2025-04-13@19:28:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 47

«NAJERIYA A YAU»:

    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Irin alaƙar da ke tsakanin wasu abokai na da matuƙar kusanci da kyau, ta yadda a wasu lokutan ma ba a iya banbance dangantakar tsakaninsu ta ’yan uwan na jini ko kuma abota. Irin wannan dangantaka ya kamata ne a ce ana samun ta a tsakanin ’yan uwa na jini. Sai dai a yayin da wasu ke samun kyakkyawan dangantaka tsakaninsu da ’yan uwan su na jini, wasu kuwa ba sa ga-maciji da nasu ’yan uwan da suke uwa ɗaya uba ɗaya. NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an ƙirƙire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da ƙabilanci. Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba’in da biyar da fara wannan shiri, jama’a da dama na tambaya —ko har yanzu shirin na da tasirin da aka kirkire shi domin shi? Ko har yanzu bautar ƙasa NYSC na ci gaba da samar da haɗin kai da ake buƙata a Najeriya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta Shirin Najeriya A...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar mutum. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke damun mutane da yawa, ita ce cutar hawan jini. Wannan cuta na kashe aƙalla mutane miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi bayani ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya kai shekara 40 ko sama da haka, zai iya tuna irin tarbiyyar da ya samu daga iyayensa a baya, da kuma yadda alaƙar da ke tsakanin yara da iyaye ta ke cike da girmamawa, kulawa, da soyayya. A yau, abubuwa sun canza sosai. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Yawancin iyaye na fuskantar ƙalubale iri-iri, musamman yadda nauyin rayuwa ke ƙaruwa a kansu. Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu shi ne yawaitar mata masu aiki, ko dai a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu. Wannan sauyin yana iya shafar irin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah? Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum. Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Wasu daga cikin matasan sun kammala karatu, wasu kuma suna da sana’o’in hannu, amma duk da haka, rashin samun aikin da zai biya musu buƙatunsu yana ƙara jefa su cikin mawuyacin hali. Wannan matsala na ci gaba da haddasa damuwa ga matasan ƙasar, inda da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam. A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai. Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu, yayin da wasu kuma ke haɓaka. Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma haɓaka a wasu sa’anni. NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyan sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari. Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi. Domin sauke...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mallakar Muhalli na ɗaya daga cikin burin kowanne ɗan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Ƙananan ma’aikata da mafi ƙarancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar da su, ko tufatar da su ba, ballantana har su yi tunanin mallakar muhalli nasu na ƙashin kansu. Sai dai masana na bayyana cewa marasa karfin ma na iya mallakan nasu muhallin daidai ruwa daidai tsaki. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da mai ƙaramin ƙarfi zai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kukan rashin aikin yi da a ko da yaushe ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, waɗanda za su cike guraben ayyukan ne suka yi ƙaranci a Najeriya. Alƙaluma na ci gaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun ƙasar a kowace shekara. A yayin da da yawa ba sa samun aikin yi, sau tari akwai ɗimbin guraben ayyuka da babu masu cike su don babu ƙwararrun da ake buƙata. NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Shirin Najeriya A Yau...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar ƙasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki waɗanda suke takun saƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke ƙullawa Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP. NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi DAGA LARABA:...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai  har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai  ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kuɗin da ake kashewa. An saba  a watan Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buɗa-baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe maƙudan kuɗaɗe ba. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al’ummar Musulmi na yin azumi ne bisa dalilan addini kamar yadda Allah Ya yi umarni don samun lada. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka haɗa da inganta ƙarfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki ba ya bukata. A taƙaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwarsa. NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan Adam, musamman mai azumi. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya. Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke. Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci gaba da kokawa kan yadda har yanzu ba su gani a ƙasa ba. Tun makonni biyu da suka gabata aka sanar da saukar farashin fulawar kamar sauran kayayyakin masarufi. To amma ba kamar sauran kayan abinci ba, har yanzu ba a ga sauyi a farashin burodi ba. NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne  ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata. Sai dai wannan sanarwa na ci gaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati. NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba. Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin. Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware. NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta. A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”. Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma. Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsakanin Hausawa  akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko mene ne alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Albarkacin Ranar Yaƙi da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya  A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutanen da ke da sha’awar shiga harkar noma don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kuɗaɗen shiga na fuskantar ƙalubale. Wannan ƙalubale ya haɗa da ƙarancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hanyoyin noma ba tare da kashe kuɗi masu yawa ba. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban. Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu. NAJERIYA A YAU: Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa? DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya yi nazari ne kan dalilan da Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aurar da ’yan mata da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci. Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata. NAJERIYA A YAU: Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akan ce ‘Noma tushen arziƙi’ kuma mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya ƙoshi babban arziƙi ne. Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwanninsu don sama wa kansu abincin da za su ci. Sai dai masana na ganin da waɗannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kuɗaɗen shiga. NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan hanyoyin da ’yan Najeriya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ci-gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da ɓangarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu. NAJERIYA A YAU: Matakan Samar Da Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a? Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ƙalubale da ke tattare da wannan harka, da damar da ake samu idan an rungume ta, da kuma dabarun yin nasara...
۱