2025-03-25@21:58:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1694

«Dokta Adamu ya»:

    Nasarar da Afirika Ta Kudu ta samu akan kasar Benin ya sa ta hada maki 13 a wasanni 6, kuma ta baiwa Nijeriya dake matsayi na 4 tazarar maki 6. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar  Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe. Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom. Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa. Wannan sakamako na nufin cewa Nijeriya na matsayi na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a...
    A shekarar 2024 da ta gabata, kamfanonin kasar Sin da masu bincike na kasar, sun gabatar da sabbin bukatun neman ikon mallakar fasaha har 20,081 ga ofishin rajistar ikon mallakar fasaha na Turai ko EPO, kamar dai yadda alkaluman shekarar 2024 da ofishin ya fitar a yau Talata suka nuna. Wannan adadi ya kai kaso 10.1 bisa dari na jimillar neman izini da ofishin na EPO ya karba a bara, wanda hakan ya tabbatar da Sin a matsayi na 4 cikin jerin kasashe mafiya gabatar da bukatar ga ofishin a duniya baki daya. A jerin kamfanoni dake cikin jadawalin na EPO, kamfanin Huawei na Sin na matsayi na biyu, da bukatun neman ikon mallakar fasaha har 4,322. Baya ga Huawei,...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya Duba daga  rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing. Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau Talata, inda ya ce daukacin mahalarta taron na karawa juna sani sun yi imanin cewa, a halin da ake ciki, ya kamata a karfafa ayyukan MDD, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kuma tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta a duniya. Kazalika, mahalarta taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ta taka...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?. Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima...
    Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da kayayyaki. Daga bisani me kasar Sin ta yi? Ta samar da tunanin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, inda aka nanata bukatar ba sauran mutane damar jin dadin zaman rayuwa, matukar wani mahaluki na son samun zaman rayuwa mai inganci. Bisa wannan tunani ne, kasar Sin ta samar da jerin shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar mabambantan...
    A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin. A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar. Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain.  Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da birnin Kaduna daga arewacin kasar a jiya Litinin. Badaru ya kara da cewa gwamnatin kasar tag a akwai butara da samar da irin wannan rundunar, saboda magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda aka dade ana fama das u, ko kuma wadanda suke tasowa nan da ca. Ya kara da cewa rundunar da aka kaddamar a jiya litinin bangare ne na runduna mai sojoji 800 da za’a...
    A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320. Hon. Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici. Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Nijeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa. Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi...
    Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa ƙungiyar kallon hadarin kaji, kan zargin ta gaza cimma wasu muradu da aka kafa ta a kai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun. Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata. Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a...
    Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.  A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar. Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa. Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin...
    Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu. Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su...
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya. “Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi. Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba motocin ɗaukar marasa lafiya na NAHCON, kayan magani, da shirye-shiryen kiwon lafiya a asibitocin Nijeriya da ke Saudiyya. Sun gano muhimman wuraren da ake buƙatar ingantawa, ciki har da wadatar magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin ɗaukar marasa lafiya. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, inda ya ce: “Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da muke yi...
    Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin kayan kiwon lafiya. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan ba a samu sabbin hanyoyin tallafi ba, yiwuwar ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar HIV na da matuƙar girma. Hakan na iya rusa nasarorin da aka samu a yaƙin da duniya ke yi da cutar. Ana ci gaba da kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji da su ceto shirin...
    Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu. Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu. Ya sanar...
    Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
    “SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba. “Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam....
    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mutum 2,000 sabbin kamuwa da cutar SIDA duk rana a faɗin duniya. MDD ta ce tana wannan gargaɗi ne sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin ƙasashen duniya ƙarƙashin Hukumar ta USAID. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas MDD ta ce ce tilas ne a maye gurbin taimakon idan ana neman kare duniya daga shiga annobar cutar ta AIDS.. Hukumar ta ce muddun Amurka ba ta dawo da tallafin daƙile cutar ba, kuma ba a samu maye gurbin taimakon na Amurka ba, nan da shekaru huɗu za a samu kimanin mutane...
    Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai linzami guda biyu da suka hada da Zulfiqar mai gudun tsiya. Ya kara da cewa hare-haren na goyon bayan Falasdinawa ne a Gaza. Saree ya yi nuni da cewa, dakarun kasar Yemen sun kuma kai hari kan jirgin yakin Amurka Harry S. Saree ya ce harin da aka kai kan jiragen ruwan yakin Amurka shi ne irinsa na biyu cikin sa’o’i 24 da suka gabata....
    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci. “Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza. “Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta. Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin. Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam. A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai. Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a...
    Misalan Wannan Hassada: 1. Hassadar Fir’auna a Kan Annabi Musa (AS): Fir’auna ba ya son aiken da Allah Ya yi wa Annabi Musa (AS) ba, domin yana tsoron cewa mulkinsa zai ƙare. Ya so cewa wannan matsayi na shugabanci da iko ya kasance a gare shi kawai. Allah Ta’ala Ya ce:” Fir’auna kuma ya ce: ‘Ku bar ni in kashe Musa, kuma ya je ya kira Ubangijinsa! Lallai ni ina tsoron ya canza addininku, ko kuma ya bayyana ɓarna a cikin ƙasa.'” Suratu Gãfir aya ta 26. Fir’auna bai so wani ya sami iko ko shugabanci sai shi, don haka ya so ya kashe annabi Musa (AS) domin mulkinsa ya dore. 2. Hassadar Ƙuraishawa ga Annabi Muhammad (SAW): A lokacin...
    A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a dangantakar Sin da Amurka, ya dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma fatan al’ummomin duniya baki daya. Dangane da rikicin Ukraine kuwa, Guo Jiakun ya ce a baya-bayan nan, kungiyar “Kawancen zaman lafiya” kan rikicin Ukraine ta gudanar da wani taro a birnin New York, domin tattauna halin da ake ciki game da...
    A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki. Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa kaimi wajen ingiza yakin cinikayya, ‘yan siyasa da wakilan manyan kamfanonin Amurka na haye wahalhalu inda suke ta kawo ziyara Sin, wanda hakan ke nuni ga matukar goyon baya da salon bude kofar cinikayyar duniya ke samu, da kuma fatan da ake yi na samun cikakken daidaito, da hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ko shakka babu, matakin Amurka na...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota. Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas Ya ce rundunar ta samu nasarar kama wanda ake zargin ne bisa tallafin wasu jami’an ƙungiyar masu sufurin motocin haya (NURTW). Kazalika, ya ce sun kama wanda ake zargin ne ɗan asalin Jihar Katsina, ɗauke da harsashi 488 na bindigogin AK-47...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin. He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen...
    Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin mutane na samun ingantacciyar rayuwa ta zama gaskiya. Shekaru 12 da suka gabata, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki ta farko a matsayinsa na shugaban kasar Sin, ya gabatar da wannan ra’ayi mai cike da hangen nesa. Tun daga wannan lokacin, ra’ayin ko tunani ya bunkasa zuwa wani tsari na musamman da ake aiwatarwa, tare da samun kaso mafi girma...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na shirin raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus na shirin maye gurbin Thiago Motta da tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Igor Tudor. Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Juventus dai za ta ɗora wa sabon kocin nauyin jajircewa wajen ganin ƙungiyar ta ƙare a cikin sahun huɗun farko na teburin Gasar Serie A ta bana, domin samun damar buga Gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa....
    Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke ta ne a yayin binciken shigowarta daga jirgin Qatar Airways daga Bangkok ta Vietnam da Doha. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd), ya ce wannan kamun ya sake nuna yadda masu safarar kwayoyi ke amfani da ‘yan ƙasashen waje don kutsawa da miyagun kwayoyi cikin ƙasar. A cewarsa, NDLEA na ci gaba da daƙile irin wannan yunƙuri ta hanyar bayanan sirri da fasahohin zamani....
    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan. Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye,...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita. “A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza. Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin...
    Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci Bayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi. Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen ɗantayin da ba nata ba, bayan an tilasta ta, ta mayar wa asalin iyayen jaririn ɗansu. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Krystena Murray, mazauniyar Jihar Georgia, ta ɗauki cikin ne bayan dashen ɗantayi na (IBF) da aka yi mata a asibitin masu neman haihuwa da ake kira Coastal Fertility Clinic,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin  a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu. Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya. Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan kusoshin Hamas, wanda yake a kan gaba wajen gwagwarmaya da  sadaukarwa, ya yi shahada a kan tafarkin gaskiya. Bayanin ya ci gaba da cewa: Bai taba gazawa wajen gudanar da ayyukansa na jihadi da hidima ga al’ummar Palastinu ba, ya kuma ci gaba da yin gwagwarmaya kan turba ta gaskiya da neman ‘yanci har zuwa karshen rayuwarsa. Hamas...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu, yayin da wasu kuma ke haɓaka. Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma haɓaka a wasu sa’anni. NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    Mataki na uku shi ne mutum ya so samun irin wannan ni’ima kamar yadda wani yake da ita, ba tare da yana so ta gushe daga hannun wanda yake da ita ba. Wannan kuwa ba hassada ba ce, sai dai ana kiranta da fatan alheri ga kai.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [4/226] Fashin Baƙi: Ibn Juzai al-Kalbi ya bayyana mana rabe-raben hassada. Inda ya ce: ● Matakin Farko na Hassada: Shi ne mutum ya so wata ni’ima da Allah Ya ba wa wani ta gushe daga gare shi, ko da kuwa ba zai amfana da ita ba. Wannan shi ne mafi munin nau’in hassada gaba ɗaya, kuma yana ɗaya daga cikin manyan cututtukan zuciya da ke hana albarka a...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki. Sai dai a daya hannun, kasar Sin na kara fadada bude kofarta. Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da...
    A yau Lahadi ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin na 2025 a nan birnin Beijing, taron da cibiyar binciken raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar asusun binciken raya kasa na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude taron, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, wanda a cikinsa ya jaddada aniyar kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje. Shi ma mataimakin darektan ofishin kula da harkokin yau da kullum na hukumar kudi da tattalin arziki ta kwamitin kolin JKS Han Wenxiu, wanda ya halarci taron na shekara-shekara, ya ce kasar Sin za ta dauki dukkan matakai na habaka kashe kudi, da...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.  Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Islami yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan ci gaban kari ne, kan ci gaban da kasar ta samu a wannan fannin, wanda kuma zai kara kyautata bangaren lafiya na kasar sannan ya zama hanyar samar da kudade ga kasar. Shugaba hukumar makamashin nukliya ta Iran ya kara da cewa a cikin shekarar Iraniyawa wanda ya kara kadai kasar...
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaba Putin shawara kan al-amurin siyasa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa Sanata Georgy Karasin ne zai jagoranci tawagar masu tattaunawa ta kasar Rasha sannan ta kasar Amurka an rika an samar da tawagar, wasu zata hadu da na Rasga a gobe litin a birnin...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan, hadin gwiwar Sin da Amurka bai taba zama na wani fanni ya ci riba dayan ya yi asara ba. Maimakon haka, kaso 41 bisa dari na kamfanonin Amurka dake kasar Sin na daukar Sin a matsayin kasa ta biyu a duniya, wajen samun ribar hada hadar kasuwanci. Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty An Kashe Askarawa 6 da...
    Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
    Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara. Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar. An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno A yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti. Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma...
    Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga watan Maris, 2025, ɗansa ya ɓace. Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi Washegari, wani ya kira shi a waya yana neman kuɗin fansa. Da farko, ya nemi miliyan uku (₦3,000,000), amma daga baya suka rage zuwa Naira dubu ɗari biyu (₦200,000). A ranar 21 ga watan Maris, aka gano gawar yaron a cikin...
    Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun. Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na majalisar Dattawa, wadanda su basu samu damar rubuta jarabawar da zata basu damar zuwa manyan makarantu ba a fadin tarayyar Nijeriya. “Ilimi shi ne wani babban abinda ya kamata kowane dan/ ‘yar kasa su kasance sun samu damar yin haka ta samun sa, don haka lamarain kudi bai dace ace ya hana su damar samun hakan ba musamman ma ga matasa wadanda sune manyan gobe...
    Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke Jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai. Wakilin Aminiya ya ziyarci garin domin gani da ido, inda ya ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya hadiye su, sun nutse a cikin ruwa. Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu Garin na Zip da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba yana bakin Kogin Biniwai ne, kuma mafi yawan mazaunansa masunta ne da manoma. Sun kuma bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru da yadda suka tsallake rijiya da baya da irin asarar da suka...
    Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko. A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa...
    An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya. Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar ranar 21 ga Maris, 2025, a lokacin da wasu matasa suka tsaya a gaban ofishin dakarun da ke Unguwar Bakin Kasuwa, a Karamar Hukumar Monguno. Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu Yadda ake noman gurjiya Majiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta. Wadanda abin ya shafa — Ya’zainab Bum da...
    Ana sa ran, za a yi jana’izarta yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin 4 na yamma (4pm) a garin Radda, ƙaramar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina.   Hajiya Radda, jigo ce da za a rika tunawa da ita bisa hikima da juriya wanda hakan ya yi tasiri matuka ga iyalai da makusantanta.   Allah ya jikan Hajiya Safara’u Umaru Barebari, ya albarkaci zuri’arta, ya sa ta huta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan. An kashe shi ne tare da matarsa ​​a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza. Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.
    Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan wasan bayan kungiyar Iñigo Martinez yana da kumburi a gwiwarsa ta dama, za a yi wa dan wasan magani a Barcelona karkashin kulawar ma’aikatan lafiya na kungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    A tattaunawarsa da Aminiya wani manomin gurjiya, Malam Muhammad Dahiru Kanda ya bayyana cewa, ya shafe sama da shekara 25 yana noman gurjiya ba tare da ya taba samun wani tasgaro ba. Ya kara da cewa, shi noman gurjiya na da muhimminci matuka domin kuwa yana samar wa duk mai yin sa babbar riba. Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo A cewarsa, noman gurjiya noma ne da bai sai ka tanadar masa babbar gona ba, ya danganta ne ga yadda duk ka dauke shi, amma kuma ko da rabin hekta ka dauka, ka noma, matukar ka gyara ta to kuwa ko tantama babu in...
    A cewarsa, domin tabbatar da gudanar da wannan tantancewar, an samar da kwakkwaran kwamitoci a matakin jiha da kananan hukumomi tare da sauran sassan hukumomin da ke da alaka da kudi, sannan an ba su umarni samar da dukkan bayanan biyan albashin nan take. Farouk ya bukaci ma’aikatan da matsala ta shafa su kai kansu gaban hukumominsu tare da nagartattun bayansu kan dalilin kin bin wannan umarni, saboda a kula da sabunta kundin biyan albashin. Ya ce Mambobin kwamitin sun hada da manyan sakatarorin daga manyan ma’aikatu, wakilai daga kwamitin tsara jadawalin albashi da kuma wasu manyan jami’an a ofishin sakataren gwamnatin Jihar Kano. Sannan ya jadadda cewa bin wannan umarni ya zama wajibi. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Ita maganar bada damar tsayawa takara ba tare da zaben fidda gwani ba an dauki matakin ne saboda yadda aka ga ‘yan adawa ko jam’iyyun adawa suke kokarin tayar da babbar kura mai hayaki,wa ita jam’iyyar mai rike da kambun mulki a 2027 domin “Ba a san maci Tuwo ba sai Miya ta kare”. Ana dai ganin tarurrukan da aka yi na mambobin APC,wadanda suke ganin ba,a kyauta masu ba da kuma Shugabannin adawa suna yin wani shiri wanda zai iya sa wasu daga cikinsu su yi jerin Tururuwa na komawa jam’iyyar SDP,kamar dai yadda tsohon Gwamnan Jihar Kaduna,Malam Nasiru El Rufa’i ya fara kasancewa na farko wanda ake ganin akwai wadanda za su iya goyo masa baya. Idan dai...
    Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata. Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin da aka kai a kauyen Fonbita da ke cikin kauyan Kokorou dake jihar Tillabery wanda ya faru a lokacin da wasu ‘yan ta’addan na kungiyar Da’ish a yankin Sahara (ISGS) suka far wa masallacin, inda suka auka wa masu ibada dake sallar Juma’a. Baghaei ya bayyana cewa, wannan ta’addancin da aka aikata a lokacin sallar Juma’a ya saba wa ka’idar Musulunci, kuma ya saba wa...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar da lada na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tare da bayyana Haqqani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo. Kawo yanzu dai babu wani martani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka dangane da matakin. Haqqani shi ne shugaban kungiyar Haqqani, wata kungiya mai karfi a cikin kungiyar Taliban wacce ta shahara wajen ayyukanta da makamai. Duk da ayyana shi a baya a matsayin “dan ta’adda na...
    Kallo ya koma sama bayan da mata suka karbe ragamar kasuwancin kayan lambu a a tsakiyar birnin Gombe, inda a baya kasuwancin kayan ya kasance a hannun maza kadai na tsawon lokaci. Wannan sabon sauyi ya da ya taso a hankali ya faru ne a sakamakon matsalolin kudi da nauyin kula da kai da kuma iyali da suka tilasta matan aure da zawarawa da ma ’yan mata da dama, suka tsunduma harkar wadda a baya ake kallo a matsayin ta maza kadai a wasu yankunan Arewa. Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi Amma a halin yanzu a wani sashe na Babbar Kasuwar...
    Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.  A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.8 da ta yi sanadiyyar mutuwar dubun-dubatar mutane tare da mayar da daukacin unguwanni tamkar kufai. An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan Ali Bozoğlan, mahaifin ‘ya’ya uku daga lardin Hatay da ke kudancin kasar, ya rasa gidansa sakamakon girgizar kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu 2023....
    ● Ta biyu, yana nuna rashin ladabi ga Allah, domin ainihin hassada ita ce jin haushin yadda Allah Ya ba wa wani ni’ima, kuma hakan yana nufin yana sukar hukuncin Allah. ● Ta uku, zuciyarsa tana shan wahala saboda yawan damuwa da baƙin ciki.” Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [14] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13] Fashin Baƙi: Ibn Juzai Allah Ya ji ƙan sa, ya yi cikakken bayani kan illolin hassada ga mai hassada ta hanyoyi guda uku: samun zunubi, da rashin ladabi ga Allah, da wahalar da zuciya. Zan ɗan yi bayani a kan waɗan gaɓoɓi guda uku da malam ya ambata, tare da hujjoji daga Alƙur’ani, da Hadisi, da mahangar masana ilimi. Ga...
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan. Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Yana mai cewa, an fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu da wuri, inda aka samu sakamako da dama, kuma tana da babban tasiri, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar...
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare hakkin dan Adam da kin amincewa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Chen Xu ya yi nuni da cewa, ana bukatar bin ra’ayin bangarori daban daban da tunanin kare hakkin dan Adam da yin hadin gwiwa mai amfani don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam. Wasu kasashe sun yi amfani da dalilin kare hakkin dan Adam wajen tsoma...
    Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa, daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yin jana’iza. Kakakin ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna samun labarin lamarin, jami’ansu suka fara bincike, musamman a wajen POS da ke kusa da inda aka nemi a biya kuɗin fansar. A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka, wanda lambar wayarsa aka yi amfani da ita wajen kira mahaifin yaron. Sun kuma gano asusun bankin da aka bayar don a biya kuɗin fansar. Da aka tambayi Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozoichikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yin garkuwa da yaron. Sannan ya ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi) mai...
    Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma. Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a fannin aikin noman kasar, domin kasar ta cimma burin da ta sanya a gaba, musamman domin Nijeriya ta rage asarar da take yi a yayin girbin amfanin gona da samar da kayan aikin noman rani da sauran makamantansu. Dakta Heike Harmgart, Manajan Daraknatan Bankin na EBRD da ke kula da yankin Afirka, wadda kuma ta jagoranci tawagar a nata jawabin ta ce, tawagar ta kawo...
    KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin  Istanbul. Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa. Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa. Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa...
    A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa  Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda  nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki. Wajibi ne mu zauna mu tattauna.” Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran. Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi. Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din...
    Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa...
    Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya. Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya. An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Channels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja. Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na...
    “Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi. Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya. A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a al’adun Bauchi, inda sarakuna da masu riƙe da mukamai ke hawa dawakai cikin shiga ta alfarma, tare da nuni da al’adun gargajiya. Hakan yana jan hankalin jama’a da yawon buɗe ido daga sassa daban-daban. Masarautar Bauchi ta jaddada cewa ba a bayyana haƙiƙanin labari ba, kuma kwamitin da ke kula da hawan ne ya nemi a soke bikin da farko. Sai dai bayan shawarwari, yanzu...
    Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana. Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon hadiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram. Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Lokacin da ta fara amai,...
    Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema a Amahoro. Wasan shi ne zagaye na biyar a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a buga a shekarar 2026, Nijeriya na matsayi na 4 a rukunin C na gasar da maki 6 a wasanni 5, sai Afrika Ta Kudu dake jan ragamar rukunin, ƙasar Benin ta biyu sai Rwanda dake matsayi na uku. Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed...
    Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake mutunta gasa mai tsafta, amma kuma ya na fifita hadin kai da ci gaban kasa fiye da komai. Shugaban IPAC na kasa, Honourable Yusuf Dantalle, ya ce shirin fim din na tarihi zai bayyana ci gaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da hadin kan al’umma, ya kuma ci gaba da “Fim din zai zama wani muhimmin tarihin kasa,...
    Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wannan ya sa Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba. Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi. Yarinyar, wacce...
    Ya sanar da cewa, yanzu a Hukumar ana kara samun nada mata kan madafun iko, inda ya sanar da cewa, a yanzu a Hukumar mace ce, ke rike da mukamin Babbar Darakta ta sashen kudi da mulki wato uwargida Bibian C. Richard-Edet. A cewarsa, a shekarun baya, akalla muna da mata sha biyu da suke rike da mukamain Janar Manaja da kuma mukamain Manajoji a Hukumar Shugaban ya bayyana cewa, mata na ci gaba da bayar da gudunmawar su wajen habaka fannonin da ke a Hukumar ciki har da bangaren tsaro, kiwon lafiya da sauransu. “Wadannan wasu misalai ne ‘yan kadan da Hukumar ke yi na inganta ‘yancin mata da tabbatar da ‘yancin su, duba da cewa, bamu iyakance irin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bubu da kari, abin mahimmancin shi ne, shi talakan Nijeriya zai iya gani a kas na irin wadannan shirye-shiyen da gwamnatin ke son aiwatarwa?   Fannin Da Gwamnatin Za Ta Zuba Kudaden: A kasafin kudin na 2025, Gwamnatin Tarayya ta warewa bangaren tsaro Naira tiriliyan 6.11 wanda ya kai ta samar da karin kaso 88 daga cikin kasafin kudin da ta warewa fannin na Naira tiriliyan 3.25 a 2024. Shin wannan burin na Gwamnatin zai iya cika, duba da yadda aka gaza dakile ta’addanci, ‘yan fashin daji, wanda idan ba a mayar da hankali ba, a 2025, tarihi ne zai sake mai-maita kansa. An ware Naira tiriliyan 5.99 a cikin kasafin kudin don yin tituna, gadoji da kuma manyan ayyuka...
    Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas. Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun. Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin...
    “Saboda haka, za a soke sunayen kadarorin da suka shafe sama da shekara goma ba a biya musu haraji ba nan take, Bugu da kari kuma, ana bayar da wa’adin kwanaki 21 ga masu rike da gidajen da ake rike da bashin kudin haraji na tsawon shekara daya zuwa goma, sannan kuma za a soke sunayensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kai hari wani masallaci da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani matashi yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud. Sai dai rundunar ’yan sandan jihar, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kai hari masallacin. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce ’yan daban sun fito daga unguwanni daban-daban kamar Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko. Sun kai farmaki Masallacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalin ƙarfe 2 na dare yayin da masu mutane ke sallar Tahajjud. Kafin jami’an tsaro su isa wajen,...
    An gudanar da Sallar Juma’a a mako na uku na watan Ramadan a Masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da tsauraran takunkumin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta dauka, tare da halartar Palasdinawa 80,000. Kamfanin dillancin labaran Al-Naba y bayar da rahoton  cewa, dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa, duk da matakai na kawo cikas da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka dauka da kuma yanayin sanyi da ruwan sama a birnin Kudus. Hukumar kula da lamurran addinin Musulunci a birnin Kudus ta bayar da bayanin cewa, masallata 80,000 ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa. Sheikh Khalid Abu Juma, limamin masallacin Al-Aqsa, ya...
    Majalisar wakilai ta tarayya ta yi watsi da zargin da ake yi ga ‘yan majalisar tarayya na cin hanci da rashawa domin marawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya na ayyana dokar ta baci a jihar Ribas. Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram daga jihar Jigawa, Honarabul Yusuf Shittu Galambi, ne ya kare majalisar a yayin da ake ta cece-kuce kan batun kafa dokar ta-baci a jihar Ribas, inda wasu kungiyoyi ke zargin majalisar dokokin kasar da yin kasa a gwiwa wajen yanke hukunci. Sai dai, Galambi a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, ya ce babu gaskiya a ikirarin na cewa an tursasa ‘yan majalisar kan matakin da shugaban kasar ya dauka. A cewarsa, yawancin mambobin sun...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kai hari wani masallaci da ke yankin Tudun Wada a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani matashi yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud. Sai dai rundunar ’yan sandan jihar, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kai hari masallacin da ke Tudun Wada a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce maharan sun fito daga wurare daban-daban kamar Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko. Sun kai farmaki Masallacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalin ƙarfe 2 na dare yayin da masu...