2025-03-18@13:12:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 23
«a shirya finafinai»:
Masana’antar Kannywood ta dade tana nishaɗantar da al’umma, musamman Hausawa da sauran kabilun Arewacin Najeriya. A makon jiya Aminiya ta ruwaito a cewa kasuwancin fina-finan ya samu koma-baya matuƙa, wanda hakan ya sa wasu suke nuna yatsa ga furodusohin yanzu kan gaza shirya fim ɗin da za a iya haskawa a Netflix da sauran manyan hanyoyin nuna fina-finai da za su samar wa masana’antar kuɗin shiga. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza Wannan ya sa Aminiya ta yi waiwayen wasu furodusohin da aka daina jin ɗuriyarsu a masana’antar. Salisu Galadanchi – Shi ne Daraktan Fim din Turmin Danya, fim na farko a Kannywood, ya...
Ya kara bayanin cewar Jami’ar za ta dauki sahun dalibanta na farko wato shekarar karatu ta 2025, inda ya kara jaddada aniyar gwamnati ta bada damar samun yin karatu na ilimi mai zurfi tare da bunkasa shi. Ministan har ila yau ya ce zai taimaka wajen tabbatar da cewar Jami’ar ta samu nata kason daga Hukumar kula da ilimin manyan makaratun ta kasa, domin hakan zai taimakawa bunkasa Jami’ar cikin wani lokaci nan gaba. Ya ci gaban da bayanin “Zan tabbatar da cewar Jami’ar ta samu taimako na gidauniya kula da ilimi mai zurfi ta lamurran manyan makarantu ta samun kudade daga wurinta wannan shekarar. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga al’ummar Kudancin Kaduna, al’ummar Jihar Kaduna,...
Mahukuntan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun sanar da shirin fara yiwa ’yan mata dake makarantun karamar sakandare allurar rigakafin cutar HPV, mai haifar da karin bakin mahaifa kyauta, tun daga watan Satumban bana, a wani mataki na dakile karuwar mata dake kamuwa da cutar. A cewar sanarwar hadin gwiwa ta cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta birnin da sauran hukumomi masu alaka da aikin, wadda aka fitar a jiya Alhamis, ya zuwa karshen watan nan na Maris, ’yan mata da a yanzu haka ke ajin karshe na makarantun firamare, za su cike takardun amincewa da karbar rigakafin, kana ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, za a kammala yi musu kashin farko na rigakafin. An shirya gudanar...
Ya ce, muddin ‘yan siyasan Nijeriya ba su haɗa kansu waje guda ba, ƙalubalen da suke cikin ƙasar nan za su yi wuyar kawuwa. Ya ce, akwai kuma buƙatar tunƙarar matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya. Ya ce, tuntuɓar da suka fara da gwamnan Bauchi a matsayinsa na fitaccen ɗan siyasa a Arewa kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya yi ne ba wai don son zuciyarsu ba, illa sai don son da suke yi da cigaban ƙasar nan da nemi mafita. Ya lura kan cewa akwai buƙatar a fara magance matsalolin talauci a Nijeriya kafin a tunƙari sauran matsaloli. Ya yi fatan cewa za su ci gaba da irin wannan tattaunawar domin nema wa Nijeriya mafita. Shi...

Tutocin Falasdinu Sun Yi Ta Kadawa A Birnin Sao Paulo Na kasar Brazil, A Gagarumin Gaggami Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa Suka Shirya
Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran. A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan...
Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...

Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya
Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada. A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Jakadan Sin a Najeriya, Mista Yu Dunhai, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa a yau alhamis. Ya ce, wadannan yarjejeniyoyi sun ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin watsa labarai da sadarwa, domin inganta dangantakar Najeriya da Sin. Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun shafi...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar. Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni. “Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya...
Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in ji shi kamar yadda ya bayyana a hirarsa da Fox News. Sai dai ya bayyana cewa musayar yawun ba ta dace ba, sannan ya kara da cewa dangantakar da ke tsakaninsa da Trump za ta gyaru. Tunda farko dai an soke taron manema labarai da aka shirya yi a fadar White House a jiya Juma’a, inda shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky...
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai. Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani. Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa. Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci. Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da...
Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin tsaron kasar a matsayin rashin hankali da wauta. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana a jiya Alhamis yayin da jami’an Isra’ila ke ci gaba da yi wa Iran barazanar daukar matakin soji, kasashen yamma na ci gaba da zargin kasar da kara karfin tsaronta. M. Baqaei ya yi nuni da cewa, yankin yammacin Asiya na fama da wata mamaya da ta dade wacce kamu ta wuce gona da iri da rashin bin doka da oda. Don haka ya kara da cewa, wajibi ne kawai Iran ta kara karfin tsaronta. Kalaman nasa sun...
Cibiyar Ilimin Mata Ta Shirya Wa Sarakuna Da Malamai Taron Inganta Karatun Mata A Kaduna
Wasu fursunoni uku da ke tsare a gidajen yari daban-daban sun lashe Gasar Musabakar Al-Kur’ani da aka gudanar a Jihar Kano. Fursunoni sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shinrya a matsayin wani bangare na tsarin ilimin fursunoni. An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al’umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan yari. Mai magana da yawun hukumar gidajen yari a Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari. Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya Ya bayyana cewa furunan da ya lashe...
A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da cewa Shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ba zai gaza ba duk da ƙoƙarin yaɗa jita-jita da wasu ke yi. Kwankwaso, ya musanta wani rahoto da ke cewa mahajjata na iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025, inda ya bayyan cewar wannan ƙarya ce da aka shirya don yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan shugaban NAHCON. An yi wa kashi 25 na matan Nijeriya kaciya Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya Ya buƙaci jama’a, musamman maniyyatan da za su yi aikin Hajjin 2025, da su yi watsi da wannan rahoto, inda ya Farfesa Pakistan yana da...
Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
Xi Da Mai Dakinsa Sun Shirya Liyafar Maraba Da Manyan Baki A Birnin Harbin
Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza. Umarnin Katz ya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump na tilastawa Falasdinawa Gaza barin zirin da kuma sanya Amurka ta mamaye yankin da yaki ya lalata. “Na umurci IDF da su shirya wani shiri don ba da damar ficewa na radin kan mazauna Gaza,” in ji kakakin na Isra’ila a cikin wata sanarwa. Katz ya bayyana cewa ya fadawa sojojin Isra’ila da su yi shirin da “zai ba da damar duk wani mazaunin Gaza da ke son barin yankin zuwa, ga duk wata kasa da yake son karba.” Ministan tsaron Isra’ila ya kara da cewa “Tsarin zai hada da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsakanin Hausawa akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko mene ne alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Albarkacin Ranar Yaƙi da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata. Domin sauke shirin, latsa nan
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...

Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya