2025-04-16@15:45:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2815
«da gwamnati»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya. Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran. Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.
Sa’an nan, dangane da layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada kasar Laos da kasar ta Sin, mista Siphandone ya ce, layin dogon ya haifar da alfanu sosai, a fannin tattalin arziki, wanda ya zarce yadda aka zata a baya. Kana wannan layin dogon zai zama wani bangaren sabon layin dogon da ya hada kasar Sin da kasar Singapore, wanda za a shimfida shi a nan gaba. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, kuma suna dauke da bindigogin toka guda uku, da adduna da wukake a lokacin da aka kama su. Kakakin ’yan sanda an jihar, CSP Moses Yamu, ya ce kanawan da aka kama mafarauta ne ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa makiyaya ba ne. Ya bayyana cewa jami’an kungiyar tsaro ta Jhar Edo ne suka kama mafarautan sannan suka damka su ga...
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero. Shaida sun ce da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba. “Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma...
Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin arziki da gobarar tankar mota da ambaliyar ruwa da gobara, abin da yake biyo baya shi ne gwamnati ta raba tallafin shinkafa da sauaran kayan abinci, tamkar shinkafa ita ce maganin duk wata matsala. A wasu lokutan, a kan raba babura masu kafa uku da dabbobi a matsayin tallafi. Makudan kudaden da gwamnatoci suke kashewa da sunan bayar da tallafi, inda ba a ganin tasirin...
Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba. ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas. “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20. “Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa. “Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma. “Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse. A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza. Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin alhazan jihar na shekarar 2025. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan...
Wasu karin majiyoyi sun nuna cewa, wannan hanyar ta hada Maiduguri da wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Borno, wacce ta kasance yankin da yan ta’addan Boko Haram ke yawan kai hare-hare tsawon shekaru. A baya hanyar, ta kasance a rufe amma Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya bude ta, domin bai wa jama’a damar ci gaba da zirga-zirga a yankin da suka hada da Damboa, Chibok da sauran kananan hukumomi a kudancin Borno tare da taimakon rakiyar sojoji a matsayin kariya. An kwashe wadanda suka rasun tare da wadanda suka jikkata, wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa. Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba. Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a tsakanin bangarorin biyu. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu...

Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun. Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500. Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun...
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma da ke lardin Al-Bayda a jiya Asabar . Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin...
Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna. An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa. Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu...
Yin garkuwa da mutane domin don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Jihar Katsina har ta kai ga ana shiga cikin manyan birane ana daukar manyan mutane ko makusantansu. Daga manyan sojoji zuwa sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da attajirai da ma dalibai, babu wanda ya tsira daga wannan matsalar ta’addanci. Gwarzon gasar Al-Kur’ani A yayin da ake shirye-shiryen daukar azumin watan Ramadana ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da Gwarzon Gasar Al-Kur’ani na Kasa da aka kammala a Jihar Kebbi, Abdulsalami Rabi’u Fasakari a hanyarsa ta komawa gida tare da ’yan uwansa bayan Gawmna Dikko Radda ya karbi bakuncinsa tare da karrama shi. Sai bayan makonni biyu, a yayin da ake gab da daukar...
Wata mata mai suna Jennifer Castro ta shigar da ƙarar kamfanin jiragen sama na GOL da wata fasinja a kotu bisa wani faifan bidiyo aka wallafa da yake nuna matar ta ki barin kujerarta da ke kusa da taga saboda wani yaro da yake kuka. Matar ’yar ƙasar Brazil da ta ƙi barin kujerar kusa da taga saboda wani yaro mai kuka ta shigar da ƙara a kotu. Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Jennifer Castro, mai shekara 29 na daukar matakin shari’a a kan kamfanin jiragin sama na GOl da kuma fasinjar da ta ɗauki bidiyonta a lokacin da lamarin ya faru. Lamarin wanda aka yi ta...
Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International” ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan da har yanzu bai zo karshe ba. Wani sashe na rahoton kungiyar ya yi ishara da yadda wannan rundunar da take fada da sojojin kasar Sudan ta tarwatsa mutane daga gidaje da matsugunansu a fadin kasar. Ita kuwa Hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ( UNHCR) cewa ta yi da akwai yan kasar ta Sudan fiye da 100,000 da suke neman yin...
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani. Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti. Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza. Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu. Bugu da kari kungiyar...
Sharhin zai yi dubi ne game da tattaunawar da aka fara gudanarwa zagaye na na farko tsakanin Iran da Amurka a birnin Mascut fadar mulkin kasar Oman, inda gwamnatin kasar Oman din take shiga tsakani a wannan tattaunawa wadda aka fara gudanarwa. Tun da safiyar Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi,...
Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya. Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta...
Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu. Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74. Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) ta 1980. Dakta Olusegun Odegbami, tsohon ɗan wasan Najeriya kuma abokin Chukwu, ya tabbatar rasuwar mai ban tausayi a saƙon da ya wallafa ta manhajar sada zumunta X. “Na samu labarin cewa tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau Asabar, Christian Chukwu, MFR, wanda aka fi sani da Chairman abokina kuma abokin wasana,...
Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata. Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar. Yadda Tashar...
Wani abin takaici ya sake afkuwa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno mai cike da tashin hankali, yayin da wani bam ya tarwatse a safiyar Asabar da rana, inda aƙalla mutane takwas ne suka mutu. Wasu shaidun gani da ido na nuni da cewa fashewar bam ɗin da ake kyautata zaton mayaƙan Boko ne suka dasa shi ya tarwatsa wata motar bas ƙirar Toyota “Hummer Bus” da ke ɗauke da fasinjoji zuwa Maiduguri babban birnin Jihar Borno. An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Wata majiya mai tushe da aka zanta da ita, ta tabbatar da cewa aƙalla mutane bakwai da suka haɗa da direban motar...
Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza. Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya. A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan. An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan...
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya. Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16. ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci. Ya ce, “An sanar da shugabannin...
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba. Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna...
Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar. Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano The lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups. Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa...
An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi. Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna. A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin...
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje “Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza ayyukan ’yan bindigar da ke addabar garuruwa da ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan. Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin...
Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta. A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa. “Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo...
Ga kuma yadda ake sarrafawa: Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa. A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla. A ci gaba da juyawa har sai ya hade sosai kuma ya zama mai laushi. Idan yana da kauri sosai, sai a kara dan ruwan zafi kadan wanda dama kin rage, kuma a ci gaba da juyawa har sai ya yi laushi. A rufe shi na ‘yan mintuna kafin a sauke. Sai kuma yadda ake miyar Uwedu: Iata ma ga abubuwan da ake bukata domin hada ta: Ganyen Ewedu...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar masauki ga malamai da sauran ma’aikata da ba malamai ba. Farfesa Chamo, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ilimi, Malam Abdullahi Hudu, ya wakilta, ya ce taron ya na da nufin tattauna shirin dawowa makarantu bayan hutun da aka yi a jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya bangaren ilimi a sahun gaba saboda muhimmancinsa ga ci gaban jihar. Kwamishinan ya nuna...
Kafar watsa labaru ta ” Axio ta Amurka ta watsa wani rahoto da yake nuni da cewa, an sami rashin yarda da juna a tsakanin masu zuba hannun jari na kasa da kasa da kuma Amurka. Kafar watsa labaran ta buga a shafinta na “Internet” cewa; Rashin tabbaci da yake faruwa a halin yanzu a cikin kasuwanni yana tsoratar da masu zuba hannun jari a duniya. Rahoton ya kuma ambaci girgizar da Dalar Amurka take yi, da kuma muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka. Kafar watsa labarun ta ce, a baya muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka, wadanda kuma su ne ke bai wa Dalar Amurka kariya, sun kasance masu...
Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya. Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa...
Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar. Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib Zakiru, da ƙonewar sashin wani gida da ke daura da wajen da ’yan gwangwan ke sana’arsu. Aminiya ta ziyarci inda lamarin ya faru unguwar IdiAraba, ta kuma zanta da mammalakin wajen sana’ar ta ’yan gwangwan, Alhaji Haruna Musa, wanda kuma shi ne shugaban masu sana’ar a yankin, inda ya shaida wa Aminiya cewa, suna zaune sai suka ji wata irin ƙara mai karfi, ko da...
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki. Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya...
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su. Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur. Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.
Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin Gaza bai da wata dangantka da tsagaita bude wuta. Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ya nakalto Yerima Faisal bin Farhan yana fadar haka a jiya Jumma’a.. Ya kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya su takurawa HKI ta bada dama a shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin gaza saboda ceton mutanen yankin daga yunwa mai tsanani da suke fama da shi. Ministan yana magana ne bayan taron ministocin harkokin waje na kasashen larabawa da Musulmi a Antalya, inda suka tattauna batun yadda al-amura suke a zikin gaza da ya hanyoyin da za’a bi don tsagaita wuta da kuma...
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a, ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan unguwar Shaja’iyya inda suka kashe Falasdinawa da dama. Ya zuwa yanzu tun fara yakin tufanul Aksa, a cikin watan Octoban shekara ta 2023, falasdinawa kimani 51,000 sannan wasu 115,688 a gaza. Ta kuma rusa kimani kasha 90% na gine-ginen Gaza.
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa. Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata. “Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar...
A ranar Juma’a da daddare, wata fashewar bama-bama a wata shahararriyar kasuwa a titin Kodesoh, Ikeja dake Lagos ta janyo raunuka ga mutane da dama. Shaidu sun bayyana cewa fashewar ta faru ne lokacin da wani mai kula da shagon kyamara ya yi kokarin bude wani kunshin da aka kawo. Hukumar agajin gaggawa, tare da jami’an ‘yansanda daga tashar yankin G, EOD-CBRN Base 23 ta Ikeja, da ma’aikatan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Lagos (LASTMA), sun tura jami’ansu domin gudanar da ayyukan daukar matakai da tsaro a wurin. Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau Wani shaida gani da ido,...
Manyan Ayyukan Malamin makaranta Malaman makaranta suna da ayyuka wadanda sun fi karfin ayi su a cikin aji saboda wurin ba huruminsu ba ne,abubuwan sun hada da irin kwarewar da suke da ita,wadda za su yi amfani da ita wajen renon/ koyar da daliban da kuma yadda rayuwarsu a matsayin ‘yan makaranatrasu za ta kasance. Ayyukan Malaman makaranta sun hada da: Shirya tsarin yadda za a koyar da darussa: Shiryawa da tsara yadda za a koyar da darussa yin hakan ya kunshi ayi abu cikin tsari da lura domin tabbatar da an shirya abubuwa masu amfani wadanda zasu amfani dalibai lokacin da aka koya masu. Matsayinka na Malamin makaranta idan kana shirin shiga aji koyarwa kamata ya yi tsarin...

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji. Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu. Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka. Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum. Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar. A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su? “Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro...
108-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s). A cikin shirimmu da ya gabata...
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40. Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
107-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s). A cikin shirimmu da ya gabata...
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin sun hada da; samar da ingantaccen Irin Shinkafa da kuma habaka yadda ake samar da Irin na Shinkafar. Sauran sun hada da mayar da hankali wajen yin girbin mai kyau, samar da nau’ikan Shinkafar da ke jurewa kowacce irin cutar da ke lalata Irin Shinkafar da aka shuka, aka ajiye a cibiyar gudanar da bincike kan amfanin gona (NCRI) da ke yankin Badeggi a Jihar...
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa. Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku. Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar...
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000. Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya. Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma...
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan. Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, tana gudanar da bincike kan wani dukan kawo wuƙa da wasu matasa suka yi wa waɗansu mutane su biyu da ake zargi da satar kare a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi. Dukan da ya yi sanadin rasa ran ɗaya daga cikinsu mai suna Peter. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata kan wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato An saki fasto an kuma tsare...
Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji Kamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya. “A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan. “Yau kuma na kai ziyarar...
Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida. Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023. Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki. Duk da yawan kudin basukan da ke kan...
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace. Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan. Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin. Sai dai a baya, Danjuma Auta,...
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya. Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata. Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance...
’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi “An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba,...
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PSP a ranar 10 ga watan Maris, tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin ‘yan adawa ta samu gagarumar nasara. Atiku da sauran ‘yan adawa sun bayyana cewa taron na ranar 20 ga watan Maris ya nuna kaddamar da kawancen a hukumance. A baya dai an ruwaito a ranar 23 ga watan Maris cewa ana jinkirin tattaunawa kawance tsakanin shugabannin siyasa saboda burin...
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari. A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari. Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa. Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan. Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja Duk da kiran...
Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan. Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC. Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.” “Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.” A ranar Litinin shugaban Amurka Donald...
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin, kamar yadda wasu majiyoyi hudu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Alhamis. Wakilan tawagogin biyu sun tabbatar da kasancewarsu a babban birnin kasar Qatar, kuma sun ce za a yi ganawar ido-da-ido a ranar Laraba, amma har yanzu suna tattaunawa kan tsarin tattaunawar. Dukkanin majiyoyi – jami’an gwamnati biyu da wakilan ‘yan tawaye – sun bukaci a sakaya sunansu saboda masu...
Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30. Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu. Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba. Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba. Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da...
Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon. A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon wani muhimmin al’amari ne na kasa da ya zama wajibi a sanya shi cikin ajandar gwamnatin Lebanon. Ya kara da cewa: Al’ummar kasar Labanon suna fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile wannan ta’addanci. Fadlallah dai ya dauki babbar matsalar...
A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar. Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh. Bayan isarsu, sun tarar da shaguna da dama na ci da wuta, amma cikin gaggawa suka dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran shagunan da ke kusa. Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin...
Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka. Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu. Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku. Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa. Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin. Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa...

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
-Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar. Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar. Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa. Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin. Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki. Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda. Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi. Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin wani kaddara daga Allah Ta’ala. Shugaban karamar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya wakilce shi, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki ganin yadda ba a yi asarar rayuka ba....
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar. Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar. Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai hanyoyin arzuka iri daban daban cikin wannan Kasa, wadanda ma suka kere fetur sau ninkin ba ninki wajen bunkasar sha’anin tattalin arziki, musamnan sabgar noma, wadda wasu Shekaru can baya, ita ce kashin bayan tattalin arzikin wannan Kasa. Kuma, tun daga wancan lokaci zuwa yau din, harkar noma ce kan gaban fetur, wajen samawa dubban jama’ar Kasa aiyukan-yi. Yankin arewacin wannan Kasa ta Nijeriya, na...
An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu da kuma Muhammad Yahaya da sunan zai yi musu aiki a sako su daga gidan yari. Lauyar masu gabatar da ƙara, Barista Sadiya Sabo, ta tuhumi mutumin da laifin damfara da kuma cin amanar da aka ba shi. Wanda ake tuhuma ya amsa laifin, amma ya bayyana cewa ba shi kaɗai ya aikata wannan haramtaccen aiki ba. ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar...
Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa. Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin. Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI. A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu...
Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...