2025-04-16@18:08:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3377

«neman ikon mallakar»:

    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya. Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da rashin mutunta juna. Mista Araghchi ya bayyana hakan ne a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin Iran na mako-mako a birnin Tehran babban birnin kasar, bayan da manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya ce Tehran “dole ne ta kawar da” shirinta na inganta makamashin nukiliya domin cimma matsaya da Washington. Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin ke shirin ganawa  a ranar Asabar....
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al’ummar duniya da su ba da himma wajen shiga wani gangami na tsawon mako guda domin ganin an kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, Hamas ta yi kira ga “kasashen Larabawa da na musulmi da kuma ‘yantattun mutane” na duniya da su halarci gangamin na ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi (18, 19 da 20 ga Afrilu). Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta ayyana wadannan ranaku a matsayin “ranakun nuna fushin duniya dangane da mamaya.” Hamas ta sake nanata bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don kawo karshen “ci gaba...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023. Juyin mulkin da sojojin sukayi a Nijar ya haifar da takaddamar diflomasiyya sosai tsakanin Nijar da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta a wannan karon. Batun mayar da hambararen shugaban Nijar Bazoum da kin lamuncewa juyin mulkin daga gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar ta ECOWAS, shi ne a sahun gaba a...
    Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar. Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur. Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.”  Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan. Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu...
      Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba 16 ga wata cewa, mizanin hada-hadar tattalin arziki da aka fi sani da GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara a cikin rubu’in farko na shekarar 2025. A tsakanin wannan lokacin, alkaluman hukumar sun kuma bayyana cewa, mizanin ya nuna hada-hadar tattalin arzikin kasar ta kai yawan adadin kudin Sin yuan tiriliyan 31, da biliyan 875 da miliyan 800, kwatankwacin dala tiriliyan 4. 42.   Har ila yau, kamar yadda alkaluman mahukuntan suka nuna, karuwar darajar kayayyakin da masana’antu suka samar ta kai kaso 6.5 bisa dari duk dai a rubu’in farkon na bana. An samu wannan bunkasa ce...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki. Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami. Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan  diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani  ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
    Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar.   Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta. Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani...
    Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar. A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu. Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare. Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take. Ya ce ” Ina...
      Ƙarin bayani na tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan  diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani  ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
    Don su wuce zuwa zagaye na gaba, Real Madrid na buƙatar ta zura ƙwallaye huɗu ba tare da ta bari Arsenal ta zura ƙwallo ko ɗaya ba. Idan kuma suka ci ƙwallo uku, kamar yadda Arsenal ta ci su, za a ƙara lokaci domin a fidda wanda yi nasara. Fitaccen ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe, wanda bai taɓa lashe gasar Zakarun Turai ba, yana fatan ya lashe kofin karo na farko tare da Real Madrid. Wannan wasa zai ba shi damar jan ragamar ƙungiyar don yin nasara a gaban dubban magoya bayanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Ya jaddada cewa dole ne a gyara jam’iyyar PDP kafin a fara tunanin neman wani muƙami. Ya ƙara da cewa ko da siyasarsa ta tsaya a matsayin gwamna, zai kasance cikin farin ciki da gamsuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    HKI tana ci gaba da kai wa yankunan Gaza mabanbanta hare-hare da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai a yau Laraba. Tun da safiyar yau Laraba ne HKI ta kai hari akan wani gida dake unguwar “al-Tuffah” dake cikin birnin Gaza da hakan ya sa mutane 6 su ka yi shahada. A yankin Jabaliya kuwa jiragen yakin HKI sun kai hari akan wani gida da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3. A wani labarin kungiyar ” Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba” ta bayyana cewa; Isra’ila ta mayar da yankin Gaza zuwa Makabarta. Kungiyar ta bayyana cewa; Yadda Isra’ila take fadada wuraren da take kai wa hare-hare ta sama, kasa da ruwa a yankin Gaza , tana korar mazauna yankin...
    Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria. Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa. Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, Shirin janyewar sojojin na Amurka bai zama abin mamaki ba,domin tun farkon rantsar da Donald Trump ne ya bayyana aniyarsa na janye sojojin kasar daga Syria. HKI tana jin cewa, idan har Amurkan ta janye daga kasar Syria, to Turkiya za ta kara azamarta ta shimfida ikonta a cikin kasar. Tun a Zangon shugabancinsa na farko ne dai Donald Trump ya bayyana cewa Idan kungiyar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba. Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan...
    Haka kuma a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, ya amsa cewa ya kashe wani mutum sannan ya sayar da babur ɗinsa wanda ya sace a kan kuɗi Naira 300,000. Rundunar ‘yansanda ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), don tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi da kuma gano ko akwai wasu da suke tare da shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da matakin da Umar ya ɗauka na miƙa kansa, tare da kira ga sauran masu laifi da su kwaikwayi irin wannan mataki. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kawar da masu aikata laifi a faɗin...
    Ya ce suna ci gaba da bincike a cikin dazuka da ke kusa da garin. Ɗan majalisar dokokin Jihar Benuwe mai wakiltar mazaɓar Otukpo-Akpa, Kennedy Angbo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na yamma kuma jama’a da dama sun tsere daga garin saboda tsoro. Wani mazaunin Otobi, Edwin Emma, ya ce wannan ne karo na biyu da ake kai musu hari cikin wata guda. “Matata da ’ya’yana sun tsere a kafa yanzu haka. Muna buƙatar taimako,” in ji shi. Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benuwe, Catherine Anene, bai yi nasara ba domin wayarta a kashe ta ke. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila. Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta. Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan...
    An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila. Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta. Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan...
    Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Wata majiyar HKI, yahudawa ta fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Ynetnews’ kan cewa sojojin sama na HKI su na dakon isowar boma-bomai har 3000 daga kasar Amurka a cikin yan makonni masu zuwa. Labarin ya kara da cewa rundunar ta na son ta gudanar da ayyukan soje mai fadin gaske a kan Falasdinwa wanda ya zai kawo karshen Hamas ya kuma kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Labarin ya kara...
    Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto  wani mai magana da yawan dakarun yana fadar haka a wani fai-fai bidiyo da rundunar ta watsa a yanar gizo a jiya talata. Dakarun suna kira ga iyalan yahudawan da su yi shirin karban gawakin yayansu a cikin akwatunan gawaki, wannan kuma saboda yadda jiragen yakin HKI suke kai hare-hare babu kakkautawa kan gaza ba tare da bambanta tsakanin  yara da mata da sauransu ba. Sakon Bidiyon yana...
    A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI,  Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne,  haka ma, karfin sojojin kasar. Janar Naeini ya ka ra da cewa, rawar dajin da sojojin IRGC suka yi a baya-bayan nan ya na tabbatar da hakan. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, Burgediya Janar Naeini yana maida martani ne ga gwamnatin Amurka wace ta fara maganar cewa, zata tattauna da kasar ta Iran ne a kan shirinta na makamai masu linzami, da kuma shirin ta...
    Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
    Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda ya tattara wakilai daga kasashen Faransa,  Burtaniya,  Jamus da kuma kungiyar tarayyar Turai, har’ila yau da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Sudan. Labarin ya kara da cewa, yakin na Sudan wanda yake cika shekaru biyu, ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 20,000, sannan ya yi sanadiyar kauracewar mutane kimani miliyon 14 zuwa cikin kasar da kuma kasashe makobta, sannan wasu da...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 18, da kuma Litinin, 21 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Easter a faɗin ƙasar. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo A jawabin da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida , Dokta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai. Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan lokaci, Mista Tunji yana kuma kira...
    Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park. Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a zagayen kwata fainal. DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ana barazanar korar sojojin Isra’ila da ke neman a kawo ƙarshen yaƙin Gaza Ita kuwa ƙungiyar ta Faransa ta ci nata ƙwallayen ta hannun Hakimi da kuma Nuno Mendes. PSG ta kai zagayen gaba da cin 5-4 gida da waje jimilla, bayan da ta yi nasarar cin 3-1 a makon jiya...
    A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya.   Shirin ya mai da hankali ne kan muhimman batutuwa kamar gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama, da gadan al’adun gargajiya da kirkire-kirkire, da kare nau’ikan halittu, da mu’amala da koyo a tsakanin al’ummomi, ya kuma gabatar da fitacciyar hikimar shugaba Xi Jinping wajen gudanar da mulkin kasar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya.   A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa.   Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan.   Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...
    Da wannan sakamakon na 5-3 a duka wasannin biyu Barcelona ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe a karon farko tun a shekarar 2016 da su ka buga wasa a wannan matakin na gasar Zakarun Turai tare da Athletico Madrid. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan  da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
    A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.   Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata.  ...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa. Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana. Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir  ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori. Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai  cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai  ta Jihar  daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025. Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci...
    Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”.   Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.   Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin  jihar da ke Dutse. A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka zai kasance ne a birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman. Baghaei ya yi watsi da rade-radin da ake yi kan inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce, “Bayan tuntubar juna, an yanke shawarar cewa birnin Muscat ne zai karbi bakwancin zagaye na biyu na shawarwarin, wanda za a yi a ranar Asabar mai...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar. Jami’in na kungiyar Hamas ya kara da cewa: A ranar litinin din nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma yin watsi da alkawurran da ta dauka, yana mai cewa kungiyar Hamas ta tabbatar wa masu shiga tsakani da “bukatar bayar da lamuni don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar.” Yana mai bayyana cewa,...
    Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.   Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...
    A kwanakin nan da suka gabata kuma, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 5, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wato Canton Fair karo na 137 a nan kasar Sin, inda yawan kamfanonin da suka halarce su suka kai matsayin koli a tarihi. Shugabar kwalejin nazarin tattalin arzikin Sin bisa salon kirkire-kirkire ta kasar Brazil madam Claudia Jannuzzi, ta ce Sin na matukar bude kofarta ga sauran sassa, tare da ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya.   Cinikin shige da ficen Sin na samun bunkasuwa mai dorewa a gabanin duk wani kalubale. Ba shakka duniya za ta ga hakikanin halin da ake ciki, wato babu mafita a aiwatar da...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...
    A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar.   A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in.   Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kafa sashen kula da masu fama da matsalar kwakwalwa a jihar ya zama doka. Dokar za ta samar da kariya da kuma bunkasa ‘yancin masu fama da matsalar kwakwalwa musamman masu tu’ammuli da muggan kwayoyi a fadin jihar Kaduna. Da yake jagorantar zaman majalisar, shugaban majalisar dokokin jihar kaduna, Yusuf Dahiru Liman ya sanar da amincewa da kudirin wanda aka yiwa lakabi da kudirin kula da lafiya masu fama da cutar kwakwalwa na jihar Kaduna. Da yake gabatar da rahoto, shugaban kwamitin hadin gwiwa na lafiya da sharia, wanda aka dorawa alhakin yin nazari a kan wannan kudiri, Mr. Haruna Barnabas ya ce sun yi nazarin kudirin sannan sun gano cewa akwai...
    Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
    Hansi Flick na fatan lashe UEFA a karo na biyu a tarihinshi na horarwa, bayan da ya lashe na farko tare da Bayern Munich a shekarar 2020, hakazalika, Barcelona na gab da lashe gasar bayan shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin.  
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a Vietnam, shugaban CMG Shen Haixiong, ya kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da shugaban gidan radiyon Vietnam Nguyen Thanh Lam, da shugaban gidan rediyon na Voice of Vietnam Do Tien Sy, kana da shugaban kwalejin yada labarai da fadakarwa na Vietnam Pham Minh Son, a gaban shugabannin kasashen biyu wato Xi Jinping da Tô Lâm. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia.   Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa a tsakanin bangarorin biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin ayyukan zamanantarwa, da sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi, da inganta gina al’umma mai kyakkaywar makomar bai daya tsakanin Sin da Malaysia zuwa wani sabon...
    Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu. EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan. Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da...
    Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar moriyar kai, gami da neman tabbatar da adalci a duniya.   Da ma shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gabatar da jerin zafafan matakan tattalin arziki ne don neman daidaita matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta. Sai dai ra’ayinsa na dora “Amurka ta zama gaba da komai” na tarnake masa damar samun biyan bukata.   Raymond Thomas Dalio, shahararren mai kula da sha’anin hada-hadar...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, ta gaza tabbatar da zargin wulaƙanta takardar Naira da take yi wa fitacciyar ’yar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya. A bayan nan ne EFCC ta gurfanar da Murja a gaban kotu kan zargin cewa ta ci karo da wani bidiyonta tana rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400. A ƙunshin ƙarar da EFCC ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ta ce laifin da take tuhumar Murja tanadi na Kundin Dokokin Babban Bankin Nijeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.  
    Hukumar tace fina-finai na ci gaba da yaƙi da duk wani abu da ya saɓa da tarbiyya da addini a kafafen sada zumunta a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris. OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata. Sabon rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin ya ce yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairu. A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce Algeria da...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
    Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda. Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba Bola Tinubu, da nufin kawo masu zuba jari na kimanin Dala biliyan guda a ɓangaren sukari a Najeriya. Daga cikin yarjejeniyar, Kamfanin SINOMACH zai kafa masana’antar sukari da kuma gonar rake da za su fara da samar da metrik ton 100,000 na sukari a duk shekara. Kamfanin zai kuma taimaka da kwarewarsa da kayayyakin aikinsa wajen zartar da abubuwan da suka danganci gine-gine sayayyan kayan...
    Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bagaei ya bayyana cewa kokari da JMI a tattaunawarta da kasar Amurka kan shirin Nukliyar kasar shi ne ganin an dauke  mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata,  ko amurka da dora mata.. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yana fadar haka a jiya, Litinin a lokacinda yake jawabi gay an jaridu a ko wani mako. Bagaei har ‘ila yau ya tabo al-amuran da suka shafi yankin kudancin Asiya da kuma karya yarjeniyar tsagaita wutan da HKI ta yi a Gaza. Ya kuma kara da cewa degewa Iran wadanan takunkuman dole ne su kasance mataki na farko don ganin hanyar diblomasiyya ta...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
    Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara. Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu.. Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma...
    Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci,  har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...
    Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza. Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi. Wadanda su ka rattaba hannu akan wasikar sun bayyana goyon bayansu ga wasikar da sojan sama su ka rubuta a ranar 9 ga watan Aprilu da ake ciki,ko da kuwa sakamakon hakan shi ne kawo karshen yaki. A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,dubban sojojin HKI sun rattaba hannu akan wasika wacce take yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma dawo da fursunonin da suke...
    Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai  harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa. Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya dauki labarin ya ambaci cewa,an gano gawawwaki 51 daga cikin wadanda aka kashe din, kuma wani adadi mai yawa na mutanen kauyukan sun jikkata. Ita kuwa kungiyar “Amnesty International” ta ambaci cewa maharan sun kuma rusa gidaje, tare da wawashe kayan da suke cikinsu. Kungiyar ta zargi jami’an tsaron kasar da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro. Jahar Filato ta dade...
    Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Samson Zakhom, ya bayyana cewa an ceto mutanen ne da misalin ƙarfe 9 na dare bayan sun tsinci motar a daji babu kowa a ciki. Ya ce ganin haka ne sojojin rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar suka yi zargin sace fasinjojin cikinta aka yi. An yi garkuwa da masu ibada a Kogi Yadda kisan mutum...
    Kasashe da dama sun bi sahu a wannan karnin, inda Saudiyya ta zama ta baya-bayan nan, wajen ba mata ‘yancin kada kuri’a a kananan zabukan kasar a shekarar 2015. (Ba su yin zaben shugaban kasa a Saudiyya.) A cewar Majalisar Dinkin Duniya, wannan ya sa yanzu mata a kowace kasa suna da ‘yancin yin zabe. Sai dai Afghanistan a karkashin mulkin Taliban, ta mayar da hannun agogo baya wajen kwace wa mata hakkin zabe. “Matan Afghanistan sun samu damar kada kuri’a ne kimanin shekaru 100 da suka gabata, amma yanzu a karkashin mulkin Taliban, an cire a tsarin dimokuradiya,” in ji tsagin mata na Majalisar Dinkin Duniya, sashen da aka ware domin karfafa gwiwar mata. Zuwa tsakiyar karni na 19,...
    A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya. A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla. Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a...
    Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48. Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno Rotayo,tare da cewa za ta mayar masa da martanin da ya dace. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Aljeriya ta bayyana cewa; A matsayinta na kasa mai cikakken shugabanci, tana daukar ma’aikatan ofishin jakadanci Faransa 12 a matsayin wadanda ba a maraba da su, sannan kuma ana bukatar da su fice daga kasar a cikin sa’oi 48.”  Aljeriya din ta dauki wannan matakin ne a matsayin...
    ’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba. Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su. Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yankin Egbola, a kan hanyar Agabja a Ƙaramar Hukumar Lokoja. Shaidu sun bayyana cewa ’yan bangan gwmanatin jihar sun yi nasarar ceto wata mata daga cikin masu ibadan, bayan sun samu rahoton aukuwar lamarin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura Wani ɗan banga daga cikin waɗanda...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwarsu. Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16978635-dalilan-rikice-rikice-a-jihar-filato.mp3?download=true
    Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki.   Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki...
    Dadin dadawa, Sin za ta ci gaba da shimfida yanayin ciniki mai inganci, da samarwa kamfanonin ingantattun hidimomi. Sin na maraba da masu zuba jari na sassan duniya da su gudanar da hada-hadarsu a kasar musamman ma wannan tasha ta ciniki maras shinge da more zarafin ci gaban Sin tare. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani. Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar. A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar za su ba da sunayen dalibai uku, yayin da aka ware wa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, guraben dalibai 10. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin tafiyar daliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta dauki nauyin karatunsu da walwalarsu bayan isarsu. Mai ba da...
    Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar. Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun da ke sintiri sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka je daga yankin Falmey. Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina Kazalika ranar Alhamis ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kama ‘yan bindiga 12 a ƙauyen Jagada da ke yankin Diffa. TRT ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan...
    Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai  Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40. A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato. Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon  bambancin addini da kabila. Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai...
    Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku. Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sashen ilimi. Da take jawabi a wajen taron, Minista a ma’aikatar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Sa’id ta bayyana cewa, a ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi na ƙarfafa tsarin ilimi, ya amince da kashe Naira biliyan 120 don bunƙasa shirin fasaha da koyon sana’o’i (TVET) a Najeriya. Ministar ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa. Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya ce shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai ziyarci Tehran a ranar Laraba.   Gharibabadi ya bayyana cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, zai gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami. Ya kara da cewa “ziyarar na cikin tsarin ci gaba da hulda da hadin gwiwa tsakanin bangarorin...
    Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa. “Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.” Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami. A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya,...
    Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka. Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya. A cikin sakon da ya wallafa, Falconer ya yaba da tattaunawar da akayi a babban birnin kasar Oman na Muscat a matsayin “muhimmiyar mataki na farko.” Kuma a cewarsa “Birtaniya, tare da kawayenta na E3, a shirye suke don tallafawa tattaunawar. A cikin 2018 a lokacin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma a baya kan shirin nukiliyar Iran da...
    Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage a zirin Gaza da aka yi wa kawanya, domin musanya abin da ya bayyana da ” fursunoni” da kuma tabbatar da kawo karshen yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi. Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto Taher al-Nunu na cewa: “A shirye muke mu sako dukkan ‘yan Isra’ila da ake tsare da su a yarjejeniyar musayar fursunoni, da kawo karshen yakin, da janyewar sojojin Isra’ila daga zirin Gaza da shigar da kayan agajin jin kai.” A halin yanzu Hamas na tattaunawa a birnin Alkahira tare da masu shiga tsakani na Masar da Qatar. Saidai, duk da haka, jami’in na...
    Kasashen Iran da kuma Iraki sun kudiri anniyar karfafa alaka ta fuskar makamashi. A ganawar da suka yi a birnin Bagadaza, kasashen biyu sun jaddada fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin mai da iskar gas, inda kasar Irakin ta bayyana matukar sha’awar yin hadin gwiwa a fannin fasaha da zuba jari da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Taron ya yi nuni da karfafa huldar dabarun samar da makamashi tsakanin kasashe biyu masu makwabtaka da juna. Mataimakin firaministan kasar Iraki mai kula da harkokin makamashi Hayan Abdul-Ghani Al-Sawad ya bayyana cewa, Iraki na ci gaba da gudanar da ayyukan da ke da nufin cimma dogaro da kai wajen samar da albarkatun man fetur. Ya jaddada aniyar Bagadaza na fadada hadin gwiwar...
    Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta. Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini. An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta Sai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki. Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da...
    Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar mai shekaru 22 daga Angwan Tana, an ce wanda ake zargin ya yi ma ta dukan jakin ne mai tsanani, Shaibu, wanda ake cewa shi ne dan uwanta. Wannan lamarin ya janyo zarge-zargen daga al’umma da kuma kiran da aka yi wa Yansanda daga mutanen gari, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama domin a kama wanda ake zargi. Ƴansanda Sun...
    A wannan Litinin ɗin ce ne aka rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina waɗanda aka gudanar da zaɓensu a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025. Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin. ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato Sai dai gab da lokacin da za a rantsar da su, ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu. Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori Honarabil Aminu Ɗan Hamidu shi ne wanda ya faɗi kuma aka ɗauka ranga-ranga zuwa asibiti. Binciken da muka yi ya nuna cewa,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya dawo daga yawon sallah ne ya far wa garin da hari. ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume “Turji da yaransa sun bar kauyensa na Fakai a Karamar Hukumar Shinkafi suka shiga wasu kauyukka a Karamar Hukumar Isa a hanyarsu ta komawa Fakai bayan sun gama...
    Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura.   A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp