2025-04-14@09:57:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3269

«shugaban hukumar»:

    Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar. Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan. A wata zantawar da aya yi da ’yan jarida a ƙarshen mako, ɗan Majalisar Dattawan ya ce mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare 252 a daga watan Nuwamban 2024 zuwa yanzu. Ya bayyana damuwa game da dawowar munanan ayyukan kungiyar a jihar duk kuwa da kokarin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi domin murƙushe su. Abincin karnuka ya fi wanda ake ba mu —Fursunonin Najeriya NAJERIYA A YAU:...
    Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas.   A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamna Sani ya bayyana cewa, an yi biris da aikin hanyar na tsawon shekaru da dama, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin.   Sai dai Gwamnan ya kafa uzurin cewa, baya ga kudade, rashin tsaro da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin ne kamfanin Berger ya ki zuwa wurin domin...
    Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi. Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa. Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya tare da wani kwamitin bincike mai zaman kansa sun ƙaryata zarge-zargen fursunonin kan yunwa a gidajen yari. A watan Satumban 2024 ne Ministan Harkokin Cikin Gida,  Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa a kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin jami’an gidajen yari da cin hanci da kuma cin zarafin fursunonin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno An sake...
    Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar. Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600.  Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic ...
    Wani babban jami’in Diblomasiyya na kasar Iran ya bada sanarwan cewa zagaye na biyu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka za’a gudanar da shi ne a kasashen Turai a ranar 19 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin waje na JMI kan al-amuran da suka shafi siysa Majid Takht-Ravabchi yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake gabatarwa Majalisar dokokin kasar Iran rahoto kan taron tawagar Amurka da kuma JMI a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Jami’in diblomasiyyar ya kara da cewa, a tattaunawar da ba kai tsaye ba tsakanin kasashen biyu a ranar Asabar da ta...
    Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba. Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin...
    ’Yan sanda sun kama shahararren mawaƙin zamani a Najeriya Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, bayan ƙazancewar rikicinsa da fitaccen ƙwararren mawakin Fuji, Okunola Saheed “Osupa.” A ranar Lahadi da dare ne ’yan sanda daga Jihar Kwara suka yi takakkiya suka kamo Portable mai waƙar “Zazu Zeh” a garin Abeokuta, Jihar Ogun Kakakin ’yan sanda na Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya ce an kama Portable bayan samun takardar ƙorafin da Osupa ya aike ɗauke da jerin manyan zarge-zarge da yake yi wa mawakin na “Zazu Zeh,” na ɓata suna, barazanar kisa, tunzura jama’a, zubar da da mutum da gangan, neman tayar da fitina, da kuma amfani da zagi da munanan kalamai. “Saboda girman waɗannan zarge-zarge da...
    Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa.  Haka ma tsakanin kasashen yankin. AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da...
    Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar. Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa. Brice zai jagoranci kasar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo. Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa guda 70 da sauran kayayyakin noma domin tallafawa manoman shinkafa. A don haka, Gwamna Umar Namadi ya yi gargadin hukunta duk wanda aka samu ya karkatar da kayayyakin aikin gona da gwamnatin ta samarwa manoman jihar. Yana mai cewar, fiye da manoma dubu hamsin da biyar ne za su amfana da shirin, wanda wani bangare ne na kokarin gwamnati na bunkasa aikin gona da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya. Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki. Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa. Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba. An...
    A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal dake matsayi na biyu a kan teburin gasar. Yayinda yake saura wasanni shida a kammala gasar, Liverpool na buƙatar maki 3 kacal domin lashe gasar a karo na biyu tun bayan da aka sauya wa gasar suna da fasali, West Ham na matsayi na 17 da maki 35 akan teburin gasar. Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah Salah Ya Ƙulla...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi amfani da bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama ta yin aiki tare da shugaba Prabowo, wajen kara zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da karfafa hadin gwiwa a batutuwan da suka shafi bangarori daban daban bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da inganta al’ummar Sin da Indonesiya mai kyakkyawar makomar bai daya daga dukkan fannoni, kuma...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu ya fusata da kuma kara takaicin masu mugun nufi kan lasar ta Iran. Yana mai bayyana cewa, tabbas akwai rauni a fannonin da suka shafi tattalin arziki da ya kamata a magance. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi la’akari da cewa; Sojojin kasar suna matsayin kariya ta al’umma da kuma mafakar al’umma daga duk wani mai wuce gona da iri, sannan kuma ya jaddada...
    Kwamandan rundunar sojojin kasa ta Iran ya bayyana cewa: Nan ba da jimawa ba za a yaye labulen ire-iren makamai na musamman da Iran ta mallaka Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya yi nuni da shirin rufe kan iyakar kasar da ke gabashin Iran, yana mai cewa: Wannan ba kawai wata katanga ba ce mai tsayin mita 4, saboda an tanadar da ita ce da nau’o’in makamai masu kwaloluwar ci gaba na zamani a duniya, wannan shiri an gudanar da shi ne tsawon shekaru hudu kuma za a kammala shi nan da shekaru uku masu zuwa. Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran ya jaddada haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a...
    Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yakin da ake yi a Gaza A karkashin taken “An rusa Gaza” kuma goyon bayan al’umma ga Falasdinawa abu ne da ya zama wajibi, ba zabi ba, mazauna birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada bukatar musulmi a ko’ina a duniya su goyi bayan gwagwarmayar da ake yi a Zirin Gaza. Zanga-zangar dai ta samu halartar kungiyoyin ‘yan jaridu da sauran kungiyoyi da dama, wadanda suka bayyana Allah wadai da shirun da manyan kasashen duniya suka yi, tare da sukar su kan goyon bayan sojojin mamayar Isra’ila. Wani sheikhin malami dan kasar Mauritaniya ya ce: “Sun sanar da mu irin wannan gagarumin aiki, Allah Ya saka...
    Sa’an nan, dangane da layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada kasar Laos da kasar ta Sin, mista Siphandone ya ce, layin dogon ya haifar da alfanu sosai, a fannin tattalin arziki, wanda ya zarce yadda aka zata a baya. Kana wannan layin dogon zai zama wani bangaren sabon layin dogon da ya hada kasar Sin da kasar Singapore, wanda za a shimfida shi a nan gaba. (Bello Wang)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro sun kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 sannan ta kama mutane 650 da ake zargi a Jihar Kano. Kwamitin Dawo da Zaman Lafiya da Kyautata Dabi’un Matasa ta Jihar Kano ce ta yi wanna kame a fadin jihar, kamar yadad ta bayyana a rahotonta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana, ya bayana cewa mutum 150 daga ckin adadin an kama su ne kan laifukan dabanci da kwacen wayada da dangoginsu. Kwamitin ya ce aikin haɗin gwiwar, ya yi wannan nasara ne bayan da suka kai samame a kan maboyar masu aikata laifuka da aka gano a kananan hukumomi takwas da ke garin Kano. An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar...
    Jami’an tsaro sun kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 sannan ta kama mutane 650 da ake zargi a Jihar Kano. Kwamitin Dawo da Zaman Lafiya da Kyautata Dabi’un Matasa ta Jihar Kano ce ta yi wanna kame a fadin jihar, kamar yadad ta bayyana a rahotonta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana, ya bayana cewa mutum 150 daga ckin adadin an kama su ne kan laifukan dabanci da kwacen wayada da dangoginsu. Kwamitin ya ce aikin haɗin gwiwar, ya yi wannan nasara ne bayan da suka kai samame a kan maboyar masu aikata laifuka da aka gano a kananan hukumomi takwas da ke garin Kano. An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar...
    Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, kuma suna dauke da bindigogin toka guda uku, da adduna da wukake a lokacin da aka kama su. Kakakin ’yan sanda an jihar, CSP Moses Yamu, ya ce kanawan da aka kama mafarauta ne ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa makiyaya ba ne. Ya bayyana cewa jami’an kungiyar tsaro ta Jhar Edo ne suka kama mafarautan sannan suka damka su ga...
      Kungiyar Kwararrun Masu Fasahar Injiniya ta Ƙasa (NATE) ta rantsar da sabbin shugabannin reshen Jihar Kaduna da za su jagoranci harkokin kungiyar a jihar.   Mataimakin Shugaban Yankin Arewa maso Yamma na NATE, Injiniya Bala Muhammad, yayin bikin rantsarwa da aka gudanar a Kaduna, ya bukaci sabbin shugabannin da su fifita haɗin kai da ci gaban ƙungiyar.   Sabbin shugabannin da aka rantsar sun hada da: Injiniya Audu John a matsayin Shugaba, AbdulKadir Julde a matsayin Mataimakin Shugaba, sannan Williams Okonkwu a matsayin Sakataren reshen.   Sauran su ne Sim Marca Maikege a matsayin Ma’ajin Kuɗi, AbdulGaniu Isah a matsayin Sakataren Kuɗi, da Racheal Ovbiagele a matsayin Sakataren Fasaha.   Haka kuma, Engr. Ishaya Buba daga Radio Nigeria Kaduna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero. Shaida sun ce da  misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba. “Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin arziki da gobarar tankar mota da ambaliyar ruwa da gobara, abin da yake biyo baya shi ne gwamnati ta raba tallafin shinkafa da sauaran kayan abinci, tamkar shinkafa ita ce maganin duk wata matsala. A wasu lokutan, a kan raba babura masu kafa uku da dabbobi a matsayin tallafi. Makudan kudaden da gwamnatoci suke kashewa da sunan bayar da tallafi, inda ba a ganin tasirin...
    Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba. ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.   “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.   “Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa.   “Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma.   “Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta...
    Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga ɓangaren zantarwa na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri Hakan dai ya ci karo da yadda aka yi hasashe a lokacin da aka kaddamar da ’yan majalisar su sama da 460 domin fara aikinsu na wakilcin ’yan Nijeriya sama da miliyan 230 a...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse. A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza. Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin  alhazan jihar na shekarar 2025. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan...
    Gwamnatin Amurka ta sanar da janye sabon harajin da ta ƙaƙaba wa kayayyakin laturoni irin su wayoyin salula, kwamfutoci da sauran na’urorin da ake shigo mata daga ƙetare. Ana sa ran matakin ya rage raɗaɗin tashin farashin kayayyakin da zai faru a Amurka bayan da a kwanaki Shugaba Donald Trump ya lafta wa ƙasashe ciki har da China haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar. Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri Janar Tsiga, Mahaifiyar Rarara da muhimman mutane da aka sace a Katsina Sai dai gwamnatin ta Amurka wacce ta sanar da sassaucin ta hannun hukumar kwastam ba ta bayyana dalilin cire harajin ba. Amma dai ana sa ran kamfanonin fasaha na Amurka kamar...
    Wasu karin majiyoyi sun nuna cewa, wannan hanyar ta hada Maiduguri da wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Borno, wacce ta kasance yankin da yan ta’addan Boko Haram ke yawan kai hare-hare tsawon shekaru.   A baya hanyar, ta kasance a rufe amma Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya bude ta, domin bai wa jama’a damar ci gaba da zirga-zirga a yankin da suka hada da Damboa, Chibok da sauran kananan hukumomi a kudancin Borno tare da taimakon rakiyar sojoji a matsayin kariya.   An kwashe wadanda suka rasun tare da wadanda suka jikkata, wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa.  Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba.   Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a  tsakanin bangarorin biyu. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X  a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu...
    Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun. Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500. Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun...
    Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren  kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
    Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai  hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma  da ke lardin  Al-Bayda a jiya Asabar . Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin...
    Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna. An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa. Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu...
    Yin garkuwa da mutane domin don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Jihar Katsina har ta kai ga ana shiga cikin manyan birane ana daukar manyan mutane ko makusantansu. Daga manyan sojoji zuwa sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da attajirai da ma dalibai, babu wanda ya tsira daga wannan matsalar ta’addanci. Gwarzon gasar Al-Kur’ani A yayin da ake shirye-shiryen daukar azumin watan Ramadana ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da Gwarzon Gasar Al-Kur’ani na Kasa da aka kammala a Jihar Kebbi, Abdulsalami Rabi’u Fasakari a hanyarsa ta komawa gida tare da ’yan uwansa bayan Gawmna Dikko Radda ya karbi bakuncinsa tare da karrama shi. Sai bayan makonni biyu, a yayin da ake gab da daukar...
    Wata mata mai suna Jennifer Castro ta shigar da ƙarar kamfanin jiragen sama na GOL da wata fasinja a kotu bisa wani faifan bidiyo aka wallafa da yake nuna matar ta ki barin kujerarta da ke kusa da taga saboda wani yaro da yake kuka. Matar ’yar ƙasar Brazil da ta ƙi barin kujerar kusa da taga saboda wani yaro mai kuka ta shigar da ƙara a kotu. Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Jennifer Castro, mai shekara 29 na daukar matakin shari’a a kan kamfanin jiragin sama na GOl da kuma fasinjar da ta ɗauki bidiyonta a lokacin da lamarin ya faru. Lamarin wanda aka yi ta...
    Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
    Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci  da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi. Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya. Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran. Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba...
     Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International”  ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan da har yanzu bai zo karshe ba. Wani sashe na rahoton kungiyar ya yi ishara da yadda wannan rundunar da take fada da sojojin kasar Sudan ta tarwatsa mutane daga gidaje da matsugunansu a fadin kasar. Ita kuwa Hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ( UNHCR) cewa ta yi da akwai yan kasar ta Sudan fiye da 100,000 da suke neman yin...
    Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.  Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa  lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance  wajen asibiti. Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza. Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.  Bugu da kari kungiyar...
    Sharhin zai yi dubi ne game da tattaunawar da aka fara gudanarwa zagaye na na farko tsakanin Iran da Amurka a birnin Mascut fadar mulkin kasar Oman, inda gwamnatin kasar Oman din take shiga tsakani a wannan tattaunawa wadda aka fara gudanarwa. Tun da safiyar Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa  Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi,...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
    Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata. Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar. Yadda Tashar...
    A kowane wasa, tauraron Super Eagles Iwobi na nuna cewa ba wai kawai tarihi yake son kafawa a Duniya ba, ya na sake rubuta labarin ‘yan wasan kwallon kafar Nijeriya a Turai, shan kayen da Liverpool ta yi a Craben Cottage ya jinkirta damarta na lashe gasar Firimiya Lig ta bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza. Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya. A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan. An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan...
    Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya. Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa...
    A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a  domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar. Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas. Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG. Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar. A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka...
    Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
    Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16. ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci. Ya ce, “An sanar da shugabannin...
    Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar. Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano The lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups. Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa...
    An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi. Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna. A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin...
      A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje “Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza ayyukan ’yan bindigar da ke addabar garuruwa da ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan. Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin...
    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki. Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta. A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa. “Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar  sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar masauki ga malamai da sauran ma’aikata da ba malamai ba. Farfesa Chamo, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ilimi, Malam Abdullahi Hudu, ya wakilta, ya ce taron ya na da nufin tattauna shirin dawowa  makarantu bayan hutun da aka yi a jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya bangaren ilimi a sahun gaba saboda muhimmancinsa ga ci gaban jihar. Kwamishinan ya nuna...
    Kafar watsa labaru ta ” Axio ta Amurka ta watsa wani rahoto da yake nuni da cewa, an sami rashin yarda da juna a tsakanin masu zuba hannun jari na kasa da kasa da kuma Amurka. Kafar watsa labaran ta buga a shafinta na “Internet” cewa; Rashin tabbaci da yake faruwa a halin yanzu a cikin kasuwanni  yana  tsoratar da masu zuba hannun jari a duniya. Rahoton ya kuma ambaci girgizar da Dalar Amurka take yi, da kuma muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka. Kafar watsa labarun ta ce, a baya muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka, wadanda kuma su ne ke bai wa Dalar Amurka kariya, sun kasance masu...
    Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa  Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.  Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai  mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa...
    Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki. Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su. Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur. Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.
    Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a, ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan unguwar Shaja’iyya inda suka kashe Falasdinawa da dama. Ya zuwa yanzu tun fara yakin tufanul Aksa, a cikin watan Octoban shekara ta 2023, falasdinawa kimani 51,000 sannan wasu 115,688 a gaza. Ta kuma rusa kimani kasha 90% na gine-ginen Gaza.
    Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...
    Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da  gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa. Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata. “Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar...
    Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji. Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu. Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka. Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum. Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar. A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su? “Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro...
    A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40. Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin sun hada da; samar da ingantaccen Irin Shinkafa da kuma habaka yadda ake samar da Irin na Shinkafar. Sauran sun hada da mayar da hankali wajen yin girbin mai kyau, samar da nau’ikan Shinkafar da ke jurewa kowacce irin cutar da ke lalata Irin Shinkafar da aka shuka, aka ajiye a cibiyar gudanar da bincike kan amfanin gona (NCRI) da ke yankin Badeggi a Jihar...
    Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko  su hana gaba daya. Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke...
    Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.
    ’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa. Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku. Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar...
    Hanyoyi Biyar Da Mai Kiwon Kajin Gidan Gona Zai Kare Kajinsa Daga Tsananin Zafin Rana. 1- A Tabbatar An Sama Musu Wadacciyar Iska A Dakin Kwanansu: Ana bukatar mai kiwon kajin ya tabbatar ya sama musu wadatacciyar iska a dakin kwanansu, ana kuma bukatar a yi wa shigifar dakinsu fenti yadda za ta rika rage zafin ranar da kuma samar da kayan koyon da za su sanyaya dakin kwanansu. Haka kuma, ana bukatar a rika sanya musu na’urar da ke sanyaya daki, wadanda za su rika rage zafin ranar, akalla na’urar ta kasance mai ma’unin yanayi daga 5 zuwa 10°C. 2- Sanya Na’urar Sanya Daki: Domin samun saukin yanayin zafin rana, ana bukatar mai kiwo ya sanya musu na’ura a...
    Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000. Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya. Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma...
    Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan.   Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, tana gudanar da bincike kan wani dukan kawo wuƙa da wasu matasa suka yi wa waɗansu mutane su biyu da ake zargi da satar kare a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi. Dukan da ya yi sanadin rasa ran ɗaya daga cikinsu mai suna Peter. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata kan wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato An saki fasto an kuma tsare...
      Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji Kamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya. “A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan. “Yau kuma na kai ziyarar...
    Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida. Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023. Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki. Duk da yawan kudin basukan da ke kan...
    Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace.  Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan. Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin. Sai dai a baya, Danjuma Auta,...
    Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya.   Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa...
    Ya ce shan giya yana barazana ga lafiyar jama’a tare da haddasa matsalolin zamantakewa. A cewarsa, hana yaɗuwar giya zai rage aikata laifuka da kuma inganta zaman lafiya. Dr. Yahuza ya kuma buƙaci al’umma da su mara wa Hisbah baya ta hanyar bayar da rahoto kan duk wani abu da ke saɓa wa doka. Ya tabbatar da cewa hukumar ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki don tabbatar da adalci, zaman lafiya da gyara halayyar al’umma a Jihar Yobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata.   Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance...
    ’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi “An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba,...
    Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar. Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya a ranar Juma’a. Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi Sai dai kwamishinan bai yi ƙarin bayani kan adadin mace-macen da aka samu tun watan Fabrairu da aka fara samun ɓullar cutar ba. Ya ce har yanzu mutane 16 na ci gaba da karɓar magani...
    Kungiyar Afica city of Refugee ta gabatar da taron bukatar da kuma muhimmancin samun zaman lafiya a tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Saka wanda ya ke karkashin jagorancin gundumar ci gaba ta Karshi da Uke,Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa saboda a tattaunakan lamarin daya shafi zaman lafiya tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma. Mutane da dama ne suka samu halartar taron wanda aka yi a Saka a makarantar Sakandare ta Saka daga cikin Shugaban kungiyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na Karamar HUkumar Karu Reberend Timothy. Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital Reberend Justin darekta wanda kuma shi...