2025-02-26@21:00:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 40
«Rage Farashi»:
Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin. A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara...
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware. Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa....

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da...
Kafin ya zama sanata, ya yi majalisar dokokin ta tarayya da ya wakilci mabazar Toro daga 2011 zuwa 2018. An shirya masa jana’iza da ƙarfe 1pm a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairum 2025 a Masallacin da ke kofar gidansa da ke Gwarimpa, Abuja. Cikakken labarin daga baya:
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a...
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke...
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani...
Gillis-Harry ya ce, “NNPC bai da wata mafita illa kawai ya rage farashin litar mai a gidajen mansa, ba zai yiwu mutane suna ganin akwai gidajen mai masu sauki kuma su je gidajen man NNPCL.” Kazalika, Ukadike ya ce, tun da ana samun bambancin farashin litar mai a tsakanin matatar mai dangote da kamfanin NNPCL,...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...

Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin...
Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na...
Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya...
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya. Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba....
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da...
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin...
A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin. Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya...
A yau Asabar, bayanai a hukumance sun nuna cewa, fiye da fasinjoji tsakanin yankuna miliyan 304 ne suka yi zirga-zirga a fadin kasar Sin a ranar Juma’a, rana ta hudu ta hutun bikin bazarar bana, yayin da aka samu yawan ziyarce-ziyarcen iyalai wanda ya ingiza yawon shakatawa. Wannan dai shi ne karo na farko na...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...

Hukumar Gidagen Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran Ta Bada Sanarwan Kama Dan Rahotonta A Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye
A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma kara da cewa dan rahoton...
“Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar. Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar. A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara. Lokacin...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa...