2025-02-21@14:49:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 231

«Injiniya Mustafa Balarabe Shehu»:

    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a...
    Kasuwannin hatsi a Jihar Neja suna fama da matsalar faduwar farashi amfanin gona, sakamakon shigo da hatsi daga kasashen makwabta kamar Chadi da Ghana da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso. Wannan yanayi ya haifar da yawan kaya, wanda ke shafar manoma da ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki a yankin. Ya yi wa kansa...
    Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 20 yana zukar taba sosai a lokacin da ya yanke shawarar ci gaba da zuka sosai. Jarabar son kowane irin abu ba shi da kyau, kuma zukar taba tana cikin mafi muni. Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin...
    A daren ranar 6 ga wannan wata, an gudanar da wani biki mai taken “Bikin Bazara Namu” a cibiyar hukumar bunksa ilmi da kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda babban rukunin Sin dake hukumar, da gidan talabijin na lardin Henan na kasar Sin suka karbi...
    Madara muhimmin abinci ne da ake bukata domin samun sinadarai masu ginawa da ƙara ƙarfi da lafiyar jiki. Bincike ya nuna cewa mutane biliyan shida ne ke shan madara a duniya, wanda ya sa shan madarar saniya da kiwon dabbobi ya zama wani vangare na rayuwar ɗan adam. Dubban mata Fulani suna samun kuɗaɗen...
    A cewar Maiha, kafa wajen bayar da horo da kamfanin na ABIS ya yi, zai cike gibin da ake da shi a fannin kiwo da kuma bayar da gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin fannin. Ministan ya kara da cewa, bayar da ingantaccen horo a fannin bunkasa kiwo, zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan. Yayin ganawarsa...
    Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu...
    Xi Da Mai Dakinsa Sun Shirya Liyafar Maraba Da Manyan Baki A Birnin Harbin
    Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25  yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A...
    Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi. Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe. Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta...
    Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya wa al’ummarta kudin wutar lantarki a kowane wata. Shugaban Hukumar, Alhaji Bishir Sabi’u na cewa nan gaba za a kammala aikin layin da aka ware musu na musamman na Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (TCN). Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa karamar...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.   A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi...
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan...
    A ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Adamu, ta ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji. An ƙaddamar da tsarin ne a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Gombe. Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya An tsinci gawar...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya...
    Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis. Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron...
    Ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT reshen Jihar Ebonyi ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ƙananan hukumomi bakwai na jihar sakamakon rashin biyan albashin watanni. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da: Ebonyi, Edda, Ezza South, Ezza North, Ivo, Ishielu da Ƙaramar Hukumar Ohaukwu. Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar...
    Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima  NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas. Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya...
    Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya...
    Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh...
    Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa. Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin...
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin...
    Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).   Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin...
    Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar, tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl. Bayan haka, nan take kasar Sin ta sanar da daukar matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka domin kare...
    Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe....
    “Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in...
    An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Tinubu...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a ƙara adadin kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2. Wannan buƙata na ckkin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Laraba. Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo...
    A yayin da farashin buhu daya na danyar citta da ke a matsayin iri ya yi tashin gwauron zabon da ba a taɓa ganin irin sa ba, inda ake sayar da shi a kan Naira 210,000 kowane buhu, shi kuwa busasshen buhun citta ana sayar da shi ne daga Naira dubu 500,000 zuwa Naira 550,000...
    Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da...
    Rahotanni  sun ambaci cewa bayan ficewar sojan Faransa na karshe daga sansanin Abaci dake gabacin kasar Chadi,kasar Turkiya tana shirin maye gurbinta. Wata majiyar kasar Turkiya ta shaidawa wata kafar labaru ta Afirka cewa, Ankara tana shirin girke jiragen yaki marasa matuki a cikin sansanin dake kan iyaka da kasar Libya akokarin da take yi...
    Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025.   Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
    Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa.  ...
    Wasu ma’aurata ’yan kasar Australia da suka yi aure kuma suka sake rabuwa da juna har sau 12 a cikin shekaru 43 da suka gabata, a yanzu ana gudanar da bincike a kan zargin zamba tsakaninsu. ’Yan sanda a birnin Vienna na kasar Australia a halin yanzu suna gudanar da bincike a kan wani lamari...
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen...
    An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.  Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan...
    A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da...