2025-04-17@03:08:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 63

«dimokuradiyya»:

    Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin  X, “Ya kamata Amurka...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin...
    Haka kuma, an gargaɗi kamfanonin da ke da alhakin kawo mutane Umrah cewa idan suka ƙi bayyana sunayen waɗanda suka ƙi dawowa gida, za a ci su tara har riyal 100,000. Ma’aikatar ta buƙaci kowa ya bi doka domin guje wa hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin...
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce Iran ba ta neman yaki da kowace kasa, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta saboda tana da kyakkyawan shiri a kan hakan. Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Pezeshkian ya ce...
    Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka. “Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya...
    Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
    Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin...
    A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun...
    Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta...
    Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a...
    Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana...
    Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan...
    Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara...
    “Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar...
    A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori. Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a...
    Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira. A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za...
    Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar...
    Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara. Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya....
    Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a. Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025. Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar. Sojoji sun kama...
    Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah. Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci...
    Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata...
    Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira da a gaggauta bibiyar bayanan manyan laifuka na shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Holland, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaya da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi...
    An shawarci shugabanni da aka zaba da su girmama hukuncin kotu domin tabbatar da dimokuradiyya a ƙasar. Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayar da wannan shawara a Kaduna, yana nuna damuwarsa kan zargin karya dokokin kotu a harkokin siyasa. Ya bayyana damuwarsa kan matakin da Gwamna Ademola Adeleke na...
    Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun...
    Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref...
    Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya....
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a...
    Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan...
    Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar...