2025-02-01@22:59:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 104
«Farashin man fetur»:
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya...
A yau Asabar, bayanai a hukumance sun nuna cewa, fiye da fasinjoji tsakanin yankuna miliyan 304 ne suka yi zirga-zirga a fadin kasar Sin a ranar Juma’a, rana ta hudu ta hutun bikin bazarar bana, yayin da aka samu yawan ziyarce-ziyarcen iyalai wanda ya ingiza yawon shakatawa. Wannan dai shi ne karo na farko na...
Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa...
Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar.
An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf...
Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar. Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa,...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmaki kan birnin Tulkarm da sansaninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shiga rana ta shida suna kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkarm da sansaninsa, inda yanayin tsoro da tarwatsa gine-gine suka lullube mazaunan yankunan, adaidai lokacin...
Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan...
Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta jaddada ƙudirorinta na tabbatar da tsaro a kan tituna da kare rayukan al’umma ta hanyar aiwatar da dokokin zirga-zirga. Saboda haka, tana buƙatar haɗin kan al’umma wajen ganin an cimma wannan buri.
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu. A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya...
Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar...
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu....
A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen...
’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum...
Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga...
“Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai...
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan...
An yi kokarin cire Damagum ta hanyoyin siyasa, ciki har da yiwuwar nada sabon shugaba daga yankin arewa ta tsakiya, amma hakan ya ci tura. Gwagwarmayar bangaranci dai ta kara dagula al’amuran cikin gida na jam’iyyar, inda aka samu bangaren masu biyayya ga fitattun mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ministan...
Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa...
Karamar Hukumar Birnin kudu ta jihar Jigawa ta bada tabbacin hada kai da duk wata hukuma ko kamfani dake da muradin cigaban yankin. Shugaban karamar hukumar, Dr. Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin lokacin da wakilan rukunin kamfanonin kasar Sin wato China suka ziyarce shi a ofishinsa. Yace karamar hukumar Birnin kudu tana sahun...
Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara...
Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata...
Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje
Masarautar Zazzau, ta sanar da rasuwar Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro. Marigayin, ya rasu ne a Asibitin Gambo Sawaba lokacin da ya halarci taro a asibitin. Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok Meta zai biya Trump $25m kan...
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi...
Masu ɗibar man fetur daga wata tankar mai da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara da ke hana su farmaki. Bayan faduwar tankar a cikin dare man cikinta ya fara tsiyaya, inda motar ta kama da wuta a kan babbar hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a ranar Laraba. Faɗuwar motar ke da wuya wasu...
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a...
Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa...
An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce,...
Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara
Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air...
Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta Kaddamar da shirin bada horo da fadakarwa ga maniyatan bana Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa an gabatar da wannan bitar ko horon ne a cibiyar hukumar alhazai ta jihar Kaduna da ke unguwar Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Garin Zaria. Shugaban hukumar na...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a...
Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a...
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin...
A ɗaya bangaren, sojoji sun tabbatar da cewa suna ci gaba da neman Bello Turji, wanda ke jagorantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin. Turji ya tsere daga maɓoyarsa, amma jami’an tsaro sun ce ba za su daina nemansa ba har sai an kama shi. Sojojin sun tabbatar da cewa suna ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya...
CMG Ya Gabatar Da Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara Cikin Nasara