2025-04-29@19:39:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3924
«wutar lantarki a»:
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya). AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba. Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.” Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya...
Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab. Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta bayyana cewa: Sojojin mayar sun kafa shingen binciken ababen hawa inda suka tsaya suna binciken ababan hawa da ke wucewa, sannan suka haska wuta don gano hanyar kafin su fita ta hanyar da suka shiga. Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna shawagi a sararin samaniyar birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya. A jiya Litinin ma, sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai...
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari. Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi. Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka...
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
Shi ma dayan, bayan ya bayyana cewa, sun kasance barayin mota ne a jihar Katsina amma wani abokinsu ya gayyace su zuwa jihar Filato domin ci gaba da sana’ar. Yayin da ya amince zai jagoranci Tawagar Soji zuwa maboyarsu, jami’an sun gano bindiga kirar fistul daya da mukullai da suke amfani da su wajen bude motoci da gidajen jama’a, inda daga bisani shi ma ya yi kokarin arcewa kamar yadda abokin shi ya yi. Hakan ta sa shi ma aka harbe shi har lahira. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka. A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda tsawonsu ya dara na bene mai hawa biyar, inda kuma aka tanadar wa da yankin, ababen more rayuwa. kananan hukumomi ne, suka gina wadannan matsugunnan, musamman donin a dakile barazanar kwararowa alumma daga kauye, zuwa cikin birane. A gwajin da aka yi na yankunan da su habaka sosai a China, ana buga misali da Hero Bay kan yadda gwamnati ke bai wa alumma...
Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida. Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal Majiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata. Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu...
Wani saurayi ya wallafa wani labarinsa a kafar sada zumunta ta Reddit tare da yin nadama, inda ya ce matar da suke soyayya ta faɗa masa cewa, an haife ta ne a shekarar 1998, har sai da ya duba bayanan fasfo dinta. A wani lamari mai ban al’ajabi da ban tsoro, matashin ɗan shekara 26 ya girgiza bayan ya gano cewa, matar da yake soyayya da ita da nufin aure, bayan shafe shekaru huɗu suna tare tana da shekara 47, ba 27 ba, kamar yadda ta yi iƙirari. An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Saurayin ya tafi shafin Reddit don ya wallafa labarinsa na nadama, inda ya...
Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN). Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamatin, Ministan Sufuri, Sanata Said Alkali, ya jaddada muhimmancin shawo kan kalubalen hadurran da ke ci gaba da barazana da haddasa munanan asarar rayuka da dukiyoyi. Alkali wanda ya jaddada bukatar a gaggauta kawo karshen wannan mumunan lamari, ya bai wa kwamitin mako guda ya gabatar da rahotonsa, inda ya jaddada cewa, tsaro da inganci su ne kan gaba a cikin manufofin gwamnatin Bola...
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai. A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita. Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu....
Ba wannan ne karo na farko da shugaba Trump ya nuna girman kai da rashin sani game da Afirka ba. A watan da ya gabata, lokacin da yake bayani game da dalilin da ya sa gwamnatinsa ke rage gudummawar jin kai da take bayarwa a duniya, ya ce a baya, Amurka ta samar wa kasar Lesotho gudummawar dala miliyan 8, amma “ba wanda ya taba jin sunan wannan kasa”. Amma ita wannan kasar da ko sunanta shugaba Trump bai taba ji ba, ya sanya ta cikin jerin kasashen da ya sanar da zai kakaba musu haraji, har ma ya sanya mata haraji na kaso 50%. Idan ba mu manta ba kuma, a wa’adin shugabancinsa na farko, shugaba Trump ya taba...
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
A nasa ɓangaren, mai bai wa Gwamnan Shawara Kan Al’ammuran Tsaro, Janar Dahiru Abdusalam (Mai Ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana ɗaukar matakai tare da jami’an tsaro don samar da tsaro mai inganci. Ya kuma bayyana cewa duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a hanyar Damaturu zuwa Gujba, jami’an tsaro na ƙoƙarin yin sintiri domin tabbatar da tsaro. Janar Dahiru ya ce, “Koda yake muna fuskantar ƙalubale daga Boko Haram a yankunan wasu sansanin sojoji, jami’an tsaro na ci gaba da aikinsu domin kare yankin.” Ya ƙara da cewa, “Muna taka-tsan-tsan musamman wajen daƙile karɓar haraji daga Boko Haram a wasu yankuna. Wannan al’amari yana da matuƙar wahala, amma muna fatan za mu samu nasara.” Janar Dahiru ya...
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno. Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu. Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa. “Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke...
Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa matsayin sabon Galadiman Kano. Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano. Wannan sabon...
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba. Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba. Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar. Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya...
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Muslunci a Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, rasuwa. Babban Mufti na ƙasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan, ne ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai a daren Litinin. Sai dai bai bayar da cikakken bayani game da inda Sheikh Hadiyatullah ya rasu ko kuma lokacin da hakan ya faru ba. Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar marigayi Sheikh Hadiyatullah ta bar giɓi mai wuyar cikewa a shugabancin Musulunci na ƙasar. Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya “An haife shi a garin Iwo a Jihar Osun kuma...
Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye. Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar. Shugaban kungiyar...
Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar. Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.” Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita...
Wata majiya kuma ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu na iya fin haka, duba da yawan mata da yara da lamarin ya rutsa da su. A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin soji da ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki. Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Birnin Kebbi. Ya kuma yi alkawarin tabbatar da jin daɗin mahajjatan jihar yayin da suke a ƙasa mai tsarki. Amirul Hajjin ya bayyana cewa jimillar mahajjata 3,800 daga jihar ne suka biya kuɗin kujerunsu gaba ɗaya domin aikin hajjin bana, kuma jigilar mahajjatan za ta fara ne ranar 9 ga watan Mayu, inda ya ce da yardar Allah za a ci...
Kasar Sin ta cimma nasarar harba sabon tauraron dan’adam na ayyukan sadarwa mai suna Tianlian II-05, daga tashar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar. An harba tauraron ne da karfe 12 saura mintuna 6 na tsakar daren jiya Lahadi agogon Beijing, ta amfani da rokar Long March-3B, kuma tuni ya shiga da’irarsa kamar yadda aka tsara. Tauraron zai rika samar da hidimomin musayar bayanan sadarwa ga kumbunan sama jannati, irin su kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati, da tashar binciken sararin samaniya, domin nasarar ayyukan taurarin dan’adam marasa nisa da doron duniya, da taurarin dan’adam masu taimakawa aikin harba kumbuna. Wannan ne karo na 572 da aka yi amfani da roka samfurin Long...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya, kamar yadda ta yi a lokacin rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, ta yaya masana’antunta za su farfado bisa wannan tsarin? Hakazalika, babu yadda za a yi Amurka ta sake zama cibiyar masana’antun duniya bayan da ta yi watsi da matsalolin da ake fuskanta a zahiri kamar sauyin yanayi, wanda ayyukan masana’antu ne suka haifar da shi tun farko. Bari mu dauka...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027. Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya. Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Bankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito. Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya. Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji. A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na...
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai. Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure. Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia. Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan...
Guo Jiakun ya bayyana cewa, a ranar 26 ga wannan wata, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki sun gabatar da sabbin matakan mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido, lamarin da ya kyautata manufar mayar da kudin haraji tun daga lokacin sayayya da kawo sauki ga baki masu sayayya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran. A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba. Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka,...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki...
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza. A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...
Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.” Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar. Har yanzu dai ba a san abin...
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kazalika, domin daidaita ci gaban cinikayyar waje, manufofin da za a aiwatar sun hada da na tallafawa kamfanonin dake fitar da hajoji, ta yadda za su rage hadurra daka iya aukuwa, da fadada fitar da hidimomin da ake samarwa ga karin sassan duniya, da karfafa gwiwar kamfanonin waje, ta yadda za su kara zuba jarinsu a kasar ta Sin. Daga nan sai jami’in ya bayyana cewa, Sin na da isassun manufofi da tsare-tsare, da za su wanzar da burinta na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a shekarar nan ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya. Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi. Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Hakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal. A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a...
A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato. Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi ’yan uku a garin Kaurar Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo ta jihar. Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi A yayin da mai jego da angon karni da ’yan uwa suke tsaka da murna, wannan karuwar haihuwa ta kara jawo musu sha-tara ta arziki, inda matar gwamnan...
“Saboda haka, Litinin 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446AH, yayin da ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 za ta zama farkon watan Zulki’ida 1446AH.” Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi na mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya. A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa. Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi...
Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun. A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga. “Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso...
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari. Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.
Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa a makon da ya gabata. Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza. A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda. Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu...
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar. A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta...
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar. “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa. “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne. “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya. Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati. Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura. Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi. “Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna...
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji. Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji. Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin. Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona...
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba. Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda...
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha. Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya. Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta. Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna. Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar...
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi. A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ke ta ƙaddamar kan sarautar Kano da Aminu Ado Bayero a gaba kotu, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano. Wannan lamari na nuni da cewa rikicin Sarautar Kano ya ɗauki sabon salo, inda kowanne daga cikin ɓangarori biyun ya naɗa nasa Galadiman Kano, inda masu riƙe da sarautun biyu za su gudanar da ayyukansu daban-daban. A cikin wasiƙar da ke ɗauke da wannan sanarwar, wadda Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, babban jami’in gudanarwa na Majalisar Masarautar Kano ya sanya hannu, naɗin Sanusi...
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu. Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara. A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata. A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama. Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba. A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.” Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.” Watanni 9 da su...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi. A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027. Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC. NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA:...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka kuma za a aiwatar da dukkan abubuwan da aka dade ana yinsu cikin shirin raya kasa a hukumance. Ana sa ran dokar za ta kara inganta tsare-tsaren da za su tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa da karfafa dacewar manufofin da suka shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da juna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne sun kashe mutane 10 na yawucin dabbobi da kuma mambobin jami’an tsaron sa kai (CJTF) a garin Kwapre, dake cikin ƙaramar hukuma ta Hong a Jihar Adamawa. Shugaban ƙaramar hukuma, Hon Usman Wa’aganda, ya tabbatar da wannan lamarin ga LEADERSHIP ta waya a ranar Lahadi a Yola, inda ya bayyana cewa wani mutum da ya samu raunuka daga harin ‘yan ta’addan yana samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba. Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa Wa’aganda ya ce ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje da dama da kuma amfanin gona,...
A cewarsa, kasar Sin ba ta neman kakaba akidunta kan sauran kasashe. Abun da take nema shi ne, aminci da tuntubar juna. Kuma a ganinsa, wannan shi ne ya kamata ya kasance ruhin hadin gwiwa. Bugu da kari, ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar game da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da ci gaban duniya da hadin gwiwa ta fuskar al’adu, sun dace da muradun MDD na wanzar da zaman lafiya da gudanar da ayyukan agaji da tabbatar da tsaro a duniya, yana mai cewa, akwai babbar dama ta kara hadin gwiwa a cikinsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin lamarin ya kai matakin da akwai wuraren da mutane ba sa iya zuwa da daddare saboda tsoron mummunan abin da ke iya samun su. An kashe sojoji 12 a barikin Nijar An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba Wasu na ganin yadda ake gudanar da siyasar jihar da kuma yadda rashin aikin yi su ne ummulahaba’isin wannan matsalar musammam a tsakanin matasa....
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya. Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya
Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka. Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran,...

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka
An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku A safiyar yau Lahadi ne aka bude zaman taron karo na uku kan harkokin tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afirka a birnin Tehran, tare da halartar shugaban kasar Iran da mataimakinsa na farko da wasu tawagar jami’ai da ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka. Kasar Iran tana gudanar da wannan biki ne tare da jami’an kungiyar Tarayyar Afirka, da manyan jami’ai, ministocin tattalin arziki da cinikayya, da shugabannin kungiyoyin kasuwanci, ‘yan kasuwa, masu fafutukar tattalin arziki, shugabannin bankuna, kamfanonin inshora, da na’urorin samar da kayayyaki, da daraktocin manyan kamfanoni da na kasa da kasa daga kasashen Afirka. Taron...

Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba
A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta. Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.” Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”
Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki. Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma. Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima. Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa. Daga kanmu, magana...
Ban da karuwar yawan wutar lantarki da aka samar ta aiki da makamashin nukiliya, karfin kasar Sin na yin kirkire-kirkire da kanta a wannan bangare ya kyautata matuka. A shekarar bara, Sin ta samar da dukkan muhimman sassan na’urorin samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin nukiliya ta hanyar dogaro da kanta.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An kashe sojoji 12 a yankin Tillaberi na yammacin ƙasar mai iyaka da Mali da Burkina Faso, yankin da ke zama tungar masu iƙirarin jihadi da ’yan ina da kisa masu nasaba da ’yan ƙungiyoyin al Qaeda da IS. Ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar da cewa an yi wa dakarunta na bataliyar ko-ta-kwana mai suna Almahao kwanton ɓauna ne a wani kauye da ke kusa da Sakoira na yammacin Tillaberi, inda sojan suka jima suna ɓarin wuta da ’yan ta’adda kafin a kawo musu ɗauki. An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Gwamnatin ta bayyana cewa tuni ta cafke mutane biyu da ake zargi da kai harin a barikin...
Ƴan fashi sun sace fasinjoji guda bakwai a cikin motocin haya biyu a ƙauyen Eleyin da ke cikin ƙaramar hukumar Isin a Jihar Kwara. A cewar rahoton LEADERSHIP, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yamma a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da wasu ƴan fashi su biyar suka toshe hanya, suka tsayar da motoci biyu, sannan suka tilasta ɗaukar dukkanin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, daga cikin fasinjojin motar ɗaya, akwai shugaban sashin shari’a na ƙaramar hukumar Oke Ero, Barr. Elizabeth Arinde,...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Bugu da kari, an fi samun kyautatuwa a bangaren samar da kayayyaki, inda yawan ribar da aka samu a farkon watanni 3 na bana ya karu da 7.6%, saurin karuwar ya kai 2.8%. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa. Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati. Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa, sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe. A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, sun ce Ja’o’ji mutum ne mai kishin matasa da ƙoƙarin inganta rayuwarsu. Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji Sun bayyana cewa, “Wannan muƙami da Sarkin Daura zai ba shi, ya ƙara tabbatar da binciken da muka gudanar wanda ya nuna cewa Ja’o’ji yana cikin shugabannin matasa 10...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane. Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke. Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar Ingila Kakakin rundunar ’yan sandan, ASP James Lashen ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Jalingo. Ya bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Shehu Ibrahim da Abdullahi Haruna da kuma Yusuf Bello. Sauran kuma sun haɗa da Sulaiman Muhammed da Tijjani Bello da Muhammed Umar. Kazalika, akwai kuma Adamu Ibrahim...

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’. Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
“Muna kira ga sauran kungiyoyi, ‘yan siyasa, masu hannu da shuni tare da gwamnatoci, cewa kofarmu a bude take wajen neman taimakon kayan abinci, tufafi da makamantan su.” In ji Goni Alhaji Goni ya kara da cewa, gungiyar su ta direbobi, ta na da mambobin sama da 30,000 a fadin jihar Yobe. Ya ce, kullum suna kan hanya, yau ace wannan ya yi hadari ya karye, gobe wannan ya rasu. “Saboda haka mu na rokon gwamnatin jihar Yobe tare da Hukumar Sake Raya Arewa Masu Gabas da sauran kungiyoyi, su kawo wa marayun mu daukin gaggawa.” In ji shi. A nashi bangaren, Kodinatan YFM a jihar Yobe, Malam Sadiq Muhammad ya ce, sun zabi bai wa marayun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
‘Yan kungiyar ta boko haram sun kashe masu sintiri farafen hula 2 da kuma wasu sana’ar yin sarar itace su 10 a a Bokko Gjide a karamar hukumar Gwoza dake Jahar Borno. Sarkin Gwoza Alhaji Muhammad Shehu Timta ya tabbatar da kisan mutanen da aka fi kira da (Civilian JTF) bayan da aka yi musu kwanton bauna a kan hanyar Kirawa. Haka nan kuma ya kara da cewa; mutanen sun shiga cikin daji ne domin saro itace, a ranar Asabar, a yayin da masu dauke da makaman su ka yi musu kwanton bauna su ka kashe kashe daga cikinsu, sannan kuma su ka yi wa wasu biyu munanan raunuka. Sarkin ya kara da cewa; Mun yi jana’izar 10 daga cikinsu...
A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun kai daukin gaggawar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan sansanin ‘yan hijira da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu da kuma yanke wutar lantarki a garin Atbarah, a jihar “Nahrun-Nil” ta arewa. Hukumar dake samar da wutar lantarki ta Sudan ta tabbatar da yankewar samar da wuta a wannan yankin saboda harin da mayakan na rundunar daukin gaggawa su ka...
Sojojin na kasar Yemen sun sake kai hari akan sansanin sojan saman a “Nivatim” na HKI a karo na biyu a cikin sa’o’i 24. Majiyar sojan kasar ta Yemen ta ce wannan shi ne karo na hudu da suke kai hari akan manufofin HKI a cikin sa’o’i 24. Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sa’ri ya fada a wata sanar wa ta tashar talabijin cewa; sojojin kasar sun kai hari da makamai masu linzami da su ka fi sauti sauri wajen kai wa sansanin na “Nivatim” hari wanda yake a cikin yankin Naqab a Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Sari ya kuma kara da cewa; hare-haren da suke kai wa HKI yana a karkashin ci gaba da taya Falasdinawa fada...
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21 Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan mahajjatan da suka yi rijista domin aikin Hajjin 2025 dole ne su gudanar da binciken lafiya cikin wannan mako. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya wannan tafiya ta ibada. Binciken lafiyar ya haɗa da gwajin ciki na dole ga mata masu shirin zuwa Hajji. Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki ba domin hana kowa yin Hajji ba ne, sai don tabbatar da cewa an tanadi cikakken tallafin lafiya musamman ga mahajjatan da ke fama da cututtuka kamar...
Manyan mutane kamar su Malam Dan Haki, Karkuzu da irinsu Samanja duka ba su yi fim don kudi ko daukaka ba, kawai abin ne yake burgesu sai kuma isar da sakonnin gwamnatin tarayya ko ta jaha, saboda haka da dama wadanda ke shigowa yanzu suna yi ne saboda wani abu da suke tunanin zasu samu. Tunda nake zaune a gida ina jinyar ciwon suga har ta kai ga an yanke mani kafa daya, akwai wadanda basu taba kirana ko a waya suka tambayeni yaya jikina ba duk da cewar sun sani bani da lafiya, saboda haka babu wani aibu idan ni ko wani dan fim yace ba zai bari dan da ya haifa ya shiga harkar fim ba. ...
Wannan wata mahawara ce da aka daɗe ana yi kan wace kungiya ce ta fi gawurta a Birtaniya? Shin wace kungiya ce ta fi lashe kofuna? Wacce ce ta fi tara kudin shiga ko kuma ta fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta? Wace kungiya ce ta fi filin wasa mai girma? Wacce ce ta fi daraja a gasar Firimiya? ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis Sai dai wannan muhawara da wuya a kawo ƙarshenta, saboda dole za a ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta, kuma ba dole ba ne a samu gamsasshiyar amsa. An tafka muhawara kan abubuwa da dama, amma a ƙarshe sai muka yi nazari tare...
Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria: Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki. Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai...
Francis, wanda aka zaba a matsayin gwarzon Shekarar na TIME a 2013, ya zama Fafaroma na farko na da ya fiton daga yankin Latin Amurka lokacin da ya karbi ragamar cibiyar addinin. A cikin wa’adinsa, Francis ya ya yi suna wajen tawali’u da kiran zaman lafiya yayin da duniya ke fuskantar manyan kalubale, da suka hada da gami da cutar Korona da rikicin Gaza. Yayin da duniya ke juyayin rasuwar Francis tare da tunawa da tarihin rayuwarsa, yanzu kuma an fara shirin mika jagoranci a fadar Batican wadda aka fi sani da interregnum, wato ana nufin wani lokaci da babu Paparoma akan kujerar mulki (wanda ake kira sede baccante, ko “kujerun da ba kowa ba”). Akwai abin da...
Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi. Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya gano ra’ayinsa ko ya iya hasashen yanayin siyasarsa. “Gwamna Buni bai tsaya kawai dan jam’iyyar APC ba; ko kawai gwamnan APC ba. Shi ne APC gaba dayanta, saboda sanannen abu ne cewa APC ta ratsa jijiyoyin jininsa. “Sannan gudunmawar da ya bayar wajen gina APC a matsayinsa na Sakatarenta na kasa sau biyu, kuma ya rike ragamar Shugaban kwamitin tsara taron jam’iyyar; ya...
Duk da haka, Mai Maciji ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun gudu lokacin da matasan gari suka afka musu. Sun kona wani shago a kasuwar, amma wutar ba ta bazu zuwa sauran shaguna ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp