2025-02-22@22:04:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 486
«Yankuna»:
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa...
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu...
Da farko za ku zuba Fulawa a wata roba haka sannan ku kawo Baikin Fauda ko Yis duk dai wanda za ku yi amfani da shi ku zuba, sai ku zuba madara sannan sai Gishiri kadan haka sai Qwai shima ku fasa a ciki, amma kada ya yi ruwa ko kauri kwabin. Sannan sai ku...
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin...
Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an...
Bishop na Cocin Katolika da ke Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja. A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata...
Shan ruwa hanya ce mafi sauwi wajen magance kumburin ido domin, ruwa yana wanke dauda a Ido. A samu cokulan karfe kamar biyar zuwa shida a saka a firiji na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a cire su, sai a rika shafawa a kumburin Ido har sai ido ya sabe. Ganyen shayi yana magance...
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun. Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas. NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Ya je...
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu...
Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin....
Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na...
Bayan bincike ta hanyar fasaha, an gano inda wayarta take, wanda hakan ya kai ga kama Abdulrahman Bello. Lokacin da aka kama shi, ya amince da laifin kisan Hafsoh da nufin yin sihirin kudi (oshole/ajoo owo). A binciken da aka yi a gidansa, an samu: Wayoyi biyu da takalmin mamaciyar Hannaye da aka sare daga...
Har ila yau a jiya Asabar, Wang Yi ya kuma gana da jami’an kasahen Brazil, da Czech, gami da Austria. (Bello Wang)
Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa idan ba tare da cikakken tantance kudi ba, babban bankin ba zai iya bude sabbin asusu ga kananan hukumomin ba.
Bugu da kari, Tinubu ya amince da rashin shinge a sabuwar harabar jami’ar ne ya kawo wannan takaddamar, inda nan take ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta ware kudade domin gudanar da aikin kafa katafaren shinge a tsakanin kauyen da Jami’ar. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na inganta ababen more rayuwa na jami’o’i a...
Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi. Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta. Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace...
“A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.” PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton...
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya buƙaci Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas (NEDC) da ma’aikatar raya yankuna ta tarayya da su magance talauci a yankin ta hanyar zuba jari a fannin ilimi. Shettima ya yi wannan kiran ne a yayin wata ganawa da ya yi da mahukuntan hukumar ta NEDC a fadar shugaban kasa da...
Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen. Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin...

Trump Ya Bukaci Ukirain Ta Bada Ma’adinanta Ga Kasar Amurka Idan Tana Son Ta Taimaka Mata Da Kayakin Yaki
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake...
Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin...
Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi...
Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke...
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta. Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu...
An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU. An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar. Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49. Dan...
Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan...
A nasa jawabin, Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa kisan da aka yi wa wani malamin addini lamari ne mai ban tausayi, amma babu wata kwakkwarar shaida da ke alakanta lamarin da wata kungiya, addini ko kabilanci. Ya tuna irin abubuwan da suka faru a baya inda daga baya aka gano wadanda suka aikata...
Sauran su ne tsohon dan majalisar wakilai Hon. Godfrey Ali Gaiya da ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Jaba a majalisar dokokin jihar Hon. Henry Marah Zakarieh da sauransu. Gwamna Uba Sani ya godewa shugabannin jam’iyya a jihar bisa kokarin da suke na jawo mutane zuwa jam’iyyar sannan ya sake jaddada aniyar Gwamnatinsa na ci...
A yau Asabar ne aka bude taron shugabannin kasashe da gwamnatocin AU a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa na Habasha. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Ministan Tattalin Arziki Na Kasar Iran Ya Kama Hanyar Kasar Saudiya Don Halattar Taron Tattalin Arziki
Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji na 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a...
Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin...
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin da ya afku a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a ranar Juma’a nan da ta gabata. A cewar hukumar FRSC, hatsarin ya rutsa da wata...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta...
Amincewa da Karin kudin dai ya zo ne domin cike gibin da aka samu, bayan da Amurka ta yanke kudaden taimakon da take bayarwa a fagen kiwon lafiya. A shekarar 2023 Kasar Najeriya mai mutane fiye da miliyan 200 tana cikin 10 na farko da su ka fi karbar tallafin hukumar Amurka na raya kasashe...
Kakakin dakarun rundunar “Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa za su saki fursunoni 3 na “Isra’ilawa” a wannan rana ta Asabar. A jiya Juma’a ne dai kakakin na dakarun rundunar “ Kassam” ya fitar da sanarwar cewa za saki fursunoni uku da suke rike da su da su ne: Shasha Alexander,Sagi Dikel Hen,Yaei Horun...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama. A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar...
Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma. Gwamnan a wajen bikin mika ragamar...
Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban,...
Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin...
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin. Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar...
Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar...

Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan...