2025-03-21@06:30:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 857
«Alhaji Usman Yako»:
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...
Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe. “Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,”...
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...

Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma. Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance...
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da...
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da shirin Da’awah na mata a hukumance, domin karfafawa mata ilimin addinin musulunci, da karfafa alakar iyali, da kyautata rayuwa a tsakanin. Da yake jawabi a wajen bikin a Dutse, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tsara tarbiyar al’umma da kyawawan dabi’u....
Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi. Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga...
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin...
Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP,...
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross. Mutanen dai Isra’ila ta kasha su a cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su lokacin kai hare-hare a Gaza. Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan hudu...
Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya...
Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan...
Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga...
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6...
Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare....

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan...
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya. Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya...

Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin...
’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja. Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran...
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki. Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada...
’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa...
“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025. “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin...
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi,...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun sanar da gano da kuma rusa wata kungugun masu yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri a yankin Arewacin Iran. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a yankin Mazandaran dake arewacin Iran ne ya sanar da bankado da kuma rusa gungun masu yi wa abokan...
Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum. Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke...
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...

Ma’aikatar sharia ta kasar Iran Ta bada sanarwan Kama Yan Kasar Burtaniya 2 Tare Da Tuhumar Leken Asiri
Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin...
Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma...
Yawan kudin tikitin kallon fim din “Ne Zha 2” na kasar Sin da aka saya ya zarce dala biliyan 16 a daren jiya, abin da ya sa ya shiga sahun fina-finai 9 mafi samun yawan kudin tikitin kallon fim dake sahun gaba a duniya. Dalilin da ya sa fim din samun wannan ci gaba shi...