2025-03-06@13:17:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 322
«Abubakar Lawal»:
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani...
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo. A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a...
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara. Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman...
Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye. Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma. Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar. Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban...
Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14. Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da shirin sake gina Gaza na Masar da aka amince da shi a wani taron gaggawa na kasahen Larabawa da aka yi a birnin Alkahira. Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, taron na birnin Alkahira ya nuna wani muhimmin mataki na daidaita alaka tsakanin Larabawa...
Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da...
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana...
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan...
Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma jiya Talata, Mataimakin ministan ya...
“A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna...
Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. “Ma’aikatan jihar za su je aiki...
Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin...
Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron da kasashen larabawa suke yi a Masar, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin da su ka bijiro da shi na sake gina yankin Gaza, ba tare da an fitar da Falasdinawa daga cikinsa ba. Gutress ya ce; Ina maraba da kuma nuna cikakken goyon bayana ga...
Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu...
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl. Game...
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya...
Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu. “Farawa daga yanzu,...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya...
Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio. A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar...
Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar...
Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau...
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar...
Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba. Badr Abdul’adhy, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar...
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar...
Sai dai, a martanin da ta yi ta bakin lauyanta a ranar Asabar, Giwa ya bukace matar Sanata Akpabio ta da janye kanta a rikicin don bai wa mijinta damar kare kansa saboda wanda yake karewa tana da “kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da zarginta.” Sanata Natasha ta kai karar Akpabio da mai...

Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma...
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau...
A jiya Juma’a ne mai magana da yawun ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin ya bayyana rashin amincewa da barazanar da Amurka ta yi ta sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa. Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wata tambayar manema labarai kan...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin...
Fira ministan hakar Habasha Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan...
Ita kuwa Kasar Algeria, ita ce ta uku; inda ta noma Dabino kimanin tan miliyan 1.25. Hadakar tsakanin Gwamnatin Jigawa da Saudiyya da kuma wani kamfanin aikin noma da ke kasar nan, wato ‘Netay Agro-Tech’, za ta kara taimakawa wajen sake habaka noman Dabinon a jihar. A duk shekara, Nijeriya na noma Dabino kimanin tan...
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta...

Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
Shuwagabannin Afrika ta Kudu, Malasiya da kuma Colombia sun jaddada matsayinsu nah ana jiragen ruwa dauke da makamai zuwa HKI tsayawa a tashishin jiragen Ruwan kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, Firaiministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim da Shugaban kasar Colmbia Gustavo Petro...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga cikin wuraren kiwo guda 400 da ke jihar, ta duba 57 domin dakile rikicin manoma da makiyaya a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a wajen bude taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen kiwo tare da hadin gwiwa da kwamitin shugaban kasa na aiwatar...
Kasar Masar ta ce an fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza. Ma’aikatar yada labaran kasar Masar ta fada a jiya Alhamis cewa, tawagogin Isra’ila, Qatar da Amurka na birnin Alkahira domin tattaunawa mai zurfi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. “Bangarorin da abin ya shafa...
Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka...
Wasu gungun ‘yan Boko Haram ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki cikin dare a garin Kwapre da ƙauyukan da ke gundumar New Yadul a ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa. Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren. Kotu...
Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu kara yawan wutar lantarkin da...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...