2025-04-16@15:45:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3369

«kasar Belgium»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
    Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe. Kazalika, a cikin kowanne wata daya, mai ajiyar zai iya zamaowa a cikin rukunin Zakaru 70, inda kowanne mai ajiya daya a Bankin, zai iya karbar Naira 100,000. Har ila yau, a cikin watanni uku kuma, kowanne mai ajiya daya a Bankin na Stanbic IBTC, da ya fito daga yanki bakwai da ake yin kasuwanci, zai lashe Naira miliyan daya, inda kuma a zagayen gasar na karashe...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa. Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan. Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja Duk da kiran...
    Ina yi wa daujacin jama’ar musulmai na wannan gari, kasa, da ma duniya baki daya barka da sallah a ciki kuwa zan gaishe da Mamana da Babana , sannan Sadiya Rimi, Islam, Nawwara, Khairat, Rahma Abdullahi, Faddima, Mufida, Huda, Labiba, Shamsiyya Adam da fatan sun yi juma’a lafiya kuma sun yi sallah lafiya. Sako daga Jamilu Usman Jihar Zamfara: Ina gaida Matata kuma uwargidana Nana Amina da Amarya ta Halimatussadiya da ‘ya’yan Usman, Zahrah, Nana, Jidda, Hanan, Amirah, Hamza, Alida sun yi juma’a lafiya. Sako daga Wasila Muhammad Jihar Jigawa karamar Hukumar Gumel: Ina gaishe da Mahaifiyata da Mahaifina na, da kawayena Fiddausi Sa’id Danjuma, Shahida, Walida, Zeenat, Baturiyya, Lawisa da fatan sun yi sallar juma’a lafiya. Daga kanmu,...
    Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan. Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC. Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin  X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.” “Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.” A ranar Litinin shugaban Amurka Donald...
    Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
    Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin, kamar yadda wasu majiyoyi hudu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Alhamis. Wakilan tawagogin biyu sun tabbatar da kasancewarsu a babban birnin kasar Qatar, kuma sun ce za a yi ganawar ido-da-ido a ranar Laraba, amma har yanzu suna tattaunawa kan tsarin tattaunawar. Dukkanin majiyoyi – jami’an gwamnati biyu da wakilan ‘yan tawaye – sun bukaci a sakaya sunansu saboda masu...
    Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30. Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu. Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba. Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba. Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da...
    Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon. A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon wani muhimmin al’amari ne na kasa da ya zama wajibi a sanya shi cikin ajandar gwamnatin Lebanon. Ya kara da cewa: Al’ummar kasar Labanon suna fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile wannan ta’addanci. Fadlallah dai ya dauki babbar matsalar...
    Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu.   Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi.   Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar...
    Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.   Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.   Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku.   Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa.   Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin.   Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa...
      -Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
    Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.   Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba.   Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade...
    Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta. An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba. Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.   Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.   Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa.   Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.   Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki.   Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda.   Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
    Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.   Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin wani kaddara daga Allah Ta’ala.   Shugaban karamar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya wakilce shi, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki ganin yadda ba a yi asarar rayuka ba....
    Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya   Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar.   Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar.   Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...
    Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
      Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai hanyoyin arzuka iri daban daban cikin wannan Kasa, wadanda ma suka kere fetur sau ninkin ba ninki wajen bunkasar sha’anin tattalin arziki, musamnan sabgar noma, wadda wasu Shekaru can baya, ita ce kashin bayan tattalin arzikin wannan Kasa. Kuma, tun daga wancan lokaci zuwa yau din, harkar noma ce kan gaban fetur, wajen samawa dubban jama’ar Kasa aiyukan-yi. Yankin arewacin wannan Kasa ta Nijeriya, na...
    An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu da kuma Muhammad Yahaya da sunan zai yi musu aiki a sako su daga gidan yari. Lauyar masu gabatar da ƙara, Barista Sadiya Sabo, ta tuhumi mutumin da laifin damfara da kuma cin amanar da aka ba shi. Wanda ake tuhuma ya amsa laifin, amma ya bayyana cewa ba shi kaɗai ya aikata wannan haramtaccen aiki ba. ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar...
    Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa. Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa. Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin. Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI. A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...
    Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su. NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita. Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na...
    Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a. Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan doka, amma wasu majiyoyin sun ambaci cewa a cikin kwanakin bayan nan an sami rikice-rikice a yankin. Wasu majiyoyin sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai sun yi harbe-harbe a yankin wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane biyu a garin  Basras-sham.
    Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da  ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL da ta kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Masalit da sauran al’ummu a cikin tsawon shekaru biyu na yakin basasar kasar. Ministan shari’a na kasar Sudan Muawia Usman ya bayyana cewa: Kisan kiyashin da dakarun kai daukin gaggawa su ka yi wa al’ummar Masalit da su ka kunshi larabawan yankin Darfur, ya faru ne ta hanyar taimakon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.” Bayan...
    Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani dan bangere na mutanen da ke yin cacar ne kawai, ke samun a cacar, inda akasarin sauran, ke tabka asarar kudadensu da suka zuba a cikin cacar. An dai jima ana yin caca a kasar, wadda a shekarun baya, ake yi mata wani kallon kan abinda bai dace ba, kamar dai yadda Coci ta alakanta ta, a matsayin hanyar yin arzikin dare daya Idan za...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
    Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa. Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar. Ya koka da...
    Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan suka fara dandana kudarsu, inda aka fara ganin koma bayan kasuwannin hannayen jari, da gurguncewar sana’o’i sakamakon rashin tabbas da kasar ke fuskanta, yayin da kasar ke tunkarar matsanancin yanayi na komadar tattalin arziki.   Wata manuniya da ka iya haskaka abun da ka iya wakana ga Amurka a wannan karo ita ce irin yadda Amurka ta sha fama da kalubalen hauhawar farashi, da koma...
    Yau Alhamis ranar 10 ga wata, an fara “Ranar Sinanci ta MDD” ta shekarar 2025, wato bikin nuna fina-finan Sinanci na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG karo na 5 a hukumance.   An kaddamar da bikin bisa hadin gwiwar CMG da kungiyar wakilan kasar Sin na MDD dake birnin Geneva da na sauran kungiyoyin kasa da kasa, da ofishin MDD dake birnin Geneva. Daga cikin shirye-shiryen bikin mai taken “Ziyara A kasar Sin” wato “China Travel” a Turance, an gayyaci jama’ar kasashen duniya da su tsara bidiyo game da ziyararsu a kasar Sin, inda suka nuna kyawawan al’adu da zamantakewar al’umma na kasar Sin, da kuma yanayin bunkasuwar kasa, domin samar wa al’ummomin...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar. Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar. Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka. Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya. A cewarsa, an...
    Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato ta fara biyan sabon albashin tun a watan Janairu ga dukkanin ma’aikatan jihar, ciki har da na ƙananan hukumomi. Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ya ce: “Sakkwato ce jiha ta farko da ta fara biyan sabon albashi na dubu 70, kuma ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi na amfana da shi. “Maganar shugaban...
    Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin hana fasa korin muggan kwayoyi da kuma sulalewar yan ta’adda suka kan iyakokin kasashen biyu. Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan  sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn   yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta. Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social, Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a dai dai lokacinda gwamnatin Amurka ta dorawa kayakin kasar China masu shigowa Amurka kudin fito na kasha 125%. Tun zagaye na farko na shugabancinsa ne shugaban ya fara rigima da kamfanin Tiktok na kasar China wanda ya sami karbuwa a cikin Amurka da kuma kasashen duniya da dama. Amurka tana ganin shafin yanar gizo na tiktok barzane ce ga tsaron kasar Amurka. Kuma har ta...
    Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI. Amma sojojin sun kammala da cewa a...
    Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan da gwamnatin shugaba Trump ta kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama wadanda suka hada da China da kuma kasashen turai EU. Labarin ya kara da cewa karin kudaden fiton sun shafi motoci da karfe da kuma karfen alminium ne da suke shigo da su daga kasar ta Amurka ne.  Banda haka karin kudaden fiton sun shafi kayakin abinci wadanda suka hada da waken...
    Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu. Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma...
    Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.   Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin daliban firamare ba su iya karatu ko rubutu yadda ya kamata.   Ya bayyana cewa, an dauki malamai sama da 7,000 a karkashin gwamnatinsa domin karfafa ilimin boko, ya kuma ce jihar ta bullo da sabbin dabaru da suka shafi al’umma, kamar taron iyaye mata da kuma farfado da kwamitocin gudanarwa na makarantu (SBMC), domin inganta zuwan yara makarantu da kuma lura da yadda malamai...
    Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A sa’i daya kuma, mambobin kungiyar WTO sun jaddada cewa, za su nuna goyon bayansu ga kungiyar WTO don ta ba da gudummawa kamar yadda ake fatan gani, kana suka yi kira ga dukkanin mambobi da su warware sabanin dake tsakaninsu bisa ka’idojin kungiyar ta WTO. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari a ƙaramar hukumar Tarmuwa a ranar 9 ga Afrilu, 2025. Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi A takardar sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya fitar ya ce, hedikwatar ’yan sanda reshen Dapchi da misalin ƙarfe 0500hrs, 9 ga Afrilu, 2025, ta cafke waɗanda ake zargin, ’yan ƙungiyar...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunkure. Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima “Manufarmu a bayyane take – bincike, tattaunawa da bayar da shawarwari masu ɗorewa. “Wannan ba kawai yawon neman gaskiya ba ne, har ila yau ƙoƙari ne na kawo zaman lafiya, domin hana sake faruwar irin wannan tashin...
      Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tommy Bruce a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun tattauna kan yunkurin diflomasiyya a Gaza na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da tsagaita bude wuta mai dorewa a Gaza inda Hamas ta samu cikaken kwance damarar makamai da nakasassu. An gudanar da taron ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yin kiraye-kirayen a samar da mafita a siyasance a yakin Gaza, inda Isra’ila ta kashe Falasdinawa fararen hula fiye da 50,000 tun daga watan Oktoban 2023 (Bahan 1401). A yayin da Amurka ke ci gaba da goyon bayan munanan hare-hare na gwamnatin sahyoniyawan da kuma kokarin...
    Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi a kasar, da kuma goyon bayan da take baiwa mayakan sa kai na Rapid Support Forces, tana mai kallonta a matsayin wani bangare na haddasa rikicin da ke faruwa a Sudan. A wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan Laraba 9 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin Sudan da ke Tehran, jakadan Sudan ya yi tsokaci kan laifukan da dakarun RSF suka aikata...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin daukar matakin hadin gwiwa da kasashen yankin domin gaggauta dakatar da laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da kuma tsagaita bude wuta a zirin Gaza, lamarin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen warware wasu rikice-rikice a yankin yammacin Asiya. Jami’an biyu sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, sakamakon ci gaba da kai...
    Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump. Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara  daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji. Kayayyakin na Amurka da tsarin...
    Guguwar ruwan sama ya lalata gidaje da dama a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a Ƙaramar hukumar Shanga, ya kuma buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su ɗauki lamarin a matsayin wata ƙaddara. Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Ahmed Idris ya fitar. A cewar sanarwar, gwamnan wanda shugaban Ƙaramar hukumar Shanga, Audu Audu ya wakilta, ya ce ruwan sama mai ƙarfi da ya afku a daren ranar Talata ya lalata gidaje da dukiyoyi...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet Ya ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne. Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa. “Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC). Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT. Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet Ya ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne. Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa. “Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban...
    Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin litar man fetur zuwa Naira 865 ga dillalai masu saya daga wurinta. A safiyar Alhamis hukumomin Matatar Ɗangote suka sanar da dillalai dangane da ragin naira 15 daga tsohon farashin man na naira 880.
    Al’ummomin Jihar Kastina sun shiga sabon tashin hankali bayan da ’yan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare a wasu yankuna biyu a Jihar Katsina a ƙarshen makon jiya, inda suka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 59. A daren Lahadi, kusan ƙarfe 10:30, ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai farmaki ƙauyen Layin Gara a Ƙaramar Hukumar Funtua, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 16. Shaidu sun ce maharan sun ɗauki sa’o’i da dama suna cin karensu babu babbaka, ba tare da wani ƙalubale daga jami’an tsaro ba. Kwana ɗaya kacal kafin hakan, a ranar Asabar, ’yan bindiga ɗauke da manyan makamai a bisa babura sun mamaye ƙauyen Maikuma, inda suka kashe...
    Wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta ce: “Wannan tsari ba na wucin gadi ba ne. Tsarin sayar da ɗanyen mai a farashin Naira wata dabara ce ta bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma bunƙasa tsaron makamashi a Nijeriya.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa. Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar da kin amincewar da Iran ta dade tana yi na yin watsi da shirye-shiryen mallakar makamin nukiliya, wanda kasashen yammacin duniya ke zarginta da neman bama-baman nukiliya. “Muna shirye don yin shawarwari, ba kai tsaye ba. Ba mu amince da su ba. Dole ne a yi tattaunawa bisa mutunta juna inji shugaban kasar ta Iran. “Ba mu taba kera bama-bamai na nukiliyaba, ko a baya,...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da kuma wani mutum guda da ke Iran, saboda abin da sashen ya bayyana a matsayin goyon bayan shirin nukiliyar Iran. Baitul malin na Amurka ya ce bangarorin da aka laftawa takunkumin na baya baya nan sun hada da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) da ta karkashinta, Kamfanin Fasaha na Centrifuge na Iran. Sakataren baitul malin kasar Scott Bessent ya bayyana a cikin wata sanarwa...
    Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Mali da kuma Aljeriya. Ecowas din ta ce ta damu matuka kan lamarin, tana kuma mai kira ga kasashen na Mali da Aljeriya da su kai zuciya nesa, su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabanin ra’ayin da ke a tsakaninsu.” Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya, ta yi tsami ne bayan da a makon da ya gabata Aljeriya ta kakkabo wani jirgi...
    A ranar Talata ne mai martaba Sarkin Kano Malam Mohammad Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Mannir Sunusi a matsayin sabon Galadiman Kano.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan jarida da yada labarai na masarautar Kano, Saddam Nasir Na’ando ya fitar, kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya da ke Kano.   Haka kuma Sarki Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Kabiru Tijjani Hashim zuwa Wamban Kano.   Sauran nada nade sun haɗa da “Alhaji Mahmoud Ado Bayero ya tashi daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano da Adam Sanusi yanzu ya zaman Tafidan Kano sai kuma Ahmed Abbas Sanusi ya zamaYariman Kano.   Sanarwar ta kara da cewa wadannan nade-naden sun fara...
    Wannan rikicin haraji ya faro ne tun shekarar 2018, lokacin da Trump ya fara ƙaƙaaba wa China da wasu ƙasashe haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shiga da su Amurka, a wani yunƙuri na kare masana’antu da ayyukan yi a cikin gida. Sai dai masana tattalin arziƙi sun ce wannan mataki zai iya kawo tasiri ga farashin kayayyaki a Amurka da kuma haifar da sabuwar ɓaraka a dangantakar cinikayya tsakanin manyan ƙasashen duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.   Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.   A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan ​​matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”   Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar...
    Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
    Ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da mara wa shirye-shiryen da za su bunƙasa ilimi da jin daɗin al’umma baya. Shugaban majalisar ya ƙara da cewa salon shugabancin gwamnan wanda ke ku8nshe da gaskiya da riƙon amana ya taimaka wajen amincewar jama’a ga gwamnati. Ya ce Gwamna Yusuf jagora ne mai sauraron ƙorafin jama’a tare da himma wajen biyan buƙatunsu. Ya buƙaci gwamnan da kada ya yi ƙasa a gwiwa wajen ci gaba da aikinsa duk da sukar da wasu ke masa. Haka kuma ya shawarci sauran jami’an gwamnati da su kwaikwayi irin sadaukarwar gwamnan wajen yi wa al’umma aiki. An gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a Abuja, inda aka yaba wa Gwamna Yusuf...
    Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta fara gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa duk shekara a jihar Sokoto da nufin karfafa sojojin Najeriya don shiryawa tsaron kasa.   Babban Jami’in Kwamandan runduna ta takwas Manjo Janar Ibikunle Ajose ya ce gasar tana nuni ne kai tsaye ga hafsan hafsoshin sojin kasar na ganin an gyara da sauya dabarun jagoranci da fagen fama a matakin farko.   GOC wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta 78 da ke samar da kayayyaki da sufuri, Birgediya Janar Moses Udom Ikobah, ya bayyana cewa fafatawar ta yi daidai da kokarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi na inganta yaki da ta’addanci ta fuskar tsaro.   Ya bukaci dukkan mahalarta taron da su...
    Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a.   Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano suka shirya, wanda aka gudanar a otal din Bristol Kano.     Falana ya yabawa jihar Kano bisa amincewa da dokar hukumar kula da laifuka ta FIDRA a shekarar 2019 tare da zama jiha ta farko da ta soke tuhumar da jami’an ‘yan sanda ke yi na aikata laifuka.   Ya kuma jaddada bukatar masu gabatar da kara su samar da na’urori na zamani da...
    Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa.   Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB) ta shirya, kwamishinan ilimi da ci gaban bil’adama na jihar, Dokta Lawal Olohungbebe ya ce shirin na daya daga cikin manyan dabarun da jihar ta bullo da shi na bunkasa harkar ilimi domin ya dace da ka’idojin karni na 21.   Ya kuma bukaci malaman da su ci gaba da jajircewa...
    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba.   Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Istijaba Villa da ke karamar hukumar Kalgo a jihar inda suka yi garkuwa da wani dalibi a dakin kwanan dalibai a harabar jami’ar, kuma abin bakin ciki, wani Malam Siddi Hussaini, wanda ke kusa yana kiwon shanun sa, a lokacin da yake kokarin shiga tsakani, shi...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan.   Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar ofishin shiyya ta Kaduna na EFCC zuwa NUJ a jihar Neja a Minna.   Mista Bawa Usman wanda ya shaida wa manema labarai cewa an kama masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba amma ya ci gaba da cewa “yaki da wadannan laifuffuka ba na EFCC kadai ba ne domin yana da girma da yawa a gare mu don haka yana bukatar hadin...
    Yankin Kogi ta Yamma na fama da matsalar tsaro, inda aka ruwaito wasu mazauna garin Oduape a Ƙaramar Hukumar Kabba Bunu sun gudanar da zanga-zanga a bara domin nuna fargabarsu game da yawaitar sace-sace da kashe-kashe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
    Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina. Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan. Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni.   Ban da haka kuma, ma’aikatar ta ce kasar ta kara sunayen wasu kamfanonin Amurka 6, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba.   Ma’aikatar wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce kamfanonin su ne Shield AI, da Sierra Nevada Corporation, da Cyberlux Corporation. Sai kuma Edge Autonomy Operations LLC, da Group W and Hudson Technologies.   Tun daga karfe...
    An yi nasarar kashe wani ɗan bindiga  yayin da jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 10 da aka sace a wani samame na haɗin gwiwa a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Waɗanda aka ceton da suka haɗa da mata shida da maza huɗu, an yi garkuwa da su ne daga kauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke da ke karamar hukumar ta Musawa. Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina Sin Ta Fitar Da Takardar Matsayarta Kan Alakar Tattalin Arziki Da Amurka A cewar sanarwar da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Katsina, Nasir Mua’zu ya fitar, an kai samamen ne da misalin karfe 10 na daren ranar 8 ga watan Afrilu a...
    Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya a yankin zai rage matsalolin sufuri da mazauna yankin ke fuskanta, musamman wajen samun damar zuwa asibiti da sauran wuraren kula da lafiya. Ya ce, samar da hanyar kuma zai kara bunkasa harkokin kasuwanci, da karfafa dangantaka tsakanin al’umma da kuma saukaka wasu bukatu na yau da kullum da ke da matukar muhimmanci ga cigaban yankin. Malam Ali Turbus ya kuma roki shugabannin karamar hukumar...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki  ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025. Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna. Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya. Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya. Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya  ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare...
    Idan Barcelona ta kai matakin gaba za ta hadu da PSG ko Aston Villa wadanda su ka buga dayan wasan da aka buga a daren ranar Laraba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma.   Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%.   Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar...
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fidda jadawalin kudaden fito ga dukkan kayakin da suke shigowa Amurka daga wadannan kasashen, daga ciki har da kasashen Turai da kuma kasar Chaina, ya zuwa yanzu dai kasar china ta maida martani da kashi 34% na kayakin Amurka da suke shigowa kasar China, sannan Amurka ta kara maida martani ga kasha 104 kan kayakin kasar china masu shigowa Amurka, sannan kasashen turai da dama...
    Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu da ke Gusau, babban birnin jihar. DSP Abubakar ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano adadin mutanen da aka sace a harin. Ya tabbatar da cewa ana kokari don ganin an ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya. Yazid ya kara da cewa an kara kaimi wajen daukar matakan tsaro domin hana faruwar irin...
      Don haka bangaren Sin ya kalubalanci kasar Amurka da ta gyara kuskurenta cikin hanzari, ta soke dukkan matakan kara buga harajin kwastam kan kasar Sin daga bangare daya, kana ta hau teburin shawarwari tare da kasar Sin, don daidaita matsalolinsu bisa tushen girmama juna. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a wanda aka gudanar a nan Tehran. Shugaban ya kara da cewa, Iran bata neman yaki da kowa, amma zata maida martani kan duk wata takala daga HKI ko Amurka. Ya ce Iran ba zata amince wani ya hana mutanen kasar amfani da fasahar da All..ya hore masu ba. Ya kuma kara jaddada cewa JMI bata neman mallakar makaman Nukliya. A rana irin ta yau ce...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu  tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
    Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a yau Laraba . Ya kuma kara da cewa, a wannan karon sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Yaffa (tel’aviv). Haka ma sun cilla wasu makaman kan jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wato USS Harry Truman dake arewacin tekun red Sea. Kafin haka dai jiragen Amurka...
    Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau Laraba sun kuma kara da cewa, idan gwamnatin Trump bata dakatar da wannan yakin kasuwanci ba to kasar China tana da hanyoyi da dama wadanda zata ci gaba da wannan yakin har zuwa karshe. Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakan kasar China masu shigowa Amurka kudaden fito daga kashe 34% zuwa kasha 104 % kuma a yau Laraba ne dokar karin zai...
    A ci gaba da kokarinsa na kawo sabon tsari domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wani babban taro da manyan masu zuba jari na duniya da masu ruwa da tsaki a harkar noma. Taron wanda ya gudana jiya Talata a otal din Hilton da ke Abuja, ya kunshi wakilai daga kamfanonin SINOMACH, China CAMC Engineering Company Ltd, YTO Group Corporation, da Agra Consortium Ltd, da kuma asusun bunkasa noma na gwamnatin tarayya (NADFUND). Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata...
    Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani.   Ta ce nahiyar Afrika za ta iya cin gajiyar fasahohin aikin gona na kasar Sin, da wanda ya dace da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, domin bunkasa noma a cikin gida da ma fitar da amfanin gonar. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Wadda aka tsara a cikin babi shida, takardar matsayar ta gwamnati ta sake tabbatar da yanayin moriyar juna ta cinikayya tsakanin Sin da Amurka.   Ta kara da bayyana cewa, kasar Sin ba ta neman cin bulus a harkar kasuwanci, kuma bangarorin biyu sun samu riba mai yawa daga hadin gwiwar tattalin arziki da suke yi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kuɗin fansa. Ribadu, ya ce biyan kuɗin fansa ba ya sa ana sakin waɗanda aka sace, kuma hakan na ƙara dagula al’amuran tsaro. Harajin China da Amurka: Mece ce makomar tattalin arziƙin duniya? Za a ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira — Gwamnati  Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, yayin da yake karɓar mutane 64 da dakarun tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da su a Zangon Kataf da ke Kudancin Kaduna. “Don Allah ku daina bai wa waɗannan mutane (masu garkuwa) kuɗi, wannan shi...
    Kungiyoyin biyu sun hadu sau 6 a tarihi, Barcelona ce ta samu nasara akan Dortmund sau 4 a tarihi yayin da aka buga canjaras a wasanni 2, Dortmund ba ta taba samun nasara akan abokan karawar ta su ta yau ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp