2025-03-03@17:42:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 218
«Kayan Masarufi»:
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Ramadan, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin mai cike da falala, tausayi, da zaman lafiya. A sakon da MDD ta fitar ta hannunsa, Guterres ya ce, “Ramadan lokaci ne da ke karantar da kyawawan ɗabi’u na tausayawa, taimakekeniya, karamci,...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma. Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba...
Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58...
Sai dai, a martanin da ta yi ta bakin lauyanta a ranar Asabar, Giwa ya bukace matar Sanata Akpabio ta da janye kanta a rikicin don bai wa mijinta damar kare kansa saboda wanda yake karewa tana da “kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da zarginta.” Sanata Natasha ta kai karar Akpabio da mai...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji. Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin...
Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan...
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu’o’i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna. Malaman sun gudanar da addu’o’in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin...
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta je har gidan Atletico Madrid ta doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Coppa Del Rey, bayan da Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa:...
Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya. Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma. HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura...
C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai. 5) Ruwan...
Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6...
Saɓanin shekarun baya, azumin watan Ramadan na bana ya zo a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa farashin kayan abinci na sauka a sassan Najeriya. Kayayyakin masarufi irinsu shinkafa da wake da fulawa na daga cikin waɗanda aka fi sarrafawa a watan na Ramadan, kuma su ne masu gwaggwaɓan kaso a faɗuwar farashin. Farashin...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta yaba da gudunmuwar da Gwamnatin Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ke badawa wajen samun nasarorin da aka samu kwanan nan. An bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban Hukumar Jindadi Alhazai na Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar ya jagoranta...
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda...
Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Jihar Kaduna da zama, bayan shafe shekara biyu a Daura, tun bayan barinsa mulki a watan Mayun 2023. Buhari, ya zaɓi yin rayuwa mai sauƙi bayan kammala wa’adin mulkinsa ba tare da shiga harkokin siyasa ba. Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan...
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda. An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba. An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada....
Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ma’aikatan da suka rasu. Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a...
Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin...
’Yan Ta’addan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Kaleri da ke Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno, inda suka sace mutum biyu da kayan abinci masu tarin yawa. Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne kusa d Jami’ar Maiduguri (UNIMAID). Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin...
Shugabannin Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da sauran manyan jagorori, sun gana a daren Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An gudanar da taron ne domin shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a yi a yau a hedikwatar APC. Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da...
Baya ga Messi shi ma Luis Suarez ya fuskanci hukunci bayan tuhumarsa da laifin dukan Birk Risa a wuya duk dai a wannan karawar tsakaninsu da New York, Messi ya koma Inter Miami daga PSG shekaru biyu da su ka gabata, tun bayan zuwanshi Miami Messi ya zura kwallaye fiye da 20 sannan ya taimaka...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage...
Iyalan Malcolm X, bakar fata fata kuma daya daga cikin jagororin musulmin Amurka da aka kashe a ranar 21 ga Fabrairun 1965, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya bayyana bayanan da ke da alaka da kashe shi, kamar yadda shafin Arabi 21 ya ruwaito. Iyalan Malcolm X sun gabatar da bukatar ne a...
Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin. A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula...
Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura. Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu...
Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba. Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce za ta fara gudanar da bincike kan kocin Fenerbahce Jose Mourinho bayan da ta zarge shi da furta kalaman wariyar launin fata bayan da ƙungiyoyin suka tashi 0-0 ranar Litinin. Zuwa yanzu dai ba a bayyana irin kalaman da Galatasaray ke nufin Mourinho da furtawa ba, da yake...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban...
nkin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya...
Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na...
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta...

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin sojan gona ga aikin hukumar. Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce mutanen...
Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai...