2025-03-29@03:51:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 973

«a Allah Ya ba»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar. Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa Hassan a jawabinta ga kasar a karshen ziyararta a yankin Tanga. Tana mai cewa, babban kamfanin gine-gine mallakin kasar Sin wato China Harbor Engineering Compnay, shi ne ya yi aikin inganta tashar ta Tanga. Ta kara da cewa, inganta tashar da aka yi ya kuma samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da shirye-shiryen mayar da tashar ta zama cibiyar jigilar takin zamani da...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye girmama kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik a fannoni 4. Firaminista Brown ya yi nuni da cewa, kasarsa ta tsibiran Cook ta dora muhimmanci ga girmamawar da Sin ta nuna mata, kasar Sin ta kiyaye yin hakan tun da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu....
    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring rolls’ Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno Haka kuma an ce, jihohin da ba sa noma suna jin tasirin rage farashin kayan abinci. Masana sun danganta faduwar farashin da aka samu a kasuwa ga karancin kudi da kuma yadda aka yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, wanda hakan ya haifar da faduwa farashin sosai. Wasu kuma sun ce, yawan shigo da...
    Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. Kamar yadda a kullum nake ba da shawarar cewa, yana da kyau uwargida ta ƙware wajen girke-girke, wato yana da matukar muhimmanci ta ƙware wajen girkin gargajiya da na zamani da kuma na ƙasashen waje. Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake ‘spring roll’. Bayan abincin buɗe baki, uwargida za ta iya koyan wannan girki a matsayin sana’a da za ta iya kawo mata kuɗi. Abubuwan da ake bukata: · Karas · Albasa · Attaruhu · Tafarnuwa · Kabeji · Kayan dandano...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan. “Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar. “Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.” Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar...
    A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar. Dokar dai zata shafi ayyukan mutanen, don wasu zasu rasa ayyukansu. Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport. Sai kuma kungiyar...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru. Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu. Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya...
    Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji shi. Tun da farko dai, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mahukuntan jami’ar suka rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan abokin aikinsu. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a Katsina a safiyar ranar Litinin cewa, “wasu jami’an CJTF sun bindige dalibai biyu ne bisa kuskure, suna tunanin...
    Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Lokacin harin, mutum biyu sun jikkata, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa sakamakon harbin da wani daga cikin mutanensa ya yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace...
    Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan  Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
    Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya: 1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya: A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100. 2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce: Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400...
    Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027. Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar. Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya gina a matsayin wakafi ga mahaifinsa. Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa bisa wannan  kokari na Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya. Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan matakin domin amfanin talakawa da marasa galihu a cikin al’umma. Ya  jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da irin wadannan mutane...
    Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%. Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna...
    Bankin na CBN ya sanar da cewa, daukacin Bankunan, ana sa ran su bi wannan umarnin nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI. Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a garuruwan Aitarun da kuma Aita shaab. Inda mutanen da dam dagayankin zuka halarta . Labarin ya kara da cewa Shahidan sun kai ga shahada ne a hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kudancin kasar ta Lebanon a cikin watannin Octoba da kuma Nuwamba na shekara ta 2024. Labarin ya kara da cewa a yakin dai mutanen leabin kimani...
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sergei Shoigu, sakataren majalisar tsaro ta kasar Rasha, a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, Sin da Rasha sun kasance masu tuntubar juna a dukkan matakai, da aiwatar da matsayar da suka cimma da shugaba Putin da hadin gwiwa mai muhimmanci da moriyar juna tare da zurfafa hadin gwiwarsu a kai a kai, domin taimakawa muradunsu na bai daya na samun ci gaba da farfado da kasashen biyu. Ya kara da cewa, ya kamata kasashen 2 su karfafa hadin kai a harkokin da suka shafi yanki da ma duniya, su kuma goyi bayan rawar da kasashen BRICS da kungiyar hadin kai ta Shanghai suke takawa, tare da...
    Wannan mataki yana da matuƙar tasiri a siyasar Jihar Ribas, inda jam’iyyar APP ce ta lashe mafi yawan kujeru a zaɓen da aka soke. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamar yadda ba a lokaci guda a ke gina dabi’u ba, haka nan ba zai yiwu a rusa su a lokaci guda ba. mutum na gina dabi’a ne ta hanyar yin mu’amala da mutane. Gina dabi’un na farawa daga shekarun yarinta, saboda a sannan ne a ke koyon al’adu, tarbiyya da girmama manya. Har zuwa mutuwan mutum ya na mu’amala ne da mutane ya na gina sabbin dabi’u. Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da...
    Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya yi wani kakkausan gargadi game da rahotannin rashin biyan albashi da rashin biyan ma’aikatan jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkin ma’aikata da kuma cin amanar jama’a.   Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bincike mai mutane bakwai, karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, domin gano musabbabin sabanin.   Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruk ya wakilta, ya ce kwamitin ya hada da manyan jami’an gwamnati da masana harkokin kudi da wadanda suka kware a tsarin biyan albashi.   Yace Membobin Kwamitin sune Abdulkadir Abdussalam_ – Shugaban, Kwamishinan Karkara da Ci gaban Al’umma Dr. Bashir Abdu Muzakkari – memba, mai ba da shawara na musamman kan...
    A 2024, rundunar ‘yansanda ta Abuja, sun kama wani mai suna Nuhu Ezra, a yanikin Lugbe dauke da Kokon kan mutum da Kasuwansa, inda wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa, ya ci karo da Kokon kan mutum da Kasuwan ne, a yayin da yake yin farauta a cikin Dajin Kuje. Kazalika, duk dai a 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar Ondo, sun cafke wani mai suna Yusuf Adenoyin, a yankin Isua, na karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas dauke da Kokon kan bil Adama guda takwas. A Jihar Oyo ma, rundunar ‘yansanda ta jihar ta kama wasu mutane biyu a yankin Amuloko da ke garin Ibadan, bisa zargin samun dauke da danyen Kokon kan wata mata , da ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al’ummar Musulmi na yin azumi ne bisa dalilan addini kamar yadda Allah Ya yi umarni don samun lada. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka haɗa da inganta ƙarfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki ba ya bukata. A taƙaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwarsa. NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa...
    An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.   Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.   Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.   Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.   Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira...
    A ranar 27 ga wata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya a birnin Beijing. Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, masana’antar mutum-mutumin inji ta zama wata muhimmiyar alama ta auna matsayin wata kasa ta fuskar kimiyya da fasahar kere-kere da kuma masana’antar kere-kere na babban mataki. Kasar Sin ta zama kasa mafi grima a duniya wajen kera mutum-mutumin inji da yin amfani da su. Ta hanyar dogaro da babban dandalin watsa labaru mai karfi, gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya ta CMG za ta nuna nasarorin da aka samu wajen kera mutum-mutumin inji ta kowane bangare, ta yadda za a hada karfin...
    Taron lakca karo na 22 na kasar Sin da aka yi jiya Laraba a birnin Alkahiran Masar, ya hada malamai Sinawa da na kasar da jami’ai sama da 200, inda suka tattauna don gane da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika, wajen daukaka zamanantar da kasashe masu tasowa. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika da cibiyar Confucius ta jami’ar Suez Canal ta Masar ne suka karbi bakuncin taron mai taken “Zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika domin jagorantar zamanantar da kasashe masu tasowa.” Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa dangantakar Sin da Masar, da fadada musaya tsakanin masana, da bunkasa tallafin ilimi ga kokarin kasashe masu tasowa na zamanantar da kansu. Tattaunawar ta kuma jaddada batun kara inganta...
    Kazalika sun yi ƙorafi tare da nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati da majalisar gudanarwar Jami’ar ke tafiyar da al’amuran da suka shafi ci gabanta.   Ƙungiyar malaman ta ce ta kafa wani kwamiti da zai tilasta tare da tabbatar da an bi umarnin yajin aikin da tsayawar harkoki a Jami’ar har sai an cimma matsaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa  gabashin Afirka zai zama  sama da sauran  yankunan nahiyar a cigaba. Ana hasashen cewa  a cikin  rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga ( GDP)  daga 4.4% da ya kasance a 2024, ya koma 6.1% a cikin 2026. Sai kuma a cikin kasashen  Rwanda, Uganda, Sudan Ta kudu, Habasha, Tanzania da Kenya mafi karancin karuwarsa zai zama  kaso 5.% a 2025. A cikin yankin yammacin Afirka kuwa, an tsinkayo cewa tattalin arzikinsu zai tashi daga 4.1% a 2024,zuwa 4.6% a 2025, kuma kasashe irin su Togo, Benin, Cote De...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Isra’ila da ta gaggauta dakatar da siyasar amfani da karfi na yi wa Falasdinawa karfa-karfa a yammacin kogin Jordan. Hakan nan kuma ta yi kira ga HKI da ta daina ayyukan da za su iya zama azabtar da al’umma kaco kau. Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma bayyana cewa, irin wannan siyasar da Isra’ilan take amfani da ita, ta tilasata wa Falasdinawa 40,000 yin hijira daga yammacin kogin Jordan. Hukumar ta “Amnesty” ta sanar a yau Alhamis cewa; Falasdinawa mazauna “Budhum” a Musafir suna fuskantar hatsarin korarsu a kurkusa saboda yadda ‘yan share wuri zauna suke kai musu hare-hare a karkashin kariyar hukumar ‘yan sahayoniya....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Moroko, Mohammed na shida, ya buƙaci ƴan ƙasar su kaurace wa layya a bana wanda al’ummar Musulmi masu hali ke yanka dabobbi, musamman rago a matsayin nuna godiya ga Allah bisa rayawa da ni’imomin da ya yi wa bayinsa.Sarkin ya ce sanarwar tasa na da alaƙa da karancin raguna da ake fuskanta a ƙasar sakamakon fari. A watan Yunin bana ake sa ran gudanar da bikin sallar Layya. Layya ibada ce da al’ummar musulmi ke yi a cikin watan Zhul Hajji. A bikin Sallar layyar ana yanka dabobbi da suka danganci raguna da awaki ta hanyar zubar da jini a kuma raba naman a matsayn kyauta da sadaka don neman kusanci ga ubanjigi. Sai dai Sarki Mohammed na moroko...
    Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF.   Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta.   A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, hafsan hafsoshin ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin shiyya da dabarun hadin gwiwa wajen karfafa karfin jiragen na Afrika da kuma magance barazanar da ake fuskanta.   Ya jaddada cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin sojojin saman Afrika na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke...
    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta sake jaddada aniyar ta na dakile yaduwar magungunan jabun a fadin kasar nan.   Darakta Janar na Hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana hakan a yayin bikin bude taron wayar da kan jama’a na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano.   Farfesa Mojisola Christianah wacce Darakta Pharmacist, Pharmacist Bitrus Fraden ta wakilta ta ce NAFDAC ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare guda uku da nufin inganta hanyoyin magance yaduwar magungunan jabu a kasar.   Babban Daraktan ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa wa wadannan tsare-tsare, da nufin tabbatar da samar da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, masu inganci ga ‘yan Nijeriya.   Ta ce Najeriya...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ya hori Kiristoci masu niyyar ziyarar su zama jakadu na gari tare dayin addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba idan sun isa can.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bankwana da masu ziyarar su 162 da zasu tashi zuwa Isra’ila.   Gwamnan ya jaddada muhimmancin da’a a yayin tafiyar tasu, inda ya bayyana cewa su dauka su Allah ya nufa da wannan ziyarar a bana.   Ya kuma tabbatar wa maziyartan jihar cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwarsu, tare da samar da matsuguni da abinci kyauta a tsawon tafiyarsu.   Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin hukumar kula da masu ziyarar kiristoci ta jihar Nasarawa, Davide Ayiwa, wanda ya yabawa...
    Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa shugaban makarantar ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg. Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi. Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta. Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” ​​an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su. A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 27, kuma za su samu horo da jagoranci kan ayyukan da hukumar ta dora musu. Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta gudanar ta taron bita ga dukkan jami’an shiyyar da nufin sanar da jami’an irin ci gaban da aka samu a shirye-shiryen gudanar da aikin hajji mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana jin dadinsa kan yadda...
    Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890. Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen. Wadanda sojojin HKI suka kashe ko suka kaisu ga shahada a shekarar da ta gabata. Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da...
    Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping. Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin  gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar. Ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci  hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati. Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse. Ya jaddada cewa, gaskiya, da  rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari. Barista Salisu Abdu, ya...
    Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a ranar Litinin ya halarci bikin kaddamar da gina yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari, inda ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na bunkasa masana’antu a kudancin Afirka. Kamfanin Xintai Resources na kasar Sin ne ya zuba jarin dala biliyan 3.6 a yankin masana’antu musamman na makamashi da karafa na kogin Palm da ke Beitbridge na lardin Matabeleland ta kudu, kuma za a aiwatar aikin a matakai biyar cikin shekaru 12, da nufin samar da kayayyakin da ake amfani da su na chromium da coke. Mnangagwa ya ce, “Ina fatan aikin wannan yankin masana’antu na musamman, zai taka rawa a matsayin wani muhimmin tubali ga ci gaban masana’antu da zamanantar da...
    An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri.   Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.   Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa. Bugu da kari bangaroin biyu sun tattauna akan alakar kasashen biyu da hanyoyin bunkasa ta.
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce;  Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta. Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran  ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da...
    ’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta. Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?...
    Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin. Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole. Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan Adam, musamman mai azumi. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ranar 21 ga watan Fabrairu ne aka cika shekaru 53 da shugaban kasar Amurka na lokacin Richard Nixon ya kawo ziyara kasar Sin a shekara ta 1972, ziyarar ta sauya tarihin duniya, ta kuma samar da tushen ci gaban yankin Asiya da tekun Pasifik cikin lumana. Lokacin da tunanin yakin cacar baka ya yi kamari a Amurka, Nixon ya fahimci muhimmancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a ci gaban Asiya da duniya baki daya. Nixon, ya kasance dan siyasa mai ra’ayin mazan jiya wanda ya girma cikin yakin cacar baka, amma duk da haka ya keta shingayen mulkin mallaka, danniya da babakere na wancan lokaci don fahimta da sauke alhakin da ke kansa na tarihi, ta hanyar hadin gwiwa da tuntuba,...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun  jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki. Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane  1,200 da suka ci gajiyar tallafin. A jawabinsa, dan majalisa...
    Shugaba Xi ya kuma yi nuni da cewa, a watan Satumban bara, Sin da Brazil, tare da wasu kasashe masu tasowa, sun kafa kungiyar abokan zaman lafiya game da rikicin kasar Ukraine, don samar da sarari da kuma ingantattun sharudda domin karfafa warware rikicin a siyasance. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar kula da muhallin halittu ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 24 ga wata, inda wani jami’inta ya nuna cewa, ingancin iska da muhallin kasar sun kyautatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta cimma burin magance gurbatar yanayi a shekara ta 2024. Jami’in ya kara da cewa, a shekara ta 2024, yawan kwanakin da aka samu kyakkyawan ingancin iska ya kai kaso 87.2%, adadin da ya karu da kaso 1.7% idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Kazalika, yawan kwanakin da aka samu mummunar gurbatar yanayi ko fiye da haka, ya kai kaso 0.9%, adadin da ya ragu da kaso 0.7%. A Beijing, wato fadar mulkin...
    Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin saman yaki samfurin Yak-130 a cikin atisayen. Inda suka tabbatar da ingancinsa. Ana gudanar da atisayen Zulfikar 1403 ne a yankin Tekun Omman da kuma wani bangare na yankin Tekun farasa daga kudancin kasar Iran. Bugediya Janar Alireza Sheikh kakakin atisayen ya fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa wannan bangare kadan ne daga atisayen, amma a yau sun...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
    Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
    Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya). Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar. Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar  Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da...
    Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo. Basaraken  ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta. Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba. “Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan...
    Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta. Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa. “Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar...
    Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi. John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin. Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya. Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke. Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi. A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma ba tare da wata matsala ba lokacin Chunyu da aka kammala jiya Asabar, alkaluman bana sun nuna an samu karuwar kashi 7.1 cikin dari a kan adadin da aka samu na daidai irin wannan lokacin a shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
    Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin ya yi Allah wadai da kasar Australia bisa yadda ta zargi kasar Sin da yin atisayen soja bisa doka a tekun dake kusa da kasar ta Australia. Kakakin, Wu Qian ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin kafofin watsa labaru game da zargin na Australia cewa jiragen ruwan yaki uku na kasar Sin sun yi atisayen soja a tekun dake kusa da kasar Australia. Wu Qian ya bayyana cewa, zargin da kasar Australia ta yi ba shi da tushe balle makama, domin yankin tekun da jiragen ruwan yakin na kasar Sin suka yi atisayen soja yana can nesa da layin teku na kasar Australia, kuma yanki ne da ba ya cikin mallakar wata kasa....
    A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
    Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Cigaba Da Zama Shugaban APC A Kano, Zan Fita – Ata
    Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025. Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta...
    ’Yan bindiga sun kai hari wata coci da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta, inda suka yi awon gaba da masu ibada a daren ranar Juma’a. Sun harbi fasto sannan suka sace masu i ada shida a cocin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na dare kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta. Maharan sun harbi fasto, Apostle Divine Omodia, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti. Mutanen yankin suna cikin fargaba kan rashin tsaro a wuraren ibada, inda suke roƙon gwamnati ta ceto mutanen da aka sace...
    Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
    “Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.”   Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa.   Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba.   “Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.”   Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya jaddada kudirinsa na karfafawa matasa sana’o’i da ayyukan yi a jihar. Ya bayyana haka ne a yayin bikin bude wani katafaren shago da wani bawan Allah ya gina a kan titin Malam-Madori a karamar hukumar Hadejia. Ya bayyana cewa, bai wa matasa damar yin sana’o’i shi ne jigon tsare-tsaren gwamnati mai dauke da manufofi 12,  da ke da nufin daukaka jihar zuwa matsayi mafi girma. A cewarsa, daya daga cikin ginshikan tsare-tsaren gwamnatinsa shi ne samar da damammaki da ke bai wa matasa sana’o’in dogaro da kai, domin samun ci gaba a kasuwar hada-hadar kudi. Gwamna Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta kaddamar da kafa shaguna da za a rika sayar da kayayyaki...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira da a gaggauta bibiyar bayanan manyan laifuka na shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Holland, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaya da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Falasdinu, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa wajen hanzarta bibiyar bayanan shari’a da laifuka a kotunan duniya dangane da kisan kiyashi da laifukan yaki da shugabannin mamayar Isra’ila suka aikata. Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen kasar Holand Caspar Veldkamp da takwaransa na Iran Abbas Araqchi sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen...
    ‘Yan daban sabuwar gwamnatin Siriya sun kai samame wani Masallaci da ke cikin karkarar birnin Damascus tare da korar masu ibada Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar da ke da alaka da gwamnatin rikon kwarya a kasar Siriya sun kai farmaki kan Masallata da ‘yan kasar ke gudanar da ibadu a cikin masallacin Al-Mustafa da ke unguwar Andalusia a garin Babila a cikin karkarar birnin Damascus, bayan da suka ki mika musu makullan masallacin da kuma rufe Masallacin saboda sabanin Mazhaba. Hakazalika ‘yan daban Al-Jolani sun lalata ofisoshi da hotuna da ke cikin masallacin, lamarin da ya fusata mazauna birnin. Masu lura da al’amura sun bayyana cewa: An gina masallacin ne da...
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza. Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman,...
    Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki. Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai...
    Rayuwar Nura Muhammad dan shekara 13 a duniya ta gamu da cikas bayan da ya tsere tsallake rijiya da baya a lokacin da gungun wasu ’yan ta’adda suka kai hari a kauyensu da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka raba shi da iyaye kuma babu matsuguni. Don haka ba shi da wani zabi, dole ya koma garin Sakkwato, domin fara sabuwar rayuwa. Ko da aka tambaye shi inda iyayen nasa suka, sai ya kada baki ya ce, “Ban san inda iyayena suke ba,” ko sun rayu a lokacin da aka kai wa kauyen hari a farkon shekara ta 2023. PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna...
    “Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar. Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda. Danlami Stingos ya kuma yabi gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da take yi na yaƙi da yan ta’adda sannan ya kuma riko gwamnatin da ta dage wajen samar da hanyoyi a yankunan da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
    Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
    Jagoran kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka a bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, ya zanta da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ta kafar bidiyo jiya Jumma’a 21 ga wata, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasashen biyu, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma. Bangarorin biyu duk sun amince da muhimmancin alakokin tattalin arziki da kasuwanci a tsakaninsu, inda suka yarda su ci gaba da tuntubar juna kan batutuwan da suka fi daukar hankulansu. Har wa yau, kasar Sin ta nuna matukar damuwa kan matakin da Amurka ta dauka kwanan nan, na kara sanya wa hajojin kasar Sin...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin HKI sun kutsa cikin sansanonin yan gudun hijira na Palasdinawa a Tulkaram da kuma Jenin tana rusa gidajen falasdinawa tana kuma kora da kuma kashe wadanda suka samu a cikin gidajen nasu. A wani labarin kuma kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi allawadai da rushe-rushen gidajen da gwamnatin HKI take yi a yankin yamma da kogin Jordan.  Kungiyar ta yi kira da kasashen duniya...
    A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
    A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na  tattalin arziki a duniya sannan suna...
    Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Dakatar Da Duk Wani Tashin Hankali A Gabashin Kongo
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
    Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
    Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan a jiya Juma’a. Yanzu kusan wata guda ke nan da Netanyahu ya ba da umarnin tsananta hare-haren kan sansanin ‘yan gudun hijiran na Tulkram, kamar yadda ofishinsa ya bayyana, kwana guda bayan tashin bama-bamai kan motocin bus-bus a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila. Ofishin fira ministan ya bayyana cewa: Kwanan nan...
    Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu. A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka...
    Kafin ya zama sanata, ya yi majalisar dokokin ta tarayya da ya wakilci mabazar Toro daga 2011 zuwa 2018. An shirya masa jana’iza da ƙarfe 1pm a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairum 2025 a Masallacin da ke kofar gidansa da ke Gwarimpa, Abuja. Cikakken labarin daga baya:
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...