2025-04-15@23:24:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1268
«a Allah Ya ba»:
Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...
A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani. Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata. ...
Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”. Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar. Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...

Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...

Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...

Ina Dalilin Da Ya Sa Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin Ke Samun Bunkasuwa Mai Dorewa Ba Tare Da Tangarda Ba?
A kwanakin nan da suka gabata kuma, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 5, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wato Canton Fair karo na 137 a nan kasar Sin, inda yawan kamfanonin da suka halarce su suka kai matsayin koli a tarihi. Shugabar kwalejin nazarin tattalin arzikin Sin bisa salon kirkire-kirkire ta kasar Brazil madam Claudia Jannuzzi, ta ce Sin na matukar bude kofarta ga sauran sassa, tare da ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya. Cinikin shige da ficen Sin na samun bunkasuwa mai dorewa a gabanin duk wani kalubale. Ba shakka duniya za ta ga hakikanin halin da ake ciki, wato babu mafita a aiwatar da...

An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar. A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in. Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia. Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa a tsakanin bangarorin biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin ayyukan zamanantarwa, da sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi, da inganta gina al’umma mai kyakkaywar makomar bai daya tsakanin Sin da Malaysia zuwa wani sabon...
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...

Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini, inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara. Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu.. Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma...
Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci, har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...
A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza. Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi. Wadanda su ka rattaba hannu akan wasikar sun bayyana goyon bayansu ga wasikar da sojan sama su ka rubuta a ranar 9 ga watan Aprilu da ake ciki,ko da kuwa sakamakon hakan shi ne kawo karshen yaki. A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,dubban sojojin HKI sun rattaba hannu akan wasika wacce take yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma dawo da fursunonin da suke...
A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya. A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla. Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwarsu. Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16978635-dalilan-rikice-rikice-a-jihar-filato.mp3?download=true
“Abin takaici ne cewa, a maimakon yin amfani da gagarumin goyon baya da yunƙurin da ƴan ƙasa ke ginawa, Onanuga ya zaɓi fitar da wata sanarwa mai takurawa. Fahimtar da ya yi wa dokar zabe yana da tsauri fiye da kima kuma ya kasa gane bambanci tsakanin yakin neman zabe ba bisa ka’ida ba da kuma furuci na siyasa na gaske na ‘yan kasa. “Ƙungiyar gamayyar matasan Arewa ta yi watsi da wannan mataki. Goyon baya ga Shugaba Tinubu na halitta ne kuma a duk faɗin ƙasar, Ginin siyasa ba laifi ba ne. “Don haka, muna kira da a gaggauta maye gurbin Bayo Onanuga, mai bayar da shawara kan harkokin siyasa da kuma mai bayar da shawara ga...
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki. Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki...
Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40. A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato. Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon bambancin addini da kabila. Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar mai shekaru 22 daga Angwan Tana, an ce wanda ake zargin ya yi ma ta dukan jakin ne mai tsanani, Shaibu, wanda ake cewa shi ne dan uwanta. Wannan lamarin ya janyo zarge-zargen daga al’umma da kuma kiran da aka yi wa Yansanda daga mutanen gari, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama domin a kama wanda ake zargi. Ƴansanda Sun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar. Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da watanni 12 masu zuwa. Malam Umar Namadi ya kara da cewar, an bada aikin sanya kwaltar ne da kuma sauran ayyukan inganta hanyoyi domin saukakawa manoma da sauran al’umma harkokin sufuri. A don haka, ya yi kira ga al’ummar jihar da su rinka sa ido akan kayayyakin da hukuma ta samar musu domin gudun lalacewa da kuma barnatarwa. A jawabinsa na maraba,...

Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.

Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu. Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza. Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can....
Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah. Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya. ‘Yan’uwan 6 da su ka yi shahadai, suna aiki ne da wata kungiyar agaji da take rabawa ‘yan hijira kayan abinci da sauran na bukatunsu na yau da kullum. Sojojin HKI sun fitar da wata sanarwa da a ciki su ka riya cewa, wadanda su ka kai wa harin suna Shirin kai musu hari ne. A jiya Litinin da marece sojojin HKI sun rushe wasu gidaje...
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar. Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar a wannan zaben. Dan takara na biyu da yake binsa a baya, shi ne Alain Claude Bilie Bie Nze da ya sami kaso 3.02% na jumillar kuri’un da aka kada. An sami halartar kaso 70.4% na jumillar wadanda su ka cancanci kada kuri’a da ya zama mai muhimmanci da zai kawo karshen mulkin rikon kwarya na soja. Zaben na wannan lokacin shi ne irinsa...
Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne a Damaturu babban birnin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, rundunar ‘yansanda ta Karasuwa ce ta kama wadanda ake zargin – Yahaya Mustapha, 28, da Bello Yakubu, 38, da misalin karfe 1:00 na rana a ranar 12 ga watan Afrilun 2025. ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Haɗa Makamai A Kano Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata Abdulkarim ya ce, wadanda ake zargin sun fito ne daga unguwar Takari da ke karamar hukumar Gashua Bade a jihar, an kama su ne da manyan igiyoyin...
’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyen Zike, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna gujegujen neman tsira. Ya shaida wa wa kafar talabijin ta Channels cewa wata tawagar ’yan banga, da shi kansa da wasu jami’an tsaro, suna sintiri a wani ƙauye ne lokacin da maharan suka kai harin. Ko da yake jami’an tsaron sun yi artabu da maharan kuma sun yi nasarar fatattakar su, amma an riga an riga an kashe mutane talatin da shida nan take, wasu...
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an kama su ne a ranar 10 ga watan Afrilu a unguwar Dorayi Babba da ke jihar, sakamakon wani hadin gwiwa da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano suka jagoranta. Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar...
Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas. A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Sani ya bayyana cewa, an yi biris da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin. Sai dai Gwamnan ya kafa uzurin cewa, baya ga kudade, rashin tsaro da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin ne kamfanin Berger ya ki zuwa wurin domin...
Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar. Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600. Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic ...

Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba. Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin...

Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa. Haka ma tsakanin kasashen yankin. AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da...
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar. Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa. Brice zai jagoranci kasar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal dake matsayi na biyu a kan teburin gasar. Yayinda yake saura wasanni shida a kammala gasar, Liverpool na buƙatar maki 3 kacal domin lashe gasar a karo na biyu tun bayan da aka sauya wa gasar suna da fasali, West Ham na matsayi na 17 da maki 35 akan teburin gasar. Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah Salah Ya Ƙulla...
Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yakin da ake yi a Gaza A karkashin taken “An rusa Gaza” kuma goyon bayan al’umma ga Falasdinawa abu ne da ya zama wajibi, ba zabi ba, mazauna birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada bukatar musulmi a ko’ina a duniya su goyi bayan gwagwarmayar da ake yi a Zirin Gaza. Zanga-zangar dai ta samu halartar kungiyoyin ‘yan jaridu da sauran kungiyoyi da dama, wadanda suka bayyana Allah wadai da shirun da manyan kasashen duniya suka yi, tare da sukar su kan goyon bayan sojojin mamayar Isra’ila. Wani sheikhin malami dan kasar Mauritaniya ya ce: “Sun sanar da mu irin wannan gagarumin aiki, Allah Ya saka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero. Shaida sun ce da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba. “Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma...
Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga ɓangaren zantarwa na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri Hakan dai ya ci karo da yadda aka yi hasashe a lokacin da aka kaddamar da ’yan majalisar su sama da 460 domin fara aikinsu na wakilcin ’yan Nijeriya sama da miliyan 230 a...
Wasu karin majiyoyi sun nuna cewa, wannan hanyar ta hada Maiduguri da wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Borno, wacce ta kasance yankin da yan ta’addan Boko Haram ke yawan kai hare-hare tsawon shekaru. A baya hanyar, ta kasance a rufe amma Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya bude ta, domin bai wa jama’a damar ci gaba da zirga-zirga a yankin da suka hada da Damboa, Chibok da sauran kananan hukumomi a kudancin Borno tare da taimakon rakiyar sojoji a matsayin kariya. An kwashe wadanda suka rasun tare da wadanda suka jikkata, wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma da ke lardin Al-Bayda a jiya Asabar . Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin...
Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
An ɗauki waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Maiduguri, inda ake ba su kulawar. Har yanzu dai ba a tantance yawan waɗanda suka jikkata ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kowane wasa, tauraron Super Eagles Iwobi na nuna cewa ba wai kawai tarihi yake son kafawa a Duniya ba, ya na sake rubuta labarin ‘yan wasan kwallon kafar Nijeriya a Turai, shan kayen da Liverpool ta yi a Craben Cottage ya jinkirta damarta na lashe gasar Firimiya Lig ta bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba. Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna...
Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
Ga kuma yadda ake sarrafawa: Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa. A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla. A ci gaba da juyawa har sai ya hade sosai kuma ya zama mai laushi. Idan yana da kauri sosai, sai a kara dan ruwan zafi kadan wanda dama kin rage, kuma a ci gaba da juyawa har sai ya yi laushi. A rufe shi na ‘yan mintuna kafin a sauke. Sai kuma yadda ake miyar Uwedu: Iata ma ga abubuwan da ake bukata domin hada ta: Ganyen Ewedu...
Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya. Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa...
Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar. Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib Zakiru, da ƙonewar sashin wani gida da ke daura da wajen da ’yan gwangwan ke sana’arsu. Aminiya ta ziyarci inda lamarin ya faru unguwar IdiAraba, ta kuma zanta da mammalakin wajen sana’ar ta ’yan gwangwan, Alhaji Haruna Musa, wanda kuma shi ne shugaban masu sana’ar a yankin, inda ya shaida wa Aminiya cewa, suna zaune sai suka ji wata irin ƙara mai karfi, ko da...
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki. Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya...
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a, ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan unguwar Shaja’iyya inda suka kashe Falasdinawa da dama. Ya zuwa yanzu tun fara yakin tufanul Aksa, a cikin watan Octoban shekara ta 2023, falasdinawa kimani 51,000 sannan wasu 115,688 a gaza. Ta kuma rusa kimani kasha 90% na gine-ginen Gaza.
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...

Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko su hana gaba daya. Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke...
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi “An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe. Kazalika, a cikin kowanne wata daya, mai ajiyar zai iya zamaowa a cikin rukunin Zakaru 70, inda kowanne mai ajiya daya a Bankin, zai iya karbar Naira 100,000. Har ila yau, a cikin watanni uku kuma, kowanne mai ajiya daya a Bankin na Stanbic IBTC, da ya fito daga yanki bakwai da ake yin kasuwanci, zai lashe Naira miliyan daya, inda kuma a zagayen gasar na karashe...
’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa. Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan. Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja Duk da kiran...

Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu. Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi. Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar...
Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban. Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba. Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade...
Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta. An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba. Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar. Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar. Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa. Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin. Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki. Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda. Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi. Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin wani kaddara daga Allah Ta’ala. Shugaban karamar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya wakilce shi, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki ganin yadda ba a yi asarar rayuka ba....

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa. Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin. Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI. A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu...
Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...
Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza. Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar ta Shuja’iyya.Dama tun da safiyar Laraba wasu Falasdinawan 50 sun yi shahada a wannan unguwa ta Shuja’iyya dake cikin birnin Gaza. Wasu majiyoyin Falasdinawa sun ambaci cewa: Sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi a kusa da masallacin; UMMU HaBIBAH, da kuma kasuwar sayar da kekune a yankin Qaizan a kudancin Khan-Yunus. A gefe daya,majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa; Da akwai Falasdinawa miliyan...
Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai...
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa. Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar. Ya koka da...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a dai dai lokacinda gwamnatin Amurka ta dorawa kayakin kasar China masu shigowa Amurka kudin fito na kasha 125%. Tun zagaye na farko na shugabancinsa ne shugaban ya fara rigima da kamfanin Tiktok na kasar China wanda ya sami karbuwa a cikin Amurka da kuma kasashen duniya da dama. Amurka tana ganin shafin yanar gizo na tiktok barzane ce ga tsaron kasar Amurka. Kuma har ta...
Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI. Amma sojojin sun kammala da cewa a...
Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi. Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin daliban firamare ba su iya karatu ko rubutu yadda ya kamata. Ya bayyana cewa, an dauki malamai sama da 7,000 a karkashin gwamnatinsa domin karfafa ilimin boko, ya kuma ce jihar ta bullo da sabbin dabaru da suka shafi al’umma, kamar taron iyaye mata da kuma farfado da kwamitocin gudanarwa na makarantu (SBMC), domin inganta zuwan yara makarantu da kuma lura da yadda malamai...
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet Ya ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne. Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa. “Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban...