2025-04-03@02:17:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 42

«bada sanarwan»:

    Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi.   Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya. Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama. A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi. Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan...
    Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu-  Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah. Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba. Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook. Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki...
    A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.” Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya  Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah. Yadda ake fitarwa Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda...
    A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa. Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki. Sai dai a daya hannun, kasar Sin na kara fadada bude kofarta. Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da...
    Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa yake yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai yake yi. Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba. Ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba. Ban ce ina tarbiyyantarwa ba. “Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi ne....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha.     A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara.   Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa.   Adamu wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tsare-Tsare Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ya bayyana jin dadinsa ga majalisar a yayin zaman majalisar.   Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore ya bukaci Adamu da ya kara samun nasarori a KNUPDA tare da yi masa fatan Alheri a sabon mukaminsa.   Nadin Adamu ya yi daidai da...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya. Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na Maris, zai kuma kunshi karin kaso 100 bisa mai rapeseed, da tunkuza, da waken peas, yayin da kuma albarkatun teku, da naman alade da ake shigarwa Sin daga Canada, aka yi musu karin harajin kaso 25 bisa dari. Mahukuntan kasar Sin sun ce matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da nuna banbanci a hada-hadar cinikayya, wanda ya tabbatar da cewa, matakan da...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci. An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu. Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan. Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba. Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za...
    Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN Ali Muhammad Ali ya ce manyan taruka biyu na kasar Sin wato taron NPC da CPPCC sun zama muhimmiyar hanya ta fahimtar manufofin da gwamnatin Sin ke dauka da yadda take daidaita harkokinta da basirarta na zamanantar da al’ummar Sinawa. Ali Muhammad ya bayyana haka ne yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, “Da farko mun zura ido kan nagartattun manufofin da Sin take dauka na daidaita harkokinta, wadanda tarukan biyu suka gabatar da su da sakamakon da take samu dangane da hakan a fili, manufofi kuma sun sauke nauyin dake wuyansu. Musamman ma a halin da duniya ke ciki na fuskantar manyan sauye-sauye, dabaru da...
    Shugaban  kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar. Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma. Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.
    Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat  wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma bakin Isra’ila a cikin harkokin wannan yankin, musamman abinda yae faruwa a kudancin Syria. Dan siyasar na kasar Lebanon  wanda ya yi taron manema labaru a jiya Lahadi ya yi gargadi akan yanayin da ake ciki a yankin “Jabalu-Duruz” da tsoma bakin HKI domin haddasa rashin tsaro a cikin wannan yankin. Haka nan kuma ya yi tuni da yabo akan tarihin gwgawarmayar ‘yan Duruz’ da...
    Rundunar Basij a yankin kudu maso gabacin kasar Iran ta bada sanarwan shahadar dakarunta guda biyu a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran, ya nakalto rundunar IRGC na yankin ya na bada sanarwan shahadar Hojjatoleslam Sadeq Mahmoudi da kuma Milad Damankesh a lokacinda suke komawa gida daga wurin aiki a cikin wata mota tasu. Labarin ya kara da cewa shahidan biyu sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda wasu yan ta’adda suka bude wuta a kan motarsu a lokacinda suke wucewa a wata unguwa zuwa gidajensu. Lardin Sitan Baluchistan wanda ke kan iyaka da kasar Pakistan dai ya dade yana fada da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke shigowa kasar daga kasar Pakistan, wadanda kuma suke samun taimako...
    Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya: 1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya: A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100. 2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce: Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.   Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.   Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa.   Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci.   Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da...
    Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami  ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu  kara  yawan wutar lantarkin da muke samarwa da  megawati 2000 a kowace sa’a daya  daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5. Zangon dai zai kare ne a cikn watan Maris 2029. Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.
    Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping. Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai...
    Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da DSS sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Ƙofar Nasarawa da ke Jihar Kano. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun yi dandazo a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa, lamarin da jami’an tsaron suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan Kawo yanzu dai ba a gano dalilin gudanar da zanga-zangar ba, sai dai tuni jami’an tsaro suka sanya shamaki a hanyoyin da ke daura da zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
      dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
    Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin yin sabon zaɓen ƙananan hukumomi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Ministan ya ce kotu ta dawo da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gboyega Oyetola, amma ta tsige su ta hanyar umarnin zartarwa da gwamnan...
    Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar. Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba. Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran. Asghar Jahangir ya bayyana cewa...
    Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar. Ya kuma kara da cewa, zasu kai harin don haka HKI da Amurka kawo mata yaki. Yace wadan nan kasashe suna neman yaki da JMI, amma mafi yawan shirin nasu na farfaganda ne. Amma dolene mu shiga yaki don mu hana yaki faruwa. Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran suna yaki ne don ladabtar da HKI don ta gane cewa JMI ba mai sauki....
    Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu sun fito ne daga Jihar Ogun. An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu sun fito ne daga Jihar Ogun. An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi
    Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
    Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
    A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
    Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek. Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza. Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15. A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan...
    Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
    Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.   Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.   Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.   Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
    A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma  kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
۱