2025-02-22@15:30:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 483

«Askira Uba»:

    Bayan bincike ta hanyar fasaha, an gano inda wayarta take, wanda hakan ya kai ga kama Abdulrahman Bello. Lokacin da aka kama shi, ya amince da laifin kisan Hafsoh da nufin yin sihirin kudi (oshole/ajoo owo). A binciken da aka yi a gidansa, an samu: Wayoyi biyu da takalmin mamaciyar Hannaye da aka sare daga...
    Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa dai tana fatan fahimtar juna. Shugaban gwamnatin kasar ta Jamus; Duk wanda yake son nahiyar turai ta shiga cikin batun zaman lafiya, to dole ne ya yi tarayya da ita...
    “Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.” Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare...
    A wani zanga-zangar lumana da suka gabatar a jiya Asabar masu goyon bayan kungiyar Hizbullah sun yi kira ga gwamnatin kasar Lebanon kada ta bari Amurka da HKI su zama su ne ke jajjuya al-amuran kasar. Tashar talabijan ta Presstv  a nan Tehran ta nakalto Mahmood Qamati shugaban kwamitin siyasa na kungiyar Hizbullah ya na...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya  kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta  “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake...
    Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin...
    Jakadan Amurka na musamman kan kasashen Rashad Ukraine ya bayyana cewa Amurka tana kokarin ganin ta kawo karshen dukkan dangantakar da ke tsakanin kasashen China da Rasha da kuma JMI. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto, Keith Kellogg ya na fadar haka a taron Munich na tsaro a jiya Asabar. Ya kuma...
    Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi...
    kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke...
    Kasashen Iran da kuma Lebanon sun tattauna kan dangantakar dake a tsakaninsu dama halin da ake ciki a yankin. A wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin yau Asabar, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Lebanon din Youssef Raji sun jaddada muhimmancin mutunta juna da hadin gwiwa. Iran da Lebanon suna da...
    Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan...
    Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama. Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin...
    Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun...
    Wasu magidanta da suka mallaki wani zakara (Ricco) jinsin Bantam daga Bourgoin-Jallieu a sashen Isère na kasar Faransa, sun karɓi sammaci domin bayyana a gaban kotu sakamakon korafin da wani makwabcinsu ya yi game da carar zakaran. Korafin da suka yi ya hada da, rashin barci saboda karar zakaran yake yi a yayin carar, kamar...
    Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar...
    Jiragen Yakin HKI Sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a kudancin kasar Lebanon, wanda hakan keta yarjeniyar tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu. Kamafanin dillancin labaran IP na kasar Iran,  ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kusa da kogin Litan, Yohmor Al-shaqif da kuma Zoutr Al-sharqiyya, da kuma Deir Siryan,...
    Gillis-Harry ya ce, “NNPC bai da wata mafita illa kawai ya rage farashin litar mai a gidajen mansa, ba zai yiwu mutane suna ganin akwai gidajen mai masu sauki kuma su je gidajen man NNPCL.” Kazalika, Ukadike ya ce, tun da ana samun bambancin farashin litar mai a tsakanin matatar mai dangote da kamfanin NNPCL,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama. A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar...
    Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.   Gwamnan a wajen bikin mika ragamar...
    Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun  yi musayar  sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye. Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece...
    Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin...
    Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar...
    Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran,...
    ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya...
    Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48. Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano...
    Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96. Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin...
    Ana fargabar mutane da dama sun rasu bayan wata tirela ta murƙushe su a Gasar Muhammadu Buhari da ke yankin Hotoro a a Jihar Kano. Tirelar ta kife ne bayan da ta kwace a ƙarƙashin gadar, a hanyarta ta zuwa Kudancin Najeriya daga Yankin Arewa maso Gabas. Wani ganau ya bayyana cewa kimanin mutane 20...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A...
    Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar.   Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a...
    Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.   Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad ​​Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau...
    Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya kasarsa suna neman murkushe al’ummar kasar  ta hanyar takunkumi da barazana. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da masana da masu fada aji na lardin Bushehr da ke kudancin kasar a ranar Alhamis , inda ya ce “Makiya suna son...
    Afirka ta Kudu ta yi alkawarin ci gaba da shari’ar kisan kiyashi da ta shigar a gaban kotun ICJ a kan Isr’ila,  duk da umurnin da Donald Trump ya bayar na katse taimakon da Amurka ke ba kasar Afirka ta Kudu saboda matakin da ta dauka kan babbar kawar Amurka. “Babu wata dama” kan janye...
    Amurka ta kakaba takunkumi kan babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da binciken da kotun ta ICC ke yi kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra’ila a Gaza da sojojin Amurka. Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakabawa Karim Khan takunkumi a matsayin martani ga umarnin shugaba...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100...
    Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka...
    Jami’an tsaro sun kama wani ma’aikacin lafiya da ake zargi da yi wa wasu ’yan bindiga da suka raunata magani a Ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina. Daga cikin majinyatan nasa har da ƙasurmin da ake nema Usman Modi Modi, wanda aka sanar da bada ladar Naira miliyan 50 don nemo shi. Tirela ta murƙushe...
    Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta. Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin. Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025 Kwastam ta lalata magungunan...
     Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya...
    Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki. Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga ranar Alhamis, 13 ga...
    Kwamandan sojan na Iran  Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya  janar Hamid Wahidi ya bayyana...
    Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...
    Rundunar sojin saman Ukraine, ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hare-hare cikin dare. Hare-haren sun fi ƙamari a yankunan Odessa da Kharkiv, a cewar sojojin. Rundunar sojin saman ta kuma ce ta samu nasarar kare wasu hare-haren daga ciki, yayin da ta tabbatar da kakkaɓo 85 daga cikin jiragen. Hakan na...
    Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.   A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka...