2025-04-03@12:49:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 30
«Syria»:
Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums, Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din...
Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar...

Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin Al’ummar Kasar A Cikin Sha’anin Kasar
Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati. A jiya Laraba...
Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu...
Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
Shugaban na kurdawa a Syira Hikmat al-Hijri ya soki halayyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar Syria, tare da nuna kin amincewa da sabon tsarin mulkin kasar da aka sanar kwanaki kadan da su ka gabata. Hikmata al-Hijri ya yi kira da gyara yadda ake tafiya a yanzu da kuma rubuta sabon tsarin mulki wanda zai...
A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya a kasar, da su kare “dukkan ‘yan Syria ba tare da nuna bambanci ba,” ba tare da la’akari da kabila, addini ba. Majalisar ta yi...
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar gwamnatin kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna...
Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba. Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan...
Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da...

Syria: Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai Suna Ci Gaba Da Kai Wa Kauyukan Lazikiyya Da Tartus Hare-hare
Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shirye daga Lebanon ta ambaci cewa; Wasu kauyuka na mabiya mazhabar Alawiyya dake Tartus, da kuma Lazikiyya, sun fuskanci hare-hare daga masu dauke da makamai. A yau Lahadi, masu dauke da makaman sun kutsa cikin wasu kauyukan Ramilah, Naq’a dake kusa da Jabalah. Daga jiya zuwa yau masu dauke...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma...
Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa gomman mutane ne sukayi shahada a sabon rikicin da ya barke a baya baya nan a wasu sassan kasar. Majiyoyin cikin gida na kasar sun tabbatarwa da tashar Al-Mayadeen cewa, a safiyar Asabar an yi ta kashe-kashe a kauyuka da garuruwa da dama a yankunan karkarar Latakia, Tartous...
Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar...
Gwamnatin Syria ta ayyana dokar ta-baci a yankuna da dama na kasar bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke kara murkushe fararen hula. An sanya dokar ta-baci a birnin Tartus da ke arewa maso yammacin kasar da kuma daukacin lardin Homs a daren Alhamis. An kuma sanar da dokar...
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa...
Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma...
Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojoji a shirye suke su shiga cikin rikicin da ya barke a garin Jarmana dake kusa da birnin Damascuss na kasar Syria domin kare ‘yan Duruz. Ofishin Fira ministan HKI Benjemine Netanyahi ya fitar da sanarwa a jiya Asabar da marece, yana ce; Netanyahu da ministansa na...
A farko-farkon da masu dauke da makamai su ka kwace iko da birnin Halab, jami’an gwganatin Turkiya sun kaucewa yin Magana akan abinda yake faruwa. Sa dai kuma da yake mai kaza a aljihu ba ya jimirin cas, ba a je ko’ina ba, su ka fara furta kalaman da suke nuni da cewa, Da kawai...
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen Damascus babban birnin kasar da kuma lardin Deraa da ke kudancin kasar. Hare-haren dai ya biyo bayan kiran da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na karbe yankin kudancin Siriya...
Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin. A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula...

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya...
Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun yi musayar sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye. Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece...
Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki. A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir...
Rahotanni da suke fitowa daga kasar Syria sun ce, ana ci gaba da yi wa daidaikun mutane kisan gilla a sassan kasar mabanbanta. A kusa da garin Hamah, an kashe mutane 7 a bayana nan, bayan da wasu masu dauke da makamai su ka shiga cikin garin Tal-Zahab. Masu dauke da bindigar sun kutsa gidan...
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata...
Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa. Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin...