2025-03-06@09:47:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 139

«Rabi u Musa Kwankwaso»:

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lin Jian ne ya jaddada cewa, alakar da take a tsakanin Rasha da China ba ta tasirantuwa da shiga tsakanin wani bangare na uku, sannan kuma ya ce, kokarin da Amurka take yi na haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu ba zai yi  nasara ba. A wani taron manema labaru...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin...
    Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada....
    Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin...
    Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu...
    Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara  kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin. A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara...
    Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci  hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin...
    Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware.   Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai kwamitin ya kada kuri’ar amincewa da kudurin na Amurka da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin Ukraine da Rasha. Kuri’u 10 ne suka amince da kudurin,...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen...
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga...
    Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta...
    Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya,...
    Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn),...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
    Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da...
    Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan...
    Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin...
    A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar...
    “A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...
    Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a.   Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh.   Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha,...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na...
    Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.  A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi,...
    Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”   Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif...
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...
    Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo...
      Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.   Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.   Ya ce,...
    Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 3000 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
    Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina.   AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani...
    Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba...
    Mataimakin shugaban ya umarci shugabannin NAHCON da su gaggauta daukan kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da kare martabar dukkanin maniyyatan Nijeriya. Da yake magana kan soke kwantiragin da suka yi da kamfanin kasar Saudiyyan, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya ba da tabbacin cewa lamarin ba sai shafi kowani maniyyancin Nijeriya ba....
    Jakadan Amurka na musamman kan kasashen Rashad Ukraine ya bayyana cewa Amurka tana kokarin ganin ta kawo karshen dukkan dangantakar da ke tsakanin kasashen China da Rasha da kuma JMI. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto, Keith Kellogg ya na fadar haka a taron Munich na tsaro a jiya Asabar. Ya kuma...
    Rahoton ya ce an fara badakalar ne a ranar 10 ga watan Disamba a lokacin da kamfanin harhada magunguna ya samu sakon imel dake nuna wani mai sayar da shi, Accent Pharma, yana neman a biya shi wani sabon asusun ajiya na banki. Ba tare da sanin sakon imel din na yaudara ne ba, ana...
    Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun  yi musayar  sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye. Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece...
      Jami’ar Tarayya ta Lafia ta yi bikin rantsar dalibai 8,000 da suka sami gurbin karatu a sassan 76 a tsakanin tsangayoyin jami’ar 12.   Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya sake jaddada matsayar hukumar a kan duk wani nau’i na rashin da’a da kuma shiga kungiyoyin asiri.  ...
     Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...
    Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero...
    Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya...
    Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...
    Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya...