2025-04-16@02:46:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 815

«Murja Ibrahim Kunya»:

    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da...
    Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese) Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Fichajes...
    Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a.   Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano...
    Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni.   Ban...
    Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna. Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga. Mutanen da suka saba...
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da...
    Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah...
    Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin.   Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin...
    Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa...
    Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan...
    Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kaka da kakanni an san Hausawa  da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba...
    Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar...
    Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar...
    Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan...
    Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin...
    A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi...
    A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar...
    Aƙalla mutane biya ne suka mutu, 19 suka yi munanan raunuka a dalilin hatsarin mota da ya rutsa da su a Kasuwar Damagum da ke kan babbar hanyar Kano-Maidugri a Jihar Yobe. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi. Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar Gobara ta...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin...
    A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine...
    Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na...
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta...
    Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa...
    Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari...
    Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 —...
    Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji tare da rasa mayaƙansu da dama. Rahotanni na cewa harin ya auke ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ’yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Nijeriya...
    Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba. Wannan dai na zuwa...
    Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata,  da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan.   Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi...
    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta...
    Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024. Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana...
    Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo,...
    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a...