2025-02-22@15:40:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 355
«rasuwa»:

Iran Da Pakisatan Sun Jaddada Bukatar Samar Da Harkokin Kasuwanci Na Akalla Dalar Amurka Billiyon $10 A Tsakaninsu
Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a...

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...

Sheikh Na’im Kassim: Za A Yi Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Rana 23 Ga Febrairu Da Ake Ciki
Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba...
Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai rabi da rabi, a wasu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban. Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya...
Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage daban-daban, yana mai cewa kasar ta samu bunkasa a dukkan bangarori cikin shekaru 40 da suka gabata. Iran ta yau ba Iran ce ta shekaru 40 da suka gabata ba – mun ci...
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da sanarwa da a ciki ta bukaci Isra’ila da ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon tana mai cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci. Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Badar Abdulatif ya ce, wajibi ne ga Isra’’ila da ta janye sojojin nata daga Lebanon ba tare...
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya...
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi...
An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Matakan Da Amurka Zata Bi Don Kyautata Dangantaka Da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin...

Shugaban Kasa Da Ministocinsa Sun Jaddada Bai’a Ga Wanda Ya Kafa JMI A Safiyar Yau Asabar A nan Iran
Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran, shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na...
Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda...
“Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako...

Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu. A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya...
Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna. Jimillar kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.75,...
Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da ke ziyara a Qatar ya gana da shugabannin Hamas a inda suka tattauna batun sake gina Gaza. Tattaunawar a birnin Doha ta hada fitattun jami’an kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da suka hada da Mohammed Darwish shugaban majalisar tuntuba ta Shura da Khalil al-Hayya babban mai shiga tsakani...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara...
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
Dakta Tingilin ya ce a cikin wannan shekarar, gwamnatin Jihar Katsina ta yi kasafin kudi na naira miliyan dubu 50 domin tabbatar da samar da tsabtataccen ruwan sha a kananan hukumomi 20 na cikin jihar. Ya kara da cewa kwamitin karbar korafe-korafe da aka kafa, an kafa shi ne domin duba aikace-aikacen shirin SURWASH da...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada aniyar Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a dukkan fannoni Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a fannoni daban daban....
Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
An harbe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani, Salwan Momika, ɗan asalin ƙasar Iraƙi mai shekaru 38, a gidansa da ke Södertälje, kusa da birnin Stockholm a Sweden. A harbe shi lokacin da yake ƙoƙarin wallafa bidiyo a kafar TikTok. Sarkin yaƙin Zazzau ya rasu ana tsaka da taro Hisbah ta kama masoya kan yin aure...
Hukumomi a birnin Quetta na Ƙasar Pakistan, sun kama wani mutum mai shekaru 50, kan zargin kashe ’yarsa mai shekaru 15 a duniya, saboda ta ƙi daina ɗora bidiyonta a kafar TikTok. Rahoton ’yan sanda ya nuna cewar, mutumin ya dawo da iyalinsa daga Amurka zuwa Pakistan kwanan nan kafin aikata kisan. Hisbah ta kama...
An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a...
An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a...
Hukumar Hisbah ta damke wasu matasa a jihar Kano bisa laifin yin aure a asirce ba tare da sanin iyayensu ko amincewar iyayensu ba. A cewar Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ma’auratan sun yi aure ne a wani wurin shakatawa bayan wani ya dauki nauyin biyan sadaki. Abubakar ya...
Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta kira zanga-zangar adawa da ƙarin data da kiran waya a Najeriya. NLC ta umarci rassanta na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da su shirya domin fara zanga-zangar daga ranar Takara 4 ga watan Fabrairu mai kamawa. Ta bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ganin an janye karin kashi...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga...