2025-03-29@03:45:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 973
«a Allah Ya ba»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahukuntan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun sanar da shirin fara yiwa ’yan mata dake makarantun karamar sakandare allurar rigakafin cutar HPV, mai haifar da karin bakin mahaifa kyauta, tun daga watan Satumban bana, a wani mataki na dakile karuwar mata dake kamuwa da cutar. A cewar sanarwar hadin gwiwa ta cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta birnin da sauran hukumomi masu alaka da aikin, wadda aka fitar a jiya Alhamis, ya zuwa karshen watan nan na Maris, ’yan mata da a yanzu haka ke ajin karshe na makarantun firamare, za su cike takardun amincewa da karbar rigakafin, kana ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, za a kammala yi musu kashin farko na rigakafin. An shirya gudanar...
A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci. Ya shigar da Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar NSCDC, da sauran hukumomin tsaro ƙara. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatar Dan Agundi, inda ta ce akwai hurumin shari’a a cikin ƙarar. Mai shari’a Abang ya bayyana cewa kotu dole ne ta yi adalci wajen yanke hukunci. Wannan hukunci yana nufin cewa dole ne dukkan ɓangarorin su ci gaba da zama yadda suke kafin Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci. Bugu da ƙari, kotu ta umarci Dan...
Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+. Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu. Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.30, wannan ya kai daidai na alkaluman watan Satumba, wanda ya haura tun a 2018. Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk...
An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa. Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum. Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa. Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan. Su kuwa...
A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa. Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin al-sha’arah’ dake gabashin Jenta a Biqa. Da marecen jiya Alhamis din dai jiragen yakin HKI sun yi shawagi a kasa-kasa yankin Biqa, kamar kuma yadda sojojin nasu su ka jefa bama-bamai masu haske a yankunan Kafar-Shuba, dake kudancin Lebanon. Irin wadannan keta tsagaita wutar da sojojin HKI suke yi, yana sanya alamar tambaya akan aikin da kwamitin dake kula da tsagaita wutar yakin yake yi....

Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa. Kasashen na China, Rasha da kuma Iran sun bayyana takunkuman na Amurka akan Iran da cewa, ba halartattu ba ne. Haka nan kuma sun ce; Tuntubar juna da kuma tattaunawar diplomasiyya bisa girmama juna ne kadai zabin da ake da shi domin cimma manufa. Taron da aka yi a yammacin birnin Beijing ya kunshi mataimakan ministan harkokin wajen Iran Garid Ridh Abadi, Sai Rasha Sergey Ryabkov da...
‘Yan mata 74,452 ne suka ci gajiyar tallafin kudi a karkashin shirin samar da ilimi da karfafawa ‘yan mata matasa AGILE a fadin kananan hukumomi 19 da ke Kano, wanda ya kunshi rukuni daya da na biyu. AGILE wani shiri ne na taimakon Bankin Duniya na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya wanda aka tsara don inganta damar samun ilimin sakandare ga ‘yan mata masu tasowa tsakanin 10 zuwa 20. Aikin yana samar da cikakkiyar hanya don inganta daidaiton samun ingantaccen ilimi ga ‘yan mata masu tasowa ta hanyar inganta kayan aikin makaranta, samar da kudade na sharaɗi ga gidaje masu karamin karfi, magance ƙa’idodin zamantakewa waɗanda ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, da kuma ƙarfafa ‘yan mata, da...
Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki. Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau. A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi. Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan. “A wannan karon,...
’Yan bindiga sun kai hari tare da tarwatsa mazauna ƙauyuka biyar da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sonudazuwa, Tsauni Dodo, da Dandauka. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Wani jagoran al’umma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki sansanin Fulani da ke Kubuwo, inda suka sace matasan makiyaya uku. Sun kai harin ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 6 na yamma. Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar sun isa ƙauyukan suna harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa....
Takawa ta kebantattun kebantattu: sun hada duk abin alkairi na gama-garin mutane, sun hada duk abin alkairi na kebantattu sannan sun kara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah, ba su ganin wanin Allah, a ko da yaushe suna Fadar Allah ko suna Fadar Annabi (SAW) ko suna fadar Waliyyan Allah. Wadannan Takawa guda Uku, Allah ya fada mana su cikin Alkur’ani yana cewa : “Ba laifi ga wadanda suka yi imani da Allah suka yi aiki mai kyau cikin abin da suka ci, idan suka yi takawa suka yi Imani, sannan suka yi wata takawa kuma suka yi Imani sannan suka yi wata takawa sannan suka yi kyautaye.” Ayar ta sauka ce lokacin da ayar haramta giya ta sauka,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare. Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Motocin dai, an bai rundunar soji Uku, yayin da rundunar ‘yansanda ta Mopol ta karbi daya. Kwamandan Barikin Soji na Birnin Kebbi, Manjo A. P. Azubuine, ya bayyana godiyarsa na goyon baya da gwamnatin ke basu wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar. Shi ma a nasa bangaren, ACP Aliyu Jega, kwamanda Mopol 36 da ke Birnin Kebbi, ya mika godiyarsa ga gwamnan, inda ya kara da cewa, Motar za ta taimaka musu wurin sauke nauyin da ya rataya akansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki a unguwar Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutane shida. Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Waɗanda aka sace su ne: God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip. Hakazalika, a ƙauyen Makyali, wasu mutane biyu sun samu raunuka na...
Ministan man fetur da ma’adanai na gwamnatin tarayyar kasar Somaliya Taha Shari Muhammad ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu aikin da kamfanin kasar Turkiya yake yi na hako man fetur a kasar ya yi nisa, kuma da akwai yiyuwar nan da shekara ta 2026 kasar za ta fara fitar da man Fetur. Taha Shari ya kuma kara da cewa; Ana gudanar da aikin hako man ne a yankunan “Marig” dake gundumar “Galgadun” da kuma yankin “Harar Tiri” dake gundumar Madga. Ministan man fetur da kuma ma’adanan na kasar Somaliya ya ce; Idan an gama aiki a wadannan yankunan biyu, za’a nufi garin “ Hobiyo”, don ci gaba da hako wasu rijiyoyin man. Bugu da kari ministan man fetur na...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwan amincewa da tsagaita budewa juna wuta tsakanin Rasha da Ukraine na tsawon kwanaki 30, wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar, sai dai akwai bukatar karin bayani filla-filla kan yadda hakan zai kasance. Sannan yana fadar wannan zai kai ga tsagaita budewa juna wata na din din din. Shafin yanar Gizo na labarai Africa News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar a kara tattaunawa da abokammu na kasar Amurka don kara fayyace yadda tsagaita wutan zai kasance. Daga cikin abubuwan da za’a tattauna akwai yiyuwar sabawa yarjeniyar da kuma matakan da za’a dauka don hana hakan faruwa ko kuma idan ya...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau , shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su gwagwadon lokacinda muke da shi da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… masu sauraro shirimmu nay au zai yi magana dangane da ‘Maida Martanin Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ga zabin zabi biyun da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bawa kasar dangane da shirinta na makamashin Nukliya na kasar, tattaunawa ko yaki’. Jagoran...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri. Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Taron ya ƙara hura...
Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da rukuni na farko na jami’an tsaro karkashin shirin Safe Schools Initiative na Jihar Jigawa. Taron, wanda kuma ya kasance bikin kammala horo ga masu tsaron, an gudanar da shi ne a sansanin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Panisau, a Dutse. Wannan shiri, wanda shi ne irin sa na farko a ƙasar, an kirkireshi ne domin kare makarantu, da asibitoci, da kotuna, da wuraren samar da ruwa a fadin jihar, inda aka dauki ma’aikata 9,974 don aiwatar da wannan aiki. Za a tura Jami’an tsaron ne karkashin kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da aka rarraba zuwa mazabun yan majalisun dattawa. Kamfanonin tsaron sun hada...
Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule. Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar. Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su, domin tabbatar da sahihanci da ingancin aikin jarida. Da yake ƙarin bayani, ya ce gwamnatin Abdullahi Sule ta kawo sauye-sauye masu amfani, musamman wajen inganta harkar haƙar ma’adinai a jihar. Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ce ke kan gaba a Naieriya wajen samar da ma’adinan Lithium, wanda ke amfani ga ci gaban tattalin arziƙi. A nasa jawabin, Shugaban ‘Yan Jarida na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju,...
Ya ƙara da cewa, ECOWAS na da aniyar tunkarar matsalolin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da wadata ga al’ummomin ƙasashen yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu. Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar. Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su. “Malam Rabe da ’ya’yansa biyar,...
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon shinkafa da sauran kayayyaki ga gidaje sama da 30,000 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar. Da yake kaddamar da rabon a Sokoto, Sanata Tambuwal ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake ganin watan Azumin Ramadan tare da tabbatar da ganin an gudanar da Ramadan cikin kwanciyar hankali. Ya jaddada mahimmancin tunani, karamci da addu’o’in ci gaba da lafiya da wadata. Tambuwal wanda shi ne Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu a jam’iyyar PDP ya ce wannan shiri na kara jaddada kudurin jam’iyyar na hadin kai, tausayi da goyon bayan al’umma a cikin wannan wata mai alfarma. Ya yaba da jajircewar...
Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma. Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi. Guguwar ruwan sama ta yi barna a kwalejin Ansar Deen da ke Ijagbo yayin da ajujuwa sama da 10 suka yi lalace, inda dalibai da malamai suka makale. An gano cewa guguwar ta afku ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Litinin, tare da yaga rufin ajujuwan tare da lalata muhimman kayan koyo da kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi. Da suke Magana game da wannan...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, a wani artabu da suka yi da shi a dajin Gidan-Abe da ke kan iyakar Bwari da Kaduna. Sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan shigowar ‘yan bindiga yankin daga Kaduna. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin Mustapha Muhammed, sun tare hanyar ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta da su. “Mun yi nasarar...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar. A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a ziyarar aiki a ƙasar Sin daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Fabrairun 2025, domin yin haɗin gwiwa a muhimman sassa. Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd,...
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa. Gwamnan, ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kangiwa da Lakurawa suka kai musu hari tare da raba su da muhallansu a kauyukan Birnin Debe, Dan Marke da Tambo. Gwamnan ya ce, ya kai ziyarar ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba shi damar samun rahoton halin da ake ciki a kan wannan mummunan...
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
SP Adeh ta kuma ce jami’an ‘yansanda sun ceto wasu mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin farmakin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi. Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%. Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa...

Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Suka Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...

Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Sun Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967. Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus. Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon...
“Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin. “Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an kwato dabbobin da suka sace. “Kwamishanan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an da suka nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikin ceto, ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike “Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar. Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka...
Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Domin tabbatar da zaman lafiya, an tura ƙarin jami’an tsar tare da haɗin gwiwar sojoji domin daƙile tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma yi kira a gare shi da ya fuskanci ƙalubalen tsaro da ke Kano tare da ɗaukar matakan da suka dace don daƙile matsalolin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba. An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin...
Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci. Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda...
Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba. Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan ta’adda su ka yi a gabar ruwan Syria, masu mulki a Damascuss suna boye gawawwakin gabanin isar tawagar MDD zuwa yankin. Mafi yawancin mutanen da aka yi wa kisan gillar a yankin gabar ruwan Syria, fararen hula ne wadanda aka fito da su daga cikin gidajensu,yayin da wasu kuma aka yi musu kisan gilla a gaban iyalansu. Ya zuwa shekaran jiya ana maganar cewa an...
Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar ƙasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki waɗanda suke takun saƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke ƙullawa Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP. NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi DAGA LARABA:...
Mayar da hankali kan taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) da kuma taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar (CPPCC), muhimmin abu ne ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin. Zuwa karshen shekara ta 2024, adadin kamfanonin da baki ’yan kasashen waje suka zuba jari don kafa su a kasar Sin, ya zarce miliyan 1.239. A matsayinsu na wadanda ke gane wa idanunsu, da wadanda ke bayar da gudummawa, gami da wadanda ke cin moriya, daga harkokin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, kamfanonin jarin waje sun riga sun bada hadin-kai tare da samun ci gaba tare da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. A...
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC Aminiya ta ruwaito cewa, Ibrahim Yakubu Adamu wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA. Falgore ya ce nan gaba kaɗan za su aika masa goron gayyata domin tabbatar da buƙatar gwamnan. Kazalika, majalisar ta kuma tabbatar da dokar...
Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu. “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki. Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu. Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Ya ƙara da cewar, wannan sana’a ta ɗinki sana’a ce da ke da matuƙar albarka idan ka sa juriya a ciki domin kuwa ba sana’a ce da za ka tara kuɗi akai-akai ba nan take. “Sai dai kuma muddin ka tsayar da gaskiya tare da cika alƙawari to lalle za ka samu babban rufin asirin...
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP. Majiyoyi sun ce ficewarsa ta biyo bayan rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar. A cewar El-Rufai, APC ta kauce daga ainihin manufofinta, don haka ba zai ci gaba da kasancewa a cikinta ba. Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku Koma wa SDP ya haifar da raɗe-raɗin cewa yana shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, lamarin da ke nuna sauyar tsarin siyasa a Nijeriya, idan har za a samu ɗan takara daga arewa a 2027. A halin yanzu, shugabannin APC...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai. Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na...
An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987. Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005. A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka. Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...
Wani mutum wanda yake nuna kin amincewa da zaluncin da HKI yake yi wa mutanen Gaza, ya hau kan hausumiyar agogon “ Big-Bang” a birnin London dauke da tutar Falasdinu. An sami cunkuson motoci a yankin Westminster dake birnin London a jiya Asabar,yayin da masu ceto suke kokarin isa ga mutumin domin sauko da shi daga kan hausmiyar agogon. Jami’an ‘yan sandan sun sanar da samin rahoton abinda ya faru da misalin karfe 7 na safe,kuma sun fara aiki domin ganin an sauko da mutumin cikin lafiya. Jami’an tsaro sun sanar da cewa an rufe hanyar da take zuwa majalisar saboda abinda ya faru. Haka nan kuma gadar da take zuwa Wesminster da sauran hanyoyin da suke yankin duk an...
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a. Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin. A shekarar...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu. Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati. Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da...
Idan ana maganar masana’antu a Arewacin Nijeriya a shekarun baya a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Bauchi da sauransu, sai ka rantse cewa jihohin Arewa su ne ginshikin ci-gaban tattalin arzikin kasar nan. Sai dai sannu a hankali duk irin wadannan tarin masana’antu da Allah Ya albarkaci yankiin da su, a yanzu sun koma kufai in banda ’yan kalilan da ke yin aiki. WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda A Jihar Kano kaɗai akwai daruruwan masana’antu waɗanda suke rukunin masana’antu na Sharada da na Bompai da na Challawa da sauransu. Hakazalika Jihar Kaduna ma ta kasance cibiyar masana’antu a can baya, amma...
A yau Asabar ne aka gudanar da zama na biyu na taro na uku, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Zaman da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarta. Albarkacin kasancewar yau ranar bikin mata ta kasa da kasa, a madadin tawagar shugabannin taron, zaman ya mika fatan alheri ga mata daga dukkan kabilu, da dukkan bangarorin kasar Sin, da mata na dukkan kasashen duniya. Bugu da kari, rahoton ayyukan zaunannen kwamitin NPC ya nuna cewa, ana shirin bitar dokoki 34 a shekarar nan ta 2025, wadanda suka hada da samar da wata doka, don inganta hadin...
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma yi kira ga Amurka da Iran su warware wannan matsalar ta ruwan sanyi. Ko hanyar diblomasiyya. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa shirinta na makamashin na zaman lafiya ne. Sannan don haka ne ta amince ta kulla yarjeniyar shirin nukliya ta zaman lafiya da manya manyan kasashen duniya, a shekara ta 2015 daga ciki har da kasar Amurka. Amma shugaban kasar Amurka na lokacin Donql Trump ta fidda kasar daga yarjeniyar sannan ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni don tursasa mata ta sake zama don sabuwar tattaunawa da ita. Mohammed...
Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran. Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai...
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu. Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris. NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa SP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47. Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da...

Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Da CGTN Ta Gudanar Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Diflomasiyyar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Jami’ar TTarayyada ke Dutse a Jihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammed ya amince da nadin Malam Abdullahi Yahaya Bello, a matsayin Daraktan riko na Jami’ar daga ranar 1 ga watan Maris na 2025. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardar jami’ar, Alhaji Abubakar Mijinyawa ya rabawa manema labarai a Dutse. Sanarwar ta taya Malam Abdullahi murna tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi nasara wajen sauke nauyin da aka dora masa. Malam Abdullahi Yahaya Bello shi ne ya kafa sashen yada labarai da hulda da jama’a na jami’ar a shekarar 2012 a matsayin jami’in hulda da jama’a na Jami’ar na farko. Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, ya ci gaba da zama mataimakin...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya. Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya. Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa. “Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu. “Duk da haka, a wannan...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya. Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya. Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa. “Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu. “Duk da haka, a wannan...
“Wadanda aka samu da laifi doka za ta hukunta su. “Ayyukan sun kai ga kwato tarin muggan makamai, haramtattun abubuwa, da abubuwan da ke da alaka da aikata laifuka. Wadannan sun hada da busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi ne, gatari uku da adduna uku, wadanda galibi ake amfani da su wajen aikata munanan laifuka. “Kananan bututu guda shida na manne, bongs din hannu guda biyar, kayan da aka fi hadawa da abubuwan maye, almakashi guda takwas, katunan ID guda biyar, kananan kwantena na filastik da yawa da wasu kwayayen da ake zargin haramun ne. “Rundunar ta kuma kara sanya ido kan gine-ginen da aka yi watsi da su da kuma wuraren da aka gano a matsayin maboyar masu...
Da yake magana kan aikin, Hundeyin ya bayyana cewa, kungiyoyi masu amfani da dabaru da ke Elemoro ne suka yi kamen, inda suka rufe hanyar Ajah, ciki har da Lekki Phase 1 zuwa Epe. “Tawagarmu ta dabara da ke Elemoro ce ta gudanar da wannan aiki tare da rufe adis na Ajah, kamar Lekki Phase 1 zuwa Epe. Sun gudanar da wannan aiki. Aanu Ayoade, Aminu Abubakar, Olayiwola James, Sahedu Abubakar, Taiwo Fawasi, Muhammed Monsuru, Abdullahi Ibrahim, Uche Achuoye, Samuel Olapade, El-Kamal Ibrahim, Hammed Taofeek, and Jamilu Usman. “Muna da kungiyoyin dabaru a wasu sassan jihar, kuma suma suna da irin wannan na kama masu aikata laifuka tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu,” in ji...
Wasu kwararru a fannin na aikin noman, sun alakanta samun wannan karuwar, saboda dauki daban-daban da gwamnatin tarayya ta samar ga fannin, musamman wajen kokarinta na rage kalubalen rashin tsaro. Daga cikin wannan daukin na gwamnati, sun hada da kirkiro da shirin jami’an tsaro na sintiri sama da 1,000 da aka tura zuwa kanannan hukumomi 19 a 2024, don bai wa manoma da amfanin noma da aka shuka kariya, inda shirin ya taimaka wajen kara bunkasa aikin noma. A cewar Hukumar ta ‘NBS’, fannin aikin noma ya samar da kashi 25.59 wajen habaka fannin tattalin arzikin kasar, wato ma’ana, a zango na uku na 2023, gudunmawar da fannin ya samar ga tattalin arzikin kasar, ya tsaya ne a kashi 26.11,...
Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin kiwon dabbobi. Shugaban ya yi fatan nadin Farfesa Jega zai haifar da ci gaba mai ma’ana a fannin kiwo, da kuma kara karfafa ayyukan ci gaban kasa. Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Jega ne ya jagoranci Kwamitin Kiwo na Shugaban Kasa tare da Shugaba Tinubu. Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya bayar da cikakkun shawarwarin da suka tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a fannin kiwon dabbobi, daya daga cikinsu shi ne...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ja hankalin shugabannin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana domin samun goyon bayan gwamnonin shiyyar. Gwamna Umar Namadi ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada a gidan gwamnati da ke Dutse. Ya ce, Hukumar Raya Arewa maso Yamma, ita ce mafi girma a cikin shiyyoyin kasar nan, a don haka bai kamata a fuskanci wasu matsaloli ba daga gareta. Namadi ya bukace su da su mai da hankali da jajircewa, tare da yin aiki da abubuwan da gwamnoni suka sa gaba domin samun nasara. Tun da farko, Shugaban Hukumar, Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya ce...
“Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun. Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane. Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi. Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo. Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya...
Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar. Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.6. “Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya. Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin...
“Bisa ga ajandar sabunta fata na Shugaba Tinubu, mun himmatu wajen tabbatar da manufofi da ka’idojin da suka jagoranci hukumar tsawon shekaru. “Ina kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya, musamman maniyyatan da suka yi niyyar zuwa aikin hajjin 2025, za su gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da NAHCON bisa sakamakon aikin hajjin 2025. “Shugaban kasa yana tsayawa kan Magana daya. Yana ba mu dukkan goyon bayan da ya kamata. Ba za mu ci amanarsa ba. Ba za mu sauka daga kan manufarmu ba. “A kan wannan, dole ne mu gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima bisa yadda suka ba mu amanar tafiyar da harkokin aikin hajji. “Hukumar ta samu wasu nasarorin da suka shahara...
Ba Zaura kadai ba ne yake kokarin ganin a samu zaman lafiya a tsakanin ‘yan siyasar guda ukun. Sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da suka hada da dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar a zaben 2023, Murtala Sule Garo da kuma fitaccen dan siyasa, Baffa Babba Danagundi, sun yi irin wannan kira. Kwankwaso, Ganduje, da Shekarau, wadanda dukkansu sun yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Kano, suna jam’iyyun siyasa daban-daban, kuma sun ci gaba da yin tasiri sosai a matakin kananan hukumomi, jiha, da kasa baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Ana sa ran shirin zai inganta samar da abinci, rage rikice-rikicen Makiyaya da Manoma, da kuma samar da damarmaki ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke dogaro da kiwo a matsayin sana’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

‘Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Kananan Hukumomi 749 Sun Gaza Bayar Da Cikakkun Bayanan Asusunsu
A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.” Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba. Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas. “Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don...
Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, zuwa karshen watan Fabarairun shekarar nan ta 2025, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin, ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2272, adadin da ya karu da dalar Amurka biliyan 18.2, sama da na karshen watan Janairu, wato karuwar kaso 0.57 cikin dari. Wani jami’i mai aiki a hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai inganci, da fa’ida mai yawa, da juriya mai karfi, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da matakan da suka wajaba na cimma nasarar tsare-tsare masu inganci, na bunkasa rundunar sojin kasar Sin na shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojin kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne a Juma’ar nan, yayin da yake halartar taron rukuni na tawagar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin PLA, da rundunar ‘yan sandan kasar, a wani bangare na taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp