2025-02-26@14:55:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9
«a kudancin Syria»:
A farko-farkon da masu dauke da makamai su ka kwace iko da birnin Halab, jami’an gwganatin Turkiya sun kaucewa yin Magana akan abinda yake faruwa. Sa dai kuma da yake mai kaza a aljihu ba ya jimirin cas, ba a je ko’ina ba, su ka fara furta kalaman da suke nuni da cewa, Da kawai rina a kaba. Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan, ya yi tsokaci akan abinda yake faruwa a Syria, ya zargi tsohuwar gwamnatin Syria da cewa; Ba ta yi aiki da bangarorin yarjejeniyar Astana ba.” Sojojin Turkiya suna cikinm kasar Syria tun a farkon 2018, inda suke mamaye da kaso 10% na yankin wannan kasa. Kuma aiki a tare da masu adawa da gwamnatin Damascuss,musamman rundunar...
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen Damascus babban birnin kasar da kuma lardin Deraa da ke kudancin kasar. Hare-haren dai ya biyo bayan kiran da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na karbe yankin kudancin Siriya baki daya.” Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta kuma bayar da rahoton cewa, Tel Aviv ta fara aiwatar da wani shiri na “shiga kudancin Syria. Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a kudancin Syria a daren Talata, yana mai cewa harin wani bangare ne na sabuwar manufar Isra’ila ta “kawar da ayyukan soji a kudancin Syria.” A cikin...
Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin. A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula zaman lafiya a yankin shi ne yadda Isra’ila ke ci gaba da mamaye yankin Golan na klasar Syria.” Sauran abubuwan da ke haifar da rashin zaman lafiya, a cewar wakilin Majalisar Dinkin Duniya, su ne yadda “Isra’ila” ke hana ‘yan kasar Lebanon da suka rasa matsugunansu komawa gidajensu a Kudancin kasar, da kuma ayyukan tada hankali da ta yi ta hanyar kai farmakin soji a...

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba. Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan...
Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun yi musayar sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye. Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece cewa, Muna cikin shiri da tanadin sake dawo da alaka da kasar Syria anan gaba. Har ila yau. Shaibani ya ce; Muna bin diddigin abubuwan da suke faruwa a Syria, kuma za mu dauki matsaya a lokacin da ya dace.” Haka nan kuma ya ce; Muna kallon Syria ne a matsayin kasa wacce take da matsayi a cikin yankin yammacin Asiya, kuma mun yi imani...
Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki. A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo karshen yakin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa. Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta karin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.
Rahotanni da suke fitowa daga kasar Syria sun ce, ana ci gaba da yi wa daidaikun mutane kisan gilla a sassan kasar mabanbanta. A kusa da garin Hamah, an kashe mutane 7 a bayana nan, bayan da wasu masu dauke da makamai su ka shiga cikin garin Tal-Zahab. Masu dauke da bindigar sun kutsa gidan fararen hula tare da bude wuta a kansu. Haka nan kuma maharan sun yi sata a cikin gidajen da su ka shiga. An gano gawawwakin mutane 7 a cikin wadannan gidajen bayan ficewar maharan. An harbi mutanan ne dai a kai da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Kamfanin dillancin larabdun “Sputnik” ya nakalto cewa, masu dauke da makaman sun kuma kame mutane da dama daga...
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa. Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito. Jami’an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu. Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau’in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba,...