2025-03-06@16:36:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 327

«Abubakar Lawal»:

    Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka...
    Wasu gungun ‘yan Boko Haram ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki cikin dare a garin Kwapre da ƙauyukan da ke gundumar New Yadul a ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa. Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren. Kotu...
    Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami  ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu  kara  yawan wutar lantarkin da...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...
    Hukumar bunƙasa ƙere-ƙere ta ƙasa (NASENI) ta bayyana cewa an kusa kammala aikin ƙera jirgin sama mai saukar ungulu na farko da aka yi a Nijeriya, kuma nan ba da jimawa ba za a fara gwajin tashinsa. Wannan ci gaba na daga cikin yunƙurin ƙasar wajen bunƙasa fasahar masana’antu da rage dogaro da kayayyakin da...
    Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross. Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin...
    Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin...
    Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga  ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ​​ma’aikatan da suka rasu. Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a...
    Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma....
    Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa. “A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane...
    An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da...
    Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata...
    Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan...
    Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga  ma’aikata da...
    Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci  hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin...
    Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren....
    Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad. Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin...
    Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar  Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu. Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban...
    Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban...
    Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun  jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta  yi alkawarin horar da matasa da ke aikin noman alkama a karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba gonakin alkama a yankin. Ya yabawa Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr Muhammad Uba Builder bisa wannan shiri da ya bayyana a matsayin...
    Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta...
    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka...
      Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.   Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na...
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin...
    Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun. Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin...
    Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron  kasar nan. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. A cewar sa,...
    Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
    Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara...
    Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya,...
    Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar...
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine. A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan...
    Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki  yankin. Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman,  an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA. Taron ya samu halartar sarki Abdullah II...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
    Ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da suka yi ritaya, sun bayyana jin dadinsu kan karin haske da Ministar Kudi ta yi game da wadanda za su ci gajiyar Naira Biliyan 758 da aka amince da su don biyansu kudaden fansho da suke bi. A tsokacin da suka...
    Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin...
    Shirin karfafa karatun mat (AGILE), ya fara horar da Malamai 20 na kwanaki 3 domin gudanar da shirin ba da ilimi na zamani mai suna dama ta biyu ta samun ilimi. “Second chance education bangaren” a Kano. Shugabar Bangaren Aikin, Miss Hafsat Adhama, ta bayyana haka a wajen taron cin abincin rana da aka gudanar...