2025-02-22@15:38:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 958
«kisan Dele Giwa»:
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da...
Kungiyar masu fama da cutar daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bullo da tallafin kula da cutar a dukkan asibitocin gwamnati. Shugaban kungiyar Salisu Yusuf ne ya yi wannan kira a yayin wani taron manema labarai na bikin ranar cutar Daji ta duniya tta shekarar 025. Ya...
Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya. A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyar jihar domin gudanar da bincike. A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mikawa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi,...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce...
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar...
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025. Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu da cewa suna yi ne kawai domin neman mulki. Uba Sani ya bayyana cewa ’yan siyasar da ke yawan sukan Tinubu a baya-bayan nan ba su da wani abin da za magance matsalolin Najeriyar da suke suka shugaban kasan...
Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata. A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a...
Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya. Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar. Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 Dalilin da...
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa. ...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF. Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa. A cewarsa, gwamnatin...
An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa tare da...
Daminar Bana: NiMet Ta Yi Hasashen Jinkirin Saukar Ruwan Sama A Jihohin Arewa
Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana. A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da fara shawarwarin tsagaita wuta a mataki na biyu tsakaninta da Isra’ila. Kakakin Abdul Latif al-Qanou ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar zamani. A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Labanon ta shigar da sabon korafi kan yahudawan sahyuniya gaban kwamitin sulhu na MDD, inda ta yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahyuniya suka kai kan kasar Labanon, da kuma keta hurimun ikon kasar, da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma yau fiye da watanni biyu....
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa...
Da yake tabbatar da harin, wani mazaunin T/wada Garmadi, Rumaya Kwassam, Mista Joel Ahada, ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin mutunta hakkin dan Adam da kare lafiyar mazauna karkara. Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan,...
Wasu ma’aurata ’yan kasar Australia da suka yi aure kuma suka sake rabuwa da juna har sau 12 a cikin shekaru 43 da suka gabata, a yanzu ana gudanar da bincike a kan zargin zamba tsakaninsu. ’Yan sanda a birnin Vienna na kasar Australia a halin yanzu suna gudanar da bincike a kan wani lamari...
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata. Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala...
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu da cewa suna yi ne kawai domin neman mulki. Uba Sani ya bayyana cewa ’yan siyasar da ke yawan sukan Tinubu a baya-bayan nan ba su da wani abin da za magance matsalolin Najeriyar da suke suka shugaban kasan...
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsohon uban gidansa kuma magabacinsa Malam Nasir El-Rufai. Uba sani ya ce babu kamshin gaskiya a maganganun da ke yawa cewa shi da tsohon gwamnan El-Rufai suna zaman doya da manja. Ya bayyana haka ne a yayin hirar da kafar tala bijin...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an kashe sojoji 2 a yankin kusa da Tubas dake Arewacin yammacin kogin Jordan. Kafafen watsa labarun sun kuma ce, maharin ya isa wani shinge na soja dake kusa da Tayasir, ya kuma boye a cikin hasumiyar da masu tsaro ke zama a ciki, sannan ya bude wa...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara...
Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu. Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai...
Gwamnan Kaduna Ɗan Amshin Shata Ne Ga Tinubu Saboda Tallafin ₦150bn — El-Rufai

Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta kammala ɗaukar tsohon ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Asensio wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2023 ya na ɗaya daga matasan ƴan wasa da tauraruwarsu ke haskawa a harkar ƙwallon ƙafa...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita. Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutanen da ke da sha’awar shiga harkar noma don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kuɗaɗen shiga na fuskantar ƙalubale. Wannan ƙalubale ya haɗa da ƙarancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. NAJERIYA A YAU:...
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...
Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie. Mai gari...
A yayin da rikici ya kaure cikin dare tsakanin jami’an tsaro da masu gine-gine a unguwar Rimin Zakara, mutane sun cinna wa gidan mai garin wuta. Da farko dai an samu rikici tsakanin mahukunta da mutanen yankin, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane huɗu tare da ƙone gidan mai unguwar. NCDC ta tsaurara matakan...
Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar. Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda...
A yayin da aka bude wasannin lokacin sanyin na Asiya karo na 9 a birnin Harbin na arewacin kasar Sin a ranar Litinin ta hanyar gabatar da tseren kunna fitila, mai dauke da fitilar, kuma mamban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC), Yu Zaiqing, ya bayyana cewa, gasar za ta sa kaimi ga...
Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Bayyana Cewa: Makamai Masu Linzaminsu Zasu Kai Duk Inda Makiya Suke
Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa: Tana Goyi Bayan Duk Wata Gwamnati Da Ke Samun Goyon Bayan Al’ummar Siriya
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Kasashen Iran Da Iraki Zasu Kare Kungiyoyin Gwagwarmaya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf...
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan...
Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna...
“An zargi Asibitin da yin aiki ba tare da rajista ba da kuma yin ayyukan likitanci a cikin wani gidan haya da ake ganin bai dace da ayyukan kiwon lafiya ba. “Bincike na farko ya nuna cewa, wani dattijo kuma shugaban Al’umma ya rasu sakamakon tiyata da aka yi masa a Asibitin, yayin da...
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa...
Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a...
Wani mahayin keken hawa, Samuel Fastuma, ɗan asalin Jihar Benue, ya kammala balaguronsa a kan keken hawa daga Legas zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a cikin kwanaki 8 kacal. A cewar Fastuma, ya fara wannan tafiya ce a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, 2025 bisa ƙudirinsa na nuna fatan alheri ga daukacin...
A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar...