2025-02-22@21:41:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1174
«haƙar ma adanai»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba. “Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a,...
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son...
Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu. Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. A...
Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Idan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. Ɗan Majalisa Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar. Ya kuma ƙara da cewa, Jam’iyyar NNPP...
Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993. Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban. Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’. Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar...
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su...
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram. An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Garba, ya nuna damuwa game da kalaman da ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi kwanan nan, inda ya zargi USAID da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram tallafi. Ya jaddada cewa Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya sama da shekara 10....
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato Masu sana’ar Gwari da abin ya shafa ’yan kasuwar Ɗan Magaji ne daga Ƙaramar Hukumar Zariya, a Jihar Kaduna. Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin waɗanda suka tsira, waɗanda suka ji raunuka, da kuma waɗanda aka sako bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu. Muhammad Zaharraddeen Sharaihu shi ne mutumin da ya kai wa ’yan...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu kuɗin Duniya ta fitar, Forbes ta zaɓi Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziƙi a duniya a shekarar 2024 da dala biliyan 13.4. Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 23.9, musamman saboda hannun jarin sa na kashi 92.3 na matatar man dangote, Aliko Dangote mai shekaru 67, ya sake zama ɗaya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya,...
Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina. Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe. Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa. Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar. Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi. Ya ci...
Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna. Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle. “Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare...
Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton ɓauna. Wata majiya ta bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle. “Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammada Bakir Qolibft yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen Asia a birnin Baku na kasar Azaibaijan. Qolibof ya kuma kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka yake yi na kwace gaza da kuma inda za’a maida Falasdinawa ba zai kai ga nasara ba. Qalibof ya yi allawadai wadai da shugaba Trump kan shishigin da yake yi a cikin...

Dubban Falasdinawa Sun Kauracewa Gidajensu A Dai-Dai Lokacinta Sojojin HKI Suke Fafatawa Da Dakarun Falasdinawa
Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu. Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali. Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka...
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Lita 60,000
Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare. A jiya Laraba ne dai aka kaddamar da sabbin makamai masu linzamin wanda ya sami halartar manjo janar Muhammad Bakeri da shi ne babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran. Shi kuwa janar Ali Kuhistani da shi ne mataimakin kwamandan rundunar ta IRGC a fagen kayan yaki, ya ce; Sabbin makamai sun kunshe da kayan aiki na zamani masu muhimmanci da aka hade su wuri daya....
An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya. Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya bayyana cewa; Yin aiki tare a tsakanin kasashen yankin yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin da duniya take cike da sarkakiya.” Haka na kuma ya kara da cewa: Kai wa ga nasara a wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci fiye da kowane lokaci a baya. Kamfanin dillancin labarun “Anatol” na Turkiya ya nakalto ministan harkokin wajen kasar yana yin ishara da babbar dama da...

Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira
Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira. Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu. Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka...
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a...

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba. Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata. Sai dai wannan sanarwa na ci gaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati. NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake doke Manchester City da ci 3 da 1 a filin wasa na Bernabeu. Madrid ta karɓi baƙuncin Man City a wasan zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai, bayan doke ta a gida da ci 3 da 2. Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Kylian Mbappe ne ya zama tauraro a wannan wasan, inda ya jefa wa Manchester City ƙwallaye uku rigis a raga. Ɗan wasan gaban na Real Madrid, ya fara jefa ƙwallo ta farko a minti na 4 da fara wasa, sannan ya jefa ƙwallo ta biyu a minti na 33. Bayan dawowa daga...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu. A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da J-Teach, da J-Agro, da J-Health, da J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya. A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna...
Kafofin yada labarai da manazarta na kasa da kasa, sun jinjinawa babban taron ‘yan kasuwan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da aka gudanar ranar Litinin, inda suka ce gwamnatin Sin na marawa wadannan kamfanonin baya wajen taka rawar gani a bangaren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, kuma Sin ta gabatar da sako mai yakini na karawa wadannan kamfanoni kwarin gwiwar bunkasuwa. A wannan taro dai, ba nanata niyyar nacewa ga manufofi masu tushe da ake bi wajen raya kamfanoni masu zaman kansu a nan kasar Sin kadai aka yi ba, an kuma gabatar da alkiblar samun ingantattun ci gaba yadda ya kamata a wannan bangare. Hakan ya sa, “kwarin gwiwa” ta sake zama muhimmiyar kalma ga kasashen waje don...
Sin Ta Tabbatar Da Goyon Bayanta Ga Kafa Kasashe Biyu Ga Isra’ila Da Palasdinu
Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida. Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar. Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi. Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa. Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin,...
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci. Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.
Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa. A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.” Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya. Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar lissafi a shekarar 1989. Ya kuma yi babbar Difloma ta a fannin Sufuri sannan ya halarci kwasa-kwasan da dama, da tarukan karawa juna sani. Hakazalika memba ne na kungiyar masana harkar sufurin jiragen sama ta Birtaniya, wato Aeronautical Society, UK, da Ƙungiyar Binciken Sufurin Jiragen Sama, da...

Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimmancin kara inganta taimakekkeniya a tsakanin kasashensu. Shugaban na Iran ya fada a yammacin yau Laraba cewa: Ci gaba da tarukan tsakanin jami’an kasashen biyu ke yi na tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai jaddada karfafa alaka da kasashe makwabta, musamman kasar Qatar, a matsayin wani muhimmin ka’ida na manufofin ketare na Iran. Shugaban kasar ya ci gaba da...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa. Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin....
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3 Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki. Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu...
Ban da haka, idan mun mai da hankali kan cudanyar kasashe daban daban, da zamansu tare a cikin duniya, za mu san huldar da ake da ita tare da Amurka, wani bangare ne kawai na huldar kasa da kasa. Saboda haka, yayin da wata kasa ta gamu da matsala, idan wata kasa ta nade hannu, ba ta son ba da taimako, tabbas ba za a rasa bangarorin da ke son samar da taimakon ba. Matukar an yi kokarin kulla abokantaka bisa ra’ayi na daidaiwa daida, da amfanawa kowa, to, tabbas ba za a rasa abokin hulda ba. Sai dai idan mun nazarci sabbin matakan gwamnatin kasar Amurka, za mu ga kusan dukkansu na da nufin tsimin kudi da tabbatar da...
’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja. Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran itace. Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano Har ila yau, ya ce wani ɗan sa-kai na daga cikin waɗanda aka sace. “A halin yanzu, ’yan bindiga suna cikin dajin Akare. Sun sace ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai, kuma yana da bindigogi biyu a tare da shi...
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba. Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver. ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicinsa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe. “Mun bi dukkanin matakan da suka dace. An aiko mana da gayyata, jami’an gwamnati...
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki. Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada labarai na Nijeriya, don haka, shugaba Tinubu na yi masa fatan alkairi a rayuwa ta gaba mai zuwa da karin kaifin basira. Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba dan jaridan lafiya da samun biyan bukata a dukkan ayyukansa.
’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa Rubochi. Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano Wani ɗan uwan mamatan, Shuaibu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun nemi iyalan waɗanda lamarin ya shafa su biya wa kowa Naira 500,000 amma Naira 500,000 suka iya tattaraws baki ɗayansu. “Shugaban maharan ya kira mu ranar Juma’a, muka...
Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu. Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES). Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe. Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma. Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.” Shugaban shirin L-PRES...
A cewarsa, amincewar wani gagarumin yunkuri ne na tallafawa dorewar tsafar muhalli a jihar. Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar ‘yan jiharta da kuma tsaftar muhalli.
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin. Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025. “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.
Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Wata majiya ta bayyana cewa, wani kwamandan ’yan ta’addan mai suna Tar ne ya jagoranci garkuwa da mutanen ne a ranar 13 ga watan Fabrairu 2025. Tar da tawagarsa da ke addabar masunta da manoma a gaɓar Tafkin Chadi sun ɗauke mutanen ne yayin da suka afka wa al’ummar Shawaram da ke ƙarƙashin Ƙaramar...
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su ka shafi Gaza da kuma Amurka, kamar yadda kamfanin dilllancin labaun Mehr ya nakalto. Jakadan Jamhuriyar musulunci ta Iran a Qatar, ya saanr da cewa ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo Tehran tana a karkashin kokarin bunkasa alakar kasarsa da Iran.
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni. Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan gabar leken asiri, ta hanyar amfani da ‘yan kasashen waje da masu zuwa yawon bude ido. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin na Mazandaran ya kara da cewa; Da dama daga cikin wadanda suke leken asirin suna fakewa ne a karkashin kamfanoni na kasuwanci, cibiyoyin al’adu da kuma kungiyoyin agaji. Bugu da kari kwamandan na dakarun kare juyin juya halin musulunci a gundumar ta Mazandaran...
Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum. Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke da ita, ta samu dauki. Birnin al-Fasha dai shi ne babbar birnin jahar Arewacin Darfur, kuma sojojin na Sudan sun ce, suna ci gaba da kutsawa a cikin jahar. A gefe daya, wani jami’in sojan Sudan Yasir Adha, ya sanar da cewa; Babu yadda yaki zai tsaya har sai an ‘yanto da kowane taku daya na kasar Sudan daga hannun ‘yan tawaye. Adha ya bayyana...
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan. Bugu da kari makaman saman na Rasha sun kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki guda 4 a sararin samaniyar “Bahrul-Aswad”, sai kuma jirgi guda daya a saman yankin Tula. A gefe daya a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya. Sakataren...
Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.” Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a. “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.
A yunƙurin daƙile ta’adar garkuwa da mutane, Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta amince da dokar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin. Majalisar ta amince da ƙudirin ne wanda ta yi wa bita daki-daki yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata. USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin wanda shugaban marasa rinjaye, Henry Okaka ya goyi baya. A baya dai Majalisar Dokokin Edo ta ayyana hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane tare da ƙwace duk wani abu...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90. DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan. Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a...
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...

Ma’aikatar sharia ta kasar Iran Ta bada sanarwan Kama Yan Kasar Burtaniya 2 Tare Da Tuhumar Leken Asiri
Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar. Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba. Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran. Asghar Jahangir ya bayyana cewa...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususlunci A Iran IRGC Sun Bada Sanarwan Kai Hari A Kan HKI Karo Na Uku
Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar. Ya kuma kara da cewa, zasu kai harin don haka HKI da Amurka kawo mata yaki. Yace wadan nan kasashe suna neman yaki da JMI, amma mafi yawan shirin nasu na farfaganda ne. Amma dolene mu shiga yaki don mu hana yaki faruwa. Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran suna yaki ne don ladabtar da HKI don ta gane cewa JMI ba mai sauki....
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma Mali suka fice daga kungiyar sannan suka samar da sabon Passport a tsakanin kasashen uku, sai al-amura suka fara sauyi tsakaninu da Ecowas. Sun fara hana wadanda suke rike da Passpory na kasashen ECOWAS shiga kasashen ba tare da visa ba. Gwamnatin Nijer bata bada sanarwan fara aiki da wannan dokar ba. Kuma wani jami’in shige da fice na Niger ya ce umurnin ne aka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
A ranar 17 ga watan Fabrairu, agogon birnin New York ne, aka yi wani zama na musamman na nuna fim din Nezha 2 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kungiyar masu sha’awar karanta littattafai na kasar Sin dake MDD suka dauki nauyin shiryawa tare. Fiye da baki 150 da suka hada da mataimakin babban sakataren MDD Xu Haoliang, da jami’an diflomasiyyar kasashen Faransa, Rasha, Girka, Thailand da sauran kasashe a MDD, da ma’aikatan hedikwatar MDD, da ’yan jarida sun halarci bikin nuna fim din. Xu Haoliang, mataimakin babban sakataren MDD ya bayyana...
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’ Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta jihar. Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce gwamnan ya amince da dokokin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 25 da ya gudana a fadar gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’ Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta jihar. Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce gwamnan ya amince da dokokin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 25 da ya gudana a fadar gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da...
Idan Rana Ta Fito, Tafin Hannu Bai Iya Kare Ta
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja. Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya. Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci...
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata. A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar. Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin zaɓe da ya binciki Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC dangane da jinkirin da take yi na gudanar da zaɓen cike giɓin wasu kujerun ’yan majalisar tarayya da na jihohi. Majalisar a wannan Talatar ta kuma bayyana cewa jazaman ne kwamitin ya gayyaci Hukumar INEC domin ta bayar da dalilai kan tsaikon da aka samu da kuma yadda take ƙoƙarin yi wa tufkar hanci. Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta buƙaci kwamitin ya sauke wannan nauyi tare da miƙa mata rahoton bincikensa nan da makonni huɗu. Wannan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da wani...
Yawan kudin tikitin kallon fim din “Ne Zha 2” na kasar Sin da aka saya ya zarce dala biliyan 16 a daren jiya, abin da ya sa ya shiga sahun fina-finai 9 mafi samun yawan kudin tikitin kallon fim dake sahun gaba a duniya. Dalilin da ya sa fim din samun wannan ci gaba shi ne ingancin abin da ya kunsa. Labarin da wannan fim ya gabatar ya yi daidai da wasan yanar gizo mai suna “Black Myth: Wukong”, wanda shi ma na kasar Sin ne. “Ne Zha” da “Wukong” dukkansu jarumai ne dake cikin tatsuniyar gargajiya a dogon tarihin Sin, wadanda ba su mika wuyansu ga makomar da aka tanade su ba, kuma suka yi kokarin rike da kaddararsu...
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.
’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban. Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a kan Iran da al’ummarta ba ta cimma nasara ko yin tasiri ba. Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake karbar bakwancin dubban mutane daga lardin gabashin Azarbaijan a Husainiyar Imam Khumaini da ke Tehran fadar mulkin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar bore mai tarihi na al’ummar Tabriz a ranar 29 ga watan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta. Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk abin da yake so. Trump ya tabo batun mataki na gaba – ana sa ran za a fara tattaunawa nan ba da jimawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar – ya ce: “Ya rage ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan mataki na gaba, tare da tuntubarsa.” An kuma tambayi Trump ko jinkirin jigilar makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila a karkashin Shugaba Biden zai “hana tsagaita...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce damarsu ta samun nasara kan Real Madrid ’yar kaɗan ce a yayin da a gobe Laraba ƙungiyoyin biyu za su yi karon-batta a Gasar Zakarun Turai. Ana iya tuna cewa, a karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City da ci 3-2, minti huɗu kafin a tashi wasan. Hauhawar farashi ya koma kashi 24 a Nijeriya — NBS Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya To sai dai gabanin karawar ta biyu da za a yi a filin wasa na Bernabeu, a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ’yan 16, Guardiola ya ce damar da suke...
Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 3000 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...
EFCC Ta Cika Hannu Da Mutane 15 Kan Zargin Zamba Ta Intanet A Abuja

Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arazgchi ya kara jadda cewa JMI ba zata zauna a teburin tattaunawa da kasar Amurka ba a karkashin takunkuman tattalin arziki ba. Ya kuma kara da cewa Amurka ba zata iya tursasawa kasar Iran zama da ita ba. Ministan ya kara da cewa, ba zakin baki mukeso ba, sai mun gani a kasa a sanya hannu a dakardu sannan mu gani a kasa. Ministan ya fadawa tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye shiryenta da harshen larabcin a nan Tehran, ta kuma bayyana cewa, Trump ya bayyana cewa ya na bukatar tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya tun watan farkon waten Fabrairu amma ba abinda muka gani a kasa.
Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa. Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa. A wata wasika da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran. Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne. Duk da...
Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai kyautata al-amuran tsaro a yankin. Wanda kuma zai tabbatar da ikon kasar Lebanon a kan dukkan kasar ta. Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Lebanon ta bokaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar. Sannan bisa kudurin mai lamba 1701 na MDD rundunar UNIFIL zata taimaka wa sojojin kasar tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin HKI da kuma kasar Lebanon. Labarin ya kara da...
Jagoran al’umar yankin Neja Delta, Cif Edwin Clark ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU, suka zabi shugaban kasar Angola Joao Lourenco, a matsayin sabon shugaban karba-karba na kungiyar da kuma ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Djibouti, Mahamoud Ali Youssouf, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanar da ayyukan kungiyar, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasashe biyu masu matukar muhimmanci a nahiyar, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da kasar Sudan. Rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara kamari, bayan samun galaba a wasu yankunan kasar da ‘yan tawayen M23 suka yi, na baya-bayan nan shi ne kwace iko da muhimman wurare da dama a birnin Bukavu, hedkwatar...
Sojojin HKI Sun Bada sanarwan cewa ba zasu bar wasu tuddai guda 5 a kudancin kasar Lebanon ba, har zuwa wani lokacin da basu sani ba, saboda tsaron haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Almayadin ta kasar Lebanon, ta nakalto cewa tankunan yakin HKI sun kutsa cikin garin kafarshuba na kudancin kasar Lebanon kuma sun kafa sansanin sojojin a garin. A jiya litinin ce yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar Lebanon da suka mamaye, amma a jiyan din ne suka bada sanarwan cewa ba zasu fita daga wurare 5 daga kudancin kasar ta Lebanon ba. Kafin haka bayan kwanaki 60 da tsagaita budewa juna wuta ne, yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar ta Lebanon, amma tare...