2025-04-12@21:50:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3221
«a Jihar Katsina»:
Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata. Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar. Yadda Tashar...
A kowane wasa, tauraron Super Eagles Iwobi na nuna cewa ba wai kawai tarihi yake son kafawa a Duniya ba, ya na sake rubuta labarin ‘yan wasan kwallon kafar Nijeriya a Turai, shan kayen da Liverpool ta yi a Craben Cottage ya jinkirta damarta na lashe gasar Firimiya Lig ta bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza. Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya. A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan. An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan...
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya. Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa...
A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar. Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas. Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG. Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar. A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16. ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci. Ya ce, “An sanar da shugabannin...
Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar. Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano The lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups. Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa...
An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi. Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna. A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin...
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje “Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza ayyukan ’yan bindigar da ke addabar garuruwa da ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan. Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin...
Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki. Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta. A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa. “Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar masauki ga malamai da sauran ma’aikata da ba malamai ba. Farfesa Chamo, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ilimi, Malam Abdullahi Hudu, ya wakilta, ya ce taron ya na da nufin tattauna shirin dawowa makarantu bayan hutun da aka yi a jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya bangaren ilimi a sahun gaba saboda muhimmancinsa ga ci gaban jihar. Kwamishinan ya nuna...
Kafar watsa labaru ta ” Axio ta Amurka ta watsa wani rahoto da yake nuni da cewa, an sami rashin yarda da juna a tsakanin masu zuba hannun jari na kasa da kasa da kuma Amurka. Kafar watsa labaran ta buga a shafinta na “Internet” cewa; Rashin tabbaci da yake faruwa a halin yanzu a cikin kasuwanni yana tsoratar da masu zuba hannun jari a duniya. Rahoton ya kuma ambaci girgizar da Dalar Amurka take yi, da kuma muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka. Kafar watsa labarun ta ce, a baya muhimman takardun da suke a matsayin kaddara a cikin Baitul-malin Amurka, wadanda kuma su ne ke bai wa Dalar Amurka kariya, sun kasance masu...
Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka. Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran. A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya. Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa...
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki. Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya...
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su. Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur. Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan cibiyoyin makamai na HKI wadanda suka Yaffa (tel aviv) saboda daukar fansa kan kashe-kashen da take yi a Gaza. Tashar talabijin Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran YAF na kasar Yemen yana fadar haka a jiya Jumma’a, ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan unguwar Shaja’iyya inda suka kashe Falasdinawa da dama. Ya zuwa yanzu tun fara yakin tufanul Aksa, a cikin watan Octoban shekara ta 2023, falasdinawa kimani 51,000 sannan wasu 115,688 a gaza. Ta kuma rusa kimani kasha 90% na gine-ginen Gaza.
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa. Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata. “Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar...

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji. Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu. Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka. Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum. Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar. A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su? “Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro...
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40. Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin sun hada da; samar da ingantaccen Irin Shinkafa da kuma habaka yadda ake samar da Irin na Shinkafar. Sauran sun hada da mayar da hankali wajen yin girbin mai kyau, samar da nau’ikan Shinkafar da ke jurewa kowacce irin cutar da ke lalata Irin Shinkafar da aka shuka, aka ajiye a cibiyar gudanar da bincike kan amfanin gona (NCRI) da ke yankin Badeggi a Jihar...

Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko su hana gaba daya. Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke...
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa. Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku. Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar...
Hanyoyi Biyar Da Mai Kiwon Kajin Gidan Gona Zai Kare Kajinsa Daga Tsananin Zafin Rana. 1- A Tabbatar An Sama Musu Wadacciyar Iska A Dakin Kwanansu: Ana bukatar mai kiwon kajin ya tabbatar ya sama musu wadatacciyar iska a dakin kwanansu, ana kuma bukatar a yi wa shigifar dakinsu fenti yadda za ta rika rage zafin ranar da kuma samar da kayan koyon da za su sanyaya dakin kwanansu. Haka kuma, ana bukatar a rika sanya musu na’urar da ke sanyaya daki, wadanda za su rika rage zafin ranar, akalla na’urar ta kasance mai ma’unin yanayi daga 5 zuwa 10°C. 2- Sanya Na’urar Sanya Daki: Domin samun saukin yanayin zafin rana, ana bukatar mai kiwo ya sanya musu na’ura a...
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000. Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya. Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma...
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan. Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce, tana gudanar da bincike kan wani dukan kawo wuƙa da wasu matasa suka yi wa waɗansu mutane su biyu da ake zargi da satar kare a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi. Dukan da ya yi sanadin rasa ran ɗaya daga cikinsu mai suna Peter. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata kan wani mutum mai suna Peter a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato An saki fasto an kuma tsare...
Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji Kamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya. “A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan. “Yau kuma na kai ziyarar...
Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida. Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023. Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki. Duk da yawan kudin basukan da ke kan...
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace. Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan. Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin. Sai dai a baya, Danjuma Auta,...
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya. Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa...
Ya ce shan giya yana barazana ga lafiyar jama’a tare da haddasa matsalolin zamantakewa. A cewarsa, hana yaɗuwar giya zai rage aikata laifuka da kuma inganta zaman lafiya. Dr. Yahuza ya kuma buƙaci al’umma da su mara wa Hisbah baya ta hanyar bayar da rahoto kan duk wani abu da ke saɓa wa doka. Ya tabbatar da cewa hukumar ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki don tabbatar da adalci, zaman lafiya da gyara halayyar al’umma a Jihar Yobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata. Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance...
’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin. Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi “An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba,...
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar. Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya a ranar Juma’a. Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi Sai dai kwamishinan bai yi ƙarin bayani kan adadin mace-macen da aka samu tun watan Fabrairu da aka fara samun ɓullar cutar ba. Ya ce har yanzu mutane 16 na ci gaba da karɓar magani...
Kungiyar Afica city of Refugee ta gabatar da taron bukatar da kuma muhimmancin samun zaman lafiya a tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Saka wanda ya ke karkashin jagorancin gundumar ci gaba ta Karshi da Uke,Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa saboda a tattaunakan lamarin daya shafi zaman lafiya tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma. Mutane da dama ne suka samu halartar taron wanda aka yi a Saka a makarantar Sakandare ta Saka daga cikin Shugaban kungiyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na Karamar HUkumar Karu Reberend Timothy. Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital Reberend Justin darekta wanda kuma shi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe. Kazalika, a cikin kowanne wata daya, mai ajiyar zai iya zamaowa a cikin rukunin Zakaru 70, inda kowanne mai ajiya daya a Bankin, zai iya karbar Naira 100,000. Har ila yau, a cikin watanni uku kuma, kowanne mai ajiya daya a Bankin na Stanbic IBTC, da ya fito daga yanki bakwai da ake yin kasuwanci, zai lashe Naira miliyan daya, inda kuma a zagayen gasar na karashe...
’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa. Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan. Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja Duk da kiran...
Ina yi wa daujacin jama’ar musulmai na wannan gari, kasa, da ma duniya baki daya barka da sallah a ciki kuwa zan gaishe da Mamana da Babana , sannan Sadiya Rimi, Islam, Nawwara, Khairat, Rahma Abdullahi, Faddima, Mufida, Huda, Labiba, Shamsiyya Adam da fatan sun yi juma’a lafiya kuma sun yi sallah lafiya. Sako daga Jamilu Usman Jihar Zamfara: Ina gaida Matata kuma uwargidana Nana Amina da Amarya ta Halimatussadiya da ‘ya’yan Usman, Zahrah, Nana, Jidda, Hanan, Amirah, Hamza, Alida sun yi juma’a lafiya. Sako daga Wasila Muhammad Jihar Jigawa karamar Hukumar Gumel: Ina gaishe da Mahaifiyata da Mahaifina na, da kawayena Fiddausi Sa’id Danjuma, Shahida, Walida, Zeenat, Baturiyya, Lawisa da fatan sun yi sallar juma’a lafiya. Daga kanmu,...
Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan. Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC. Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.” “Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.” A ranar Litinin shugaban Amurka Donald...
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin, kamar yadda wasu majiyoyi hudu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Alhamis. Wakilan tawagogin biyu sun tabbatar da kasancewarsu a babban birnin kasar Qatar, kuma sun ce za a yi ganawar ido-da-ido a ranar Laraba, amma har yanzu suna tattaunawa kan tsarin tattaunawar. Dukkanin majiyoyi – jami’an gwamnati biyu da wakilan ‘yan tawaye – sun bukaci a sakaya sunansu saboda masu...
Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30. Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu. Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba. Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba. Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da...
Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon. A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon wani muhimmin al’amari ne na kasa da ya zama wajibi a sanya shi cikin ajandar gwamnatin Lebanon. Ya kara da cewa: Al’ummar kasar Labanon suna fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile wannan ta’addanci. Fadlallah dai ya dauki babbar matsalar...

Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu. Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi. Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar...
Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka. Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu. Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku. Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa. Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin. Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa...

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
-Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban. Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba. Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade...
Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta. An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba. Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar. Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar. Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa. Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin. Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki. Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda. Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi. Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin wani kaddara daga Allah Ta’ala. Shugaban karamar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya wakilce shi, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki ganin yadda ba a yi asarar rayuka ba....
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar. Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar. Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai hanyoyin arzuka iri daban daban cikin wannan Kasa, wadanda ma suka kere fetur sau ninkin ba ninki wajen bunkasar sha’anin tattalin arziki, musamnan sabgar noma, wadda wasu Shekaru can baya, ita ce kashin bayan tattalin arzikin wannan Kasa. Kuma, tun daga wancan lokaci zuwa yau din, harkar noma ce kan gaban fetur, wajen samawa dubban jama’ar Kasa aiyukan-yi. Yankin arewacin wannan Kasa ta Nijeriya, na...
An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu da kuma Muhammad Yahaya da sunan zai yi musu aiki a sako su daga gidan yari. Lauyar masu gabatar da ƙara, Barista Sadiya Sabo, ta tuhumi mutumin da laifin damfara da kuma cin amanar da aka ba shi. Wanda ake tuhuma ya amsa laifin, amma ya bayyana cewa ba shi kaɗai ya aikata wannan haramtaccen aiki ba. ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar...
Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa. Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin. Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI. A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu...
Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su. NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita. Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na...
Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a. Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan doka, amma wasu majiyoyin sun ambaci cewa a cikin kwanakin bayan nan an sami rikice-rikice a yankin. Wasu majiyoyin sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai sun yi harbe-harbe a yankin wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane biyu a garin Basras-sham.
Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL da ta kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Masalit da sauran al’ummu a cikin tsawon shekaru biyu na yakin basasar kasar. Ministan shari’a na kasar Sudan Muawia Usman ya bayyana cewa: Kisan kiyashin da dakarun kai daukin gaggawa su ka yi wa al’ummar Masalit da su ka kunshi larabawan yankin Darfur, ya faru ne ta hanyar taimakon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.” Bayan...
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani dan bangere na mutanen da ke yin cacar ne kawai, ke samun a cacar, inda akasarin sauran, ke tabka asarar kudadensu da suka zuba a cikin cacar. An dai jima ana yin caca a kasar, wadda a shekarun baya, ake yi mata wani kallon kan abinda bai dace ba, kamar dai yadda Coci ta alakanta ta, a matsayin hanyar yin arzikin dare daya Idan za...
Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na...
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa. Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar. Ya koka da...
Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan suka fara dandana kudarsu, inda aka fara ganin koma bayan kasuwannin hannayen jari, da gurguncewar sana’o’i sakamakon rashin tabbas da kasar ke fuskanta, yayin da kasar ke tunkarar matsanancin yanayi na komadar tattalin arziki. Wata manuniya da ka iya haskaka abun da ka iya wakana ga Amurka a wannan karo ita ce irin yadda Amurka ta sha fama da kalubalen hauhawar farashi, da koma...
Yau Alhamis ranar 10 ga wata, an fara “Ranar Sinanci ta MDD” ta shekarar 2025, wato bikin nuna fina-finan Sinanci na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG karo na 5 a hukumance. An kaddamar da bikin bisa hadin gwiwar CMG da kungiyar wakilan kasar Sin na MDD dake birnin Geneva da na sauran kungiyoyin kasa da kasa, da ofishin MDD dake birnin Geneva. Daga cikin shirye-shiryen bikin mai taken “Ziyara A kasar Sin” wato “China Travel” a Turance, an gayyaci jama’ar kasashen duniya da su tsara bidiyo game da ziyararsu a kasar Sin, inda suka nuna kyawawan al’adu da zamantakewar al’umma na kasar Sin, da kuma yanayin bunkasuwar kasa, domin samar wa al’ummomin...
Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar. Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar. Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka. Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya. A cewarsa, an...
Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato ta fara biyan sabon albashin tun a watan Janairu ga dukkanin ma’aikatan jihar, ciki har da na ƙananan hukumomi. Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ya ce: “Sakkwato ce jiha ta farko da ta fara biyan sabon albashi na dubu 70, kuma ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi na amfana da shi. “Maganar shugaban...
Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin hana fasa korin muggan kwayoyi da kuma sulalewar yan ta’adda suka kan iyakokin kasashen biyu. Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta. Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a dai dai lokacinda gwamnatin Amurka ta dorawa kayakin kasar China masu shigowa Amurka kudin fito na kasha 125%. Tun zagaye na farko na shugabancinsa ne shugaban ya fara rigima da kamfanin Tiktok na kasar China wanda ya sami karbuwa a cikin Amurka da kuma kasashen duniya da dama. Amurka tana ganin shafin yanar gizo na tiktok barzane ce ga tsaron kasar Amurka. Kuma har ta...
Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI. Amma sojojin sun kammala da cewa a...
Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan da gwamnatin shugaba Trump ta kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama wadanda suka hada da China da kuma kasashen turai EU. Labarin ya kara da cewa karin kudaden fiton sun shafi motoci da karfe da kuma karfen alminium ne da suke shigo da su daga kasar ta Amurka ne. Banda haka karin kudaden fiton sun shafi kayakin abinci wadanda suka hada da waken...
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu. Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma...
Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi. Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin daliban firamare ba su iya karatu ko rubutu yadda ya kamata. Ya bayyana cewa, an dauki malamai sama da 7,000 a karkashin gwamnatinsa domin karfafa ilimin boko, ya kuma ce jihar ta bullo da sabbin dabaru da suka shafi al’umma, kamar taron iyaye mata da kuma farfado da kwamitocin gudanarwa na makarantu (SBMC), domin inganta zuwan yara makarantu da kuma lura da yadda malamai...
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp