2025-02-21@14:31:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 401
«Sani Haidara»:
daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga. “A baya masu sana’ar a kullum suna samun kudaden shiga masu yawan gaske, sai dai; saboda raguwar Kifin a Koguna, kudaden shigar da suke samu sun ragu”, in ji Dauda. Wani jami’i a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar, wanda bai bukaci a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da wannan raguwa ta Kifin a Kogunan jihar. Kazalika, Mallam Dauda ya alakanta wannan kalubalen kan irin yanayin kamun Kifin...
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis sun bayar da gudunmawar ne domin ginin dakin karatun da tsohon shugaban ƙasan ke shirin ginawa. Attajiri mafi yawan arziki a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Alikon Ɗangote ya ba da gudunmawar Naira biliyan takwas, Naira biliyan biyu a duk shekara, na tsawon shekara huɗu. Ya kuma yi alƙawarin karin biliyan biyu a duk shekara...
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar. Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu. Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080. Tace Siriya tana...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba ɗaya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama’a irin cigaban da gwamnati ke samu.
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan takara. Mafi yawancin wa’azi da khudubobi sun kasance wurin tattauna harkokin siyasa. A wasu majami’u, fastoci sun yi da’awar manzancin kan ‘yan takararsu, yayin da a cikin malaman addinin musulmi, limamai sun bukaci mabiya da su yi zabe ta hanyar addini. Abin mamaki, yawancin wadannan hasashen addini ba su tabbata ba. A kwann nan dai an tafka cece-kuce kan taron da aka shirya gudanarwa a...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu wanzuwa idan babu Amurka, yana mai cewa, ita kanta Amurka ta kama hanyar rugujewa. Ya kara da cewa: Wadannan al’amura suna faruwa ne a kasa kuma wani bangare ne na makomar al’umma, don haka wajibi ne al’umma su dogara ga Allah kuma su yi duk abin da za su iya. A yayin ganawarsa da Ziyad al-Nakhala babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami, Manjo Janar Salami ya yi...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci gaba da kokawa kan yadda har yanzu ba su gani a ƙasa ba. Tun makonni biyu da suka gabata aka sanar da saukar farashin fulawar kamar sauran kayayyakin masarufi. To amma ba kamar sauran kayan abinci ba, har yanzu ba a ga sauyi a farashin burodi ba. NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya...
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man. “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha. An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, damar tsayawa takara a zabubuka masu zuwa, sannan a amince da islama a matsayin addini mai rinjaye a kasar. Taron ya kuma bukaci rushe dukkan jam’iyun siyaya 172 a kasar. A yayin rufe taron janar Tiani ya yi alkawarin biyan bukatun mahalarta taron. A shekarar 2023 ne sojoji suka kwace mulkin Nijar, bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, bisa hujjar tabarɓarewar matsalar tsaro da rashin...
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza. Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito. Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare. Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi...
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son...
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram. An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Garba, ya nuna damuwa game da kalaman da ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi kwanan nan, inda ya zargi USAID da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram tallafi. Ya jaddada cewa Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya sama da shekara 10....
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Lita 60,000
Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida. Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar. Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi. Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa. Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin,...
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci. Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3 Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a Saudiyya ba. ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa A cewar Trump, Ukraine ce ta jawo wa kanta matsalar. “Da ba ku fara wannan yaƙin ba, da kun cimma yarjejeniya tun farko,” in ji shi. “Da ni ne, da na samo muku mafita, kuma babu wanda za a kashe.”...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki. Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu...
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki. Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada labarai na Nijeriya, don haka, shugaba Tinubu na yi masa fatan alkairi a rayuwa ta gaba mai zuwa da karin kaifin basira. Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba dan jaridan lafiya da samun biyan bukata a dukkan ayyukansa.
Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu. Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES). Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe. Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma. Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.” Shugaban shirin L-PRES...
Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin. Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a...
Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Wata majiya ta bayyana cewa, wani kwamandan ’yan ta’addan mai suna Tar ne ya jagoranci garkuwa da mutanen ne a ranar 13 ga watan Fabrairu 2025. Tar da tawagarsa da ke addabar masunta da manoma a gaɓar Tafkin Chadi sun ɗauke mutanen ne yayin da suka afka wa al’ummar Shawaram da ke ƙarƙashin Ƙaramar...
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su ka shafi Gaza da kuma Amurka, kamar yadda kamfanin dilllancin labaun Mehr ya nakalto. Jakadan Jamhuriyar musulunci ta Iran a Qatar, ya saanr da cewa ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo Tehran tana a karkashin kokarin bunkasa alakar kasarsa da Iran.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan. Bugu da kari makaman saman na Rasha sun kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki guda 4 a sararin samaniyar “Bahrul-Aswad”, sai kuma jirgi guda daya a saman yankin Tula. A gefe daya a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya. Sakataren...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90. DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan. Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a...
Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma Mali suka fice daga kungiyar sannan suka samar da sabon Passport a tsakanin kasashen uku, sai al-amura suka fara sauyi tsakaninu da Ecowas. Sun fara hana wadanda suke rike da Passpory na kasashen ECOWAS shiga kasashen ba tare da visa ba. Gwamnatin Nijer bata bada sanarwan fara aiki da wannan dokar ba. Kuma wani jami’in shige da fice na Niger ya ce umurnin ne aka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata. A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar. Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.
’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban. Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a kan Iran da al’ummarta ba ta cimma nasara ko yin tasiri ba. Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake karbar bakwancin dubban mutane daga lardin gabashin Azarbaijan a Husainiyar Imam Khumaini da ke Tehran fadar mulkin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar bore mai tarihi na al’ummar Tabriz a ranar 29 ga watan...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk abin da yake so. Trump ya tabo batun mataki na gaba – ana sa ran za a fara tattaunawa nan ba da jimawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar – ya ce: “Ya rage ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan mataki na gaba, tare da tuntubarsa.” An kuma tambayi Trump ko jinkirin jigilar makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila a karkashin Shugaba Biden zai “hana tsagaita...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce damarsu ta samun nasara kan Real Madrid ’yar kaɗan ce a yayin da a gobe Laraba ƙungiyoyin biyu za su yi karon-batta a Gasar Zakarun Turai. Ana iya tuna cewa, a karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City da ci 3-2, minti huɗu kafin a tashi wasan. Hauhawar farashi ya koma kashi 24 a Nijeriya — NBS Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya To sai dai gabanin karawar ta biyu da za a yi a filin wasa na Bernabeu, a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ’yan 16, Guardiola ya ce damar da suke...
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...

Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arazgchi ya kara jadda cewa JMI ba zata zauna a teburin tattaunawa da kasar Amurka ba a karkashin takunkuman tattalin arziki ba. Ya kuma kara da cewa Amurka ba zata iya tursasawa kasar Iran zama da ita ba. Ministan ya kara da cewa, ba zakin baki mukeso ba, sai mun gani a kasa a sanya hannu a dakardu sannan mu gani a kasa. Ministan ya fadawa tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye shiryenta da harshen larabcin a nan Tehran, ta kuma bayyana cewa, Trump ya bayyana cewa ya na bukatar tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya tun watan farkon waten Fabrairu amma ba abinda muka gani a kasa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran. Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne. Duk da...
Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai kyautata al-amuran tsaro a yankin. Wanda kuma zai tabbatar da ikon kasar Lebanon a kan dukkan kasar ta. Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Lebanon ta bokaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar. Sannan bisa kudurin mai lamba 1701 na MDD rundunar UNIFIL zata taimaka wa sojojin kasar tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin HKI da kuma kasar Lebanon. Labarin ya kara da...
Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo. Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi. Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Aminiya ta ruwaito cewa, zuwa wayewar gari Litinin, matar da ’ya’yanta —Bukola da Ifeoluwa— sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar. Wani maƙwabcinsu da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun tsakar dare gobarar ta tashi amma ana ji ana gani ta rutsa da mutanen uku...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin. Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi. Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar...
Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau. Ya kuma kara da cewa abubuwan da HKI ta sa a gaba sun hada da ganin kasar Iran bata mallaki makaman Nukliya ba, da shafe kungiyar hamas, sakin fursinoni a hannun Hamasa da kuma samar da huldar jakadanci da kasar Saudiya. Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da...
Shirin Trump Na Gaza Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila. A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a yankin.
Da farko za ku zuba Fulawa a wata roba haka sannan ku kawo Baikin Fauda ko Yis duk dai wanda za ku yi amfani da shi ku zuba, sai ku zuba madara sannan sai Gishiri kadan haka sai Qwai shima ku fasa a ciki, amma kada ya yi ruwa ko kauri kwabin. Sannan sai ku cuccura shi kamar Bol. Sai ku dora Mai a wuta ya yi zafi, sannan ku fara soyawa. Bayan kin gama suya shi sai ki barbada masa sikari. Yadda Ake Hada Fankek da Zuma: Abubuwan da za ku tanada: Fulawa, Bakin Fauda, Qwai, Madarar Ruwa, Gishiri, Bota: Yadda za ku hada: Za ku samu roba tankade fulawar a ciki duk abin da za ku...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan.
Ƙungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa ta Ƙasa (IPAC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana amincewarta da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Laminu Lawal Boyi, ya bayyana cewa IPAC ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bai wa dukkanin jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen. Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan sanda a Ondo NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya “Baya ga shugabancina a IPAC, ni kuma shugaban jam’iyyar Accord ne, wacce ta shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 34 da kujerun kansiloli 361 a faɗin jihar. “A matsayina na ɗan takara kuma mai ruwa da tsaki, na...
An samar da ruwan sha a yankunan Danbatta, da Makoda da Minjibir dake gundumar Kano ta Arewa bayan kwashe kimanin shekaru goma. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka a wani rangadin da ya kai kananan hukumomin uku domin tantance yadda ake samar da ruwan sha ga al’umma. Umar Doguwa ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu sosai wajen samar da ruwan sha a dukkan lungu da sako na jihar Kano. Ya ce an gyara kananan cibiyoyin samar da ruwan sha a yankunan inda ake samar da ruwa babu kakkautawa. Kwamishinan ya ce yanzu haka ana samun ruwan sha a kauyukan kunya, da Kilawa da ,wailare duk a karamar hukumar Minjibir yayin da...
Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sake jaddada cewa ƙasashen waje ne ke tallafa wa ’yan ta’addan Boko Haram da kuɗi da makamai. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Janar Musa ya nuna damuwa kan yadda ƙungiyar ke ci gaba da aikata ta’addanci sama da shekaru 16, duk da ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi na daƙile. Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Ya bayyana cewa an kama wasu ’yan Boko Haram ɗauke da maƙudan kuɗaɗe da ke da alaƙa da ƙasashen ƙetare. Ya nuna cewa akwai ƙasashen da ke taimaka wa ƙungiyar daga waje. Janar Musa ya yi tambaya cewar: “Ta...
Bugu da kari, Tinubu ya amince da rashin shinge a sabuwar harabar jami’ar ne ya kawo wannan takaddamar, inda nan take ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta ware kudade domin gudanar da aikin kafa katafaren shinge a tsakanin kauyen da Jami’ar. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na inganta ababen more rayuwa na jami’o’i a fadin kasar nan.
Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi. Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta. Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace gidajen Falasdinawa da dama da suke a kusa da sansanin Tul-kram, da mayar da su zama sansanonin soja. Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da ‘yan sahayoniyar su ka tilastawa yin hijira daga sansanonin Tul-Karam da Nuru-Sahmsh, sun kai 10,000. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa, adadin mutanen da su ka yi shahada a cikin kwanaki 21 na hare-hare sun kai 11, yayin...
Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa dai tana fatan fahimtar juna. Shugaban gwamnatin kasar ta Jamus; Duk wanda yake son nahiyar turai ta shiga cikin batun zaman lafiya, to dole ne ya yi tarayya da ita cikin daukar matakan da su ka dace.” Shugaban gwamnatin na kasar Jamus dai yana mayar da martani akan batun kawo karshen yakin Rasha da Ukiraniya ba tare da bai wa kasashen na turai damar bayyana ra’ayinsu akan batun ba. Dangane da batun kara kudaden fito akan hajar da kasashen turai ke shigarwa Amurka, Olaf Scholz ya ce, Turai tana da karfin da za ya iya...
Shekara guda bayan da Hukumar Zabe (INEC) ta dakatar da sake zaben mazabar Tsanyawa da Kunci a Majalisar Dokokin Jihar Kano, yankin ya ci gaba da zama babu zaɓaɓɓen wakili da yake wakiltar su a Majalisar Dokokin jihar. Hukumar Zabe ta Ƙasa ta dakatar da sake zaɓen ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2024, bayan da wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ce suka tarwatsa sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe da dama a kananan hukumomin biyu. Yadda za a yaƙi talauci a Arewa maso Gabas — Shettima Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 a Borno A shekarar 2023 ce Kotun Daukaka kara ta soke zaben dan Majalisar Dokoki na Jam’iyyar APC mai wakiltar...
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen farfado da darajar ilimi, ya kuma nuna damuwa bisa ganin yadda darajar ilimi take kara faduwa a kasar nan. Ya ce dole sai gwamnati tarayya da na jihohi sun hada kai wajen tafiyar da harkar karantawa a kasar nan ta yadda yaran masu karamin karfi za su sami ilimi mai inganci.
Ƙungiyar Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan takwararta na ISWAP da dama yayin wani ƙazamin rikici da suka tafka ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno. Bayanai sun ce an kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 yayin harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ƙarƙashin jagorancin wani ta’adda mai suna Bakoura. Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Wata majiya ta shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, cewa yaƙin da aka fara tun da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Fabrairu ya haɗa da sansanonin ISWAP da ke Toumbun Gini...
“Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami’an tsaronmu na iya bakin kokarinsu.” BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same shi ba, duk da an tura masa sakon kar-ta-kwana game da lamarin. A kwanan nan dai rahotanni daga jihar ta Zamfara na cewa ana ci gaba da samun gagarumar nasara wajen yaƙi da ‘yan bindiga, sai ga shi yanzu wasu al’umma na bayyana cewa sabbin mahara na sake dawowa.
Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Kanada Tana Adawa Da Sin Don Neman Tausayin Amurka Wadda Ta Kan Ci Zarafinta
Ya ce Jihar Kogi ce ta gudanar da taron domin tana da shugabannin kungiyar a matsayin gwamna da mataimakinsa, inda ya ce Gwamna Usman Ododo na daya daga cikin jami’ansa a Jihar Neja sannan kuma mataimakin jami’in kungiyar malamai ta Nijeriya (NUT). Ya ce, “Don haka muna son mu yi wannan taron ne domin mu saurare ku don sanin abin da aka yi da abin da ba a yi yadda ya kamata ba, don haka mu dauka mu kai musu. “A gare mu, kamar zuwan gida ne. Muna so mu zo mu yi hulda da su don gano ko suna yin abubuwan da muke sukar wasu.” Kan haramta kungiyoyin kwadago a kwalejojin jihar da gwamnatin baya ta Yahaya Bello ta...
Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar. Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su. Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba...
Wasu magidanta da suka mallaki wani zakara (Ricco) jinsin Bantam daga Bourgoin-Jallieu a sashen Isère na kasar Faransa, sun karɓi sammaci domin bayyana a gaban kotu sakamakon korafin da wani makwabcinsu ya yi game da carar zakaran. Korafin da suka yi ya hada da, rashin barci saboda karar zakaran yake yi a yayin carar, kamar yadda mai gabatar da ƙara ya ambata, wanda ya gayyaci masu zakara (Ricco) zuwa kotu a watan Janairun 2025. Kasuwanci: Yadda matan Arewa ke samun arziki daga cikin gidajensu Gurgu mai mata huɗu da bai yarda da yin bara ba Mutumin, wanda ya fi son a sakaya sunansa, yana daya daga cikin makwabtan masu ikirarin cewa, carar zakaran ba za a iya jure ta ba...
Hukumar Zaɓe Mai ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin...
Jakadun kasashen larabawa da kuma na wasu kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa daga yankin Zirin gaza, saun kuma bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa. Shirin Trump na korar Falasdinawa daga Gaza dai ya fusata kasashen duniya musamman kasashen larabawa da musulmi, sun kuma ki amincewa da duk wani abu da zai sauyawa Falasdinawa kasarsu. Wannan yana faruwa ne bayan da HKI ta kasa kwace zirin Gazar a hannun mayakan Hamas da kawayenta na wasu kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin. Amurka tana son abinda yahudawan basu same shi a yaki ba Trump ya zo ya kwace shi ya mika masu ba tare da wata wahala...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji na 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a cikin kasashen kungiyar, ta BRICS wanda suke ganin Amurka ta mamaye al-amuran tattalin arziki a duniya. An kafa kungiyar BRICS ne a shekara 2009 kuma kasashen da suka fara kafata sune, Brazil, Russia, India, da kuma China, amma daga baya kungiyar ta kara fadada, inda kasashen Afirka ta kudu, Iran, Habasha, da kuma Hadaddiyar daular Larabawa. Bayan da kasar Rasha ta karbi shugabancin kungiyar na...
Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin yahudawan sun kashe Adel Abdel Bashkar a sansanin yan gudun hijira na Askar a kusa da garin Nablus bayan albarusai sun sameshi a kirjinsa. Labarin ya kara da cewa bayan an kai shi asbine sai yace ga garinku, ko kuma yayi shahada. Har’ila yau majiyar ta kara da cewa Falasdinawa matasa uku ne suka yi shahada a lokacinda sojojin yahudawan suka kai hari a sansanin...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta fara sana’a domin dogara da kanta kafin Allah Ya kawo mata aiki. Daga nan ne tunanin fara kasuwancin harkar girke-girke da hada lemo ya zo mata, har ta fara ‘M&S Mannah Wassalwa Kitchen’. Labarin Salma na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan...
Duk da kasancewar Malam Murtala Abubakar nakasasshe mara kafafu, amma bai lamunci yin bara ba. Hasali ma, ya rabu da matarsa ta fari saboda dabi’arta ta yin bara. Shekaru 50 da suka wuce Malam Muratala ya rasa kafafunsa, tun yana dan shekara bakwai a duniya. A haka ya ci gaba da rayuwarsa, inda a halin yanzu yake kula da iyalansa, mata hudu wadanda dukansu nakasassu ne da ’ya’yansu 15. A haka yake fadi-tashin daukar dawainiyarsu, domin tsare mutuncinsa, saboda ya yi imanin cewa, “Bara tana rage daraja da kimar mutum.” Wannan ne ma ya sa ya rabu da matarsa ta farko saboda dabi’ar bara. Rayuwar Malam Murtala, wanda a lokacin da yake dan shekara bakwai yake takawa da kafafunsa zuwa...
Gillis-Harry ya ce, “NNPC bai da wata mafita illa kawai ya rage farashin litar mai a gidajen mansa, ba zai yiwu mutane suna ganin akwai gidajen mai masu sauki kuma su je gidajen man NNPCL.” Kazalika, Ukadike ya ce, tun da ana samun bambancin farashin litar mai a tsakanin matatar mai dangote da kamfanin NNPCL, ba abun da ya rage wa mutane fiye da su je inda za su samu sauki. “Da yiwuwar kamfanin NNPCL zai rage farashin litar mai saboda akwai kokuwar farashin tsakaninsa da matatar man dangote. Da zarar matatar man dangote ta rage farashin litar mai, shi ma NNPC zai biyo baya,” ya shaida. Dalilin da ke janyo ko da matatar man dangote da NNPCL sun rage...
Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma. Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su. Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma. ...
Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula...
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin. Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar kudaden, za su iya chazar masu sayen kudaden. “Dole ne dilolin da su gabatar da rahotannin su ga sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, na kudaden da suka sayar ga masu hada-hadar musayar kudaden, inda su kuma masu hada-hadar musayar kudaden, dole ne su rinka gabatar da ribar da suka samu a kullum ta saye da sayar kudaden, ta hanyar amfani da tsarin cibiyoyin...
Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon. Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani da kakkausar murya ga kalamai da kuma matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ta hanyar halartar gagarumar zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran. Ayatullah Khatami ya kara da cewa: A yau daga mimbarin Juma’a da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yana tabbatar da cewa: Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci...
Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran, ba tare da batun soke jigilar jiragen saman Iran zuwa kasar Lebanon ba. Gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma’a ya sanar da cewa: An yi watsi da furucin wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu da suka ce, gwamnatin Lebanon ta hana tafiyar jiragen saman Iran guda biyu zuwa kasar Lebanon da suke tashi a ranakun Alhamis da Juma’a, don haka ofishin jakadancin Iran...

Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Cibiyar Ilimin Mata Ta Shirya Wa Sarakuna Da Malamai Taron Inganta Karatun Mata A Kaduna
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya. Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar. A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...