’ila ba,” in ji Qassem, bayan firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi barazanar komwa yaki idan har ba a sako mutanen da aka kama ba zuwa ranar Asabar. A ranar Laraba, ministan harkokin soji na gwamnatin ya yi gargadin cewa Isra’ila za...
Kasashen Iran da kuma Turkmenistan sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a bangarori daban-daban, in ji shugaba Masoud Pezeshkian. A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Turkmenistan Avazgeldyevich Meredov a birnin Tehran, shugaban na Iran ya ce “An bayar da umarnin da suka wajaba ga hukumomin da abin ya shafa domin nazarin bangarorin da za su kara yin hadin gwiwa da gwamnatin Turkmenistan.” Pezeshkian ya kuma yi ishara da wani taro da za a yi a birnin Teheran na tekun Kasbiya, inda ya kara da cewa Iran na kokarin fadada alaka a tsakanin kasashen Caspian bisa zaman lafiya, abokantaka, da kyakkyawar makwabtaka. A yayin wannan ganawar, ministan harkokin waken Turkmenistan ya yaba da yarjejeniyoyin da...
An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali. Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU, ana gudanar da shi ne a karkashin taken da kungiyar ta AU ta fitar na shekarar 2025 : “Adalci ga ‘yan Afirka ta hanyar biyan diyya.” Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar kula da harkokin AU, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada muhimmancin samar da kokarin hadin gwiwa domin inganta zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar. Ya kuma bayyana wajibcin gudanar da shugabanci nagari, da...
Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”. A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da rikicin masu dauke da makamai.” A taswirorin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, jiragen sama daga Kigali na kasar Rwanda, yanzu haka na kaucewa shiga sararin samaniyar Kongo. Bayanai sun ce wani jirgin da ya tashi daga babban birnin kasar Rwanda zuwa birnin Landan na kasar Birtaniyaa ranar Talata, an tilas ya sauya hanyarsa don yin aiki da dokar, wanda a yanzu ya shafi “dukkan jiragen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen. Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin biyan kudi ta fasahar zamani kamarsu Amazon da PayPal da su ma suka samu hadin kan kamfanonin kasar Sin don fadada kasuwancinsu a cikin kasar. Duka wannan yana nuna yadda Sin ke fada da cikawa ne a kan manufofinta na kara bude kofa ga duniya. Kuma ya dace Amurka ta nuna sanin ya kamata a kan bahaguwar fahimtarta da sake lale kan matakanta na haddasa...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)
Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya ce ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023. Yayin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Kwamanda ya ce Shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu. Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta Ya bayyana cewa, a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba. “Da ciwo, amma dole a faɗi gaskiya. Ni cikakken ɗan jam’iyyar APC ne,...
Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare. Kimiyya ba ta da iyaka. Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin...
Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023. Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151 na jigilar kayayyaki na kasa da sama da wuraren ajiyar kayayyaki 2,500 a kasashen waje. Haka kuma ta bude sabbin hanyoyi 168 na jiragen dakon kayayyaki na kasa da kasa a baran. A cewar Hu Han, jami’i a cibiyar tattara bayanan da suka shafi jigila ta kasar, ingantawa kayayyakin aiki da suka shafi jigila da daukaka tsarin hanyoyin jigila sun bunkasa ware albarkatu ga bangaren...
A karshe ya ce yana neman afuwa ga al’umma saboda tallata gwamnatin Tinubu da ya yi akan za ta yi abin kirki amma sai aka samu akasin haka.

Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu. Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu...
Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 5 da kuma raunata wasu da dama. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Daesh Khorasan” tana fadar haka a shafinta na sadarwa, bayanda wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da wani banki a garin Kunduz, wanda ya halaka shi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar. Labarin ya kara da cewa an kai harin kunan bakin wakenne da misalign karfi 8:35 na safe a yau Laraba, wato 4:05 na safe agogin GMT. Mai gidan bankin da kuma wasu mutane 4 daga cikin akwai fararen hula da kuma wani...

Amurka Tana Son Ta Maida Rasha Da China Gefe A Duk Wata Tattaunawa Ta Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Iran
Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba. A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke...
Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23% Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi...

Kungiyar Hamas Ta Godewa Kasashen Duniya Wadanda Suka Ki Amincewa Da Shirin Trump Na Korarsu Daga Gaza
Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa. Mutanen gaza basa son rabuwa da kasarsu, ta kaka da kakanni. Kuma suna maraba da dukkan shawarorin da kasashe larabawa da sauran kasashe duniya zasu bayar, don ganin an sake gina Gaza ba tare da an kori falasdinawa daga kasarsu ba. A wani Labari...
Karon Farko A Shekarar 2025: Turken Rarraba Hasken Wutar Lantarki Ya Fadi A Nijeriya

Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin. Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata. Hakazalika,...
Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i. Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA) a dukkan shirye shiryenta ta bada tallafi, domin ganin al’ummar jihar sun ci gajiyar ayyukan gwamnati. Wani shugaban al’ummar yankin Walewale a karamar hukumar Garki, Malam Haruna Abdullahi, ya ce, hanyar da shirin FADAMA na gwamnatin tarayya ya yi amfani da ita ya tabbatar da cewa tallafin ya isa ga masu bukata. A cewarsa, tsarin ya kawar da son zuciya da siyasa, wanda...
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya. Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi. Yawancin ’yan majalisar...
Kasar Sin Ta Yi Kiran Samar Da Ci Gaba Da Tsaro Bai-daya A Fannin Fasahar AI
Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu. Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia. Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Sun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu. Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin. Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.
Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu. Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia. Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Sun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu. Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa. N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum Ya bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta. Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice. Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice....
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum “Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja. “Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum “Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja. “Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda...
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa. Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin. Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a wannan lokacin, saboda har yanzu babu tsayayyen layin waya mai sabis mai kyau a cikinsu. Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su A don haka ne majalisar ta buƙaci NCC da Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, su dakatar da ƙarin saboda matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya...
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD. Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar. “Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar...
Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na musamman na kungiyar OIC a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Aljeriya Ahmed Attaf, a wani bangare na tuntubar da yake yi da ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan Gaza. A yayin tattaunawar tasa, Mista Araghchi ya yi cikakken bayani kan shawarwarin da ya yi a baya-bayan nan da shugabannin kasashen musulmi, da kuma babban sakataren kungiyar OIC, Hussein...