2025-02-21@14:57:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 289
«Yan Nijeriya»:
Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na...
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya halarci wani taron tattaunawa na kamfanoni masu zaman kansu a yau Litinin. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsakiya na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan sauraron ra’ayoyin wakilan ‘yan kasuwa masu zaman kansu....
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa...
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa...
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu...
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin...
Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an...
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin....
Har ila yau a jiya Asabar, Wang Yi ya kuma gana da jami’an kasahen Brazil, da Czech, gami da Austria. (Bello Wang)
Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi. Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta. Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace...
“A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.” PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton...
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya buƙaci Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas (NEDC) da ma’aikatar raya yankuna ta tarayya da su magance talauci a yankin ta hanyar zuba jari a fannin ilimi. Shettima ya yi wannan kiran ne a yayin wata ganawa da ya yi da mahukuntan hukumar ta NEDC a fadar shugaban kasa da...
Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen. Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin...

Trump Ya Bukaci Ukirain Ta Bada Ma’adinanta Ga Kasar Amurka Idan Tana Son Ta Taimaka Mata Da Kayakin Yaki
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake...
Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi...
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta. Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu...
Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan...

Ministan Tattalin Arziki Na Kasar Iran Ya Kama Hanyar Kasar Saudiya Don Halattar Taron Tattalin Arziki
Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar...
Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta...
Amincewa da Karin kudin dai ya zo ne domin cike gibin da aka samu, bayan da Amurka ta yanke kudaden taimakon da take bayarwa a fagen kiwon lafiya. A shekarar 2023 Kasar Najeriya mai mutane fiye da miliyan 200 tana cikin 10 na farko da su ka fi karbar tallafin hukumar Amurka na raya kasashe...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama. A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar...
Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma. Gwamnan a wajen bikin mika ragamar...
Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen...
Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya. Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar. A cikin...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A...
Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma...
Manyan jami’an Philippines sun sake ikirarin shirin sayen makamai masu linzami dake cin matsakaicin zango na Amurka tare da hada su da batun tekun kudancin Sin. Hakika matakin na Philippines ya damka muradun kasar na tsaro a hannun kawayenta na yammacin duniya. Dabarar Philippines ta dogaro da kasashen yamma ba za ta samar da tsaro...
Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA). A duk duniya, OCHA, wacce ke...
An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100...

Malaman Yahudawa Fiye Da 300 Sun Rattaba Hannu Akan Takardar Kin Amincewa Da Shirin Donald Trump A Yankin Gaza
Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya...
A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da...

Ranar Kafar Rediyo ta Duniya: Minista Ya Buƙaci Gidajen Rediyo Da Su Faɗakar Da Jama’a Kan Sauyin Yanayi
A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli. “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta...
Mutanen Najeriya suna bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa. Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da...
An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano. Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula,...
Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025. A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon...