2025-03-04@17:17:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1592

«zargi»:

    A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan...
    Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza...
    A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu  da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama suke daukarta a matsayin bi ta da kullin siyasa. Wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an diflomasiyya da yan siyasa da lauyoyi da kuma...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata...
    Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu  a kasar. Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen  50...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Sepp Blatter, da tsohon shugaban UEFA, Michel Platini, za su sake gurfana a gaban wata kotu a Switzerland kan zargin cin hanci da rashawa. Kotun ɗaukaka ƙara da ke Muttenz za ta saurari buƙatar ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasar, wanda ke son sake dawo...
      Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.   Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da...
      Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025.   Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu.   “Farawa daga yanzu,...
    A cewar ‘yansandan Ukraine, hare-haren Rasha sun raunata mutane a yankin Donetsk, sannan a ƙaramar hukumar Kherson, mutum biyar sun mutu, yayin da 13 suka jikkata, ciki har da ‘yansanda da suka je ɗauko gawar wani mutum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin...
    Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
    Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida...
    Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi...
    Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke...
    A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za...
    Haka kuma, an sake zaɓar Mojisola Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar bayan sauka daga matsayinta na kakakin majalisar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari. Rahotanni sun bayyana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai...
    Taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin (CPPCC) da za a fara ranar 4 ga watan Maris, da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da za a fara ranar 5 ga watan Maris, su kasance manyan taruka biyu na kasar Sin inda ake gangamin siyasa domin nazartar baya da kuma...
    A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio. A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar...
    Hukumar kula da gandun daji da filayen ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, namun dajin kasar ta Sin sun karu yadda ya kamata ba tare da cikas ba. Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau, yayin da...
    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa...
    Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) za ta gudanar da taron shekara-shekara daga ranar 4 zuwa ta 10 ga Maris a nan birnin Beijing, a cewar wani kakaki a yau Litinin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin...
    Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kira matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin dake shiga Gaza a matsayin abin damuwa. Jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na katse taimakon da take baiwa Gaza, yana...
    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin...
    Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana. Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar. HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali...
    Kamfanin gungun gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, zai watsa bikin bude zama na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC karo na 14 a gobe Talata 4 ga watan nan. Za a bude taron ne da karfe 3 na rana bisa agogon Beijing. Kuma shugaban...
    Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa  zuwa aiki. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin. A cewarsa,...
    Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa. NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C. Hakar ma’adanai: ILO ta horas...
    A wani yunkuri na kawo karshen bautar da kananan yara a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO ) ta horas da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kuma yakar bautar da yara a aikin hakar ma’adanai. Kungiyar da ke kula da wurare hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta shirya taron ne da...
    Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu. Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin...
    Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar. Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al’ummarta a watan na Ramadan. Mataimakin gwamnan...
    Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin...