2025-03-25@01:47:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 563
«Yan Nijeriya»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya. Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar...
Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi. A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma...

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da...
Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan...
’Yan bindiga sun kai hari wata coci da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta, inda suka yi awon gaba da masu ibada a daren ranar Juma’a. Sun harbi fasto sannan suka sace masu i ada shida a cocin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 —...

Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da...
“Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.” Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa. Idris ya ƙara...
‘Yan daban sabuwar gwamnatin Siriya sun kai samame wani Masallaci da ke cikin karkarar birnin Damascus tare da korar masu ibada Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar da ke da alaka da gwamnatin rikon kwarya a kasar Siriya sun kai farmaki kan Masallata da ‘yan kasar ke...
Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun...
“Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar. Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda. Danlami...
Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.

Hamas, Da OIC Sun Yi Allawadai Da Dirar Mikiyan Da HKI Take Yi A Tulkaram Na Yankin Yamma Da Kogin Joirdan
Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin...

Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD
A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da...

Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron...

Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan
Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar...
Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin...
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da...
Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau
Ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da suka yi ritaya, sun bayyana jin dadinsu kan karin haske da Ministar Kudi ta yi game da wadanda za su ci gajiyar Naira Biliyan 758 da aka amince da su don biyansu kudaden fansho da suke bi. A tsokacin da suka...
Fitaccen dan jarida na Amurka wanda Patrick Heili ya yi hira da shi ta Podcast, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son ya ci gaba da zama akan kujerar mulki har abada. Hirar da Thomas Friedman ta mayar da hankali ne akan salon mulkin Donald Trump da yadda yake son sauya yadda...
Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai hada kasashe da dama na yankin. ‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu...
A kasar Malaysia an bude yin kira da a yanke kere-keren kamfanin Elon Musk saboda goyon bayan da yake nuna wa Donald Trump da siyasarsa ta son korar Falasdinawa daga Gaza. Mutanen kasar ta Malaysia ne suke amfani da kafofin sadarwa na al’umma wajen yin kira da a yanke mu’amala da motocin da kamfanin na...
A yau Jumma’a ne jirgin saman da kasar Sin ta kera samfurin AS700D mai amfani da makamashin lantarki ya kammala tashinsa na farko cikin nasara, wanda ya nuna sabon ci gaban da kasar ta samu a sashen samar da kayayyakin sufurin jiragen sama masu amfani da makamashi mai tsafta a fannin tattalin arzikin jirage masu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba. Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu. Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA...
Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...
Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe. “Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,”...
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma. Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance...
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da...
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross. Mutanen dai Isra’ila ta kasha su a cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su lokacin kai hare-hare a Gaza. Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan hudu...
Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya...
Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan...
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga...
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6...
Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare....

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan...