2025-03-20@17:48:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 838
«farashin man fetur»:
Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa. ‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’ Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus. Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin...
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani? Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a...
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da ikon rushe zaɓaɓɓun shugabanni na jiha. Bugu da ƙari, Sambauna ya caccaki yadda Gwamnatin Tinubu ke nuna bambanci wajen raba wa matasa tallafi. Ya ce: “Seyi Tinubu ya bayar da kayan abinci a Arewa a matsayin tallafi, amma a Kudu yana bayar da tallafin kuɗi domin mutane su dogara da kansu wajen bunƙasa kasuwanci. Wannan nuna bambanci ne da...
Dokta Saleh ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar, yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya. Har ila yau, a buƙaci a samu haɗin gwiwa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da zuwa asibiti don bincike da magani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
Wasu ‘yan tada ƙayar baya bakwai da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun miƙa wuya ga rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a Damasak da ke Jihar Borno tare da miƘa tarin makamai da kayan aiki. Kamar yadda Zagàzola Makama ya ambata wannan miƙa wuyan da waɗannan maharan suka yi ga sojojin da ke aiki ƙarƙashin sashe na 3 Monguno, na nuni da nasarar da aka samu wajen yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chadi. Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan ‘Yan Boko Haram ɗin da suka miƙa wuya sun haɗa da Malam Baba Ibrahim ɗan shekara 19, Malam Bamai Ali mai shekara 20, Malam Jundu Ali mai...
Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta. Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja A matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar. Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Me Ya Sa Aka Ayyana Dokar Ta-ɓaci? Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas. Shugaba Tinubu ya yanke...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis. Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun...

Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah. Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano. A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na zurfafa kallon al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha. Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta...
Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Dokta Nuhu Koko, ya bayyana cewa a Gwandu ne aka fi samun waɗana suka rasu, inda mutum 25 suka rasu, sai Jega da ke 16, sannan Aliero ke da mutum 14 da suka mutu. Yawancin waɗanda suka rasu sun ɗauka cewa zazzaɓin cizon sauro ne ke damunsu, wanda hakan ya sa ba su garzaya...
Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025. A cewar sanarwar mai Magana da aywun rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubukar Abdullahi ya bayyana cewa, a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda 10 a wata arangama da suka yi a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun. Ta ce an fara kai farmakin ne a jihar Katsina, inda sojoji suka kai farmakin a kan ‘yan ta’addan a babbar filin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara. “Hakan ya...
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13. A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa. Sanarwar ta bayyana cewa...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar. Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar mutane 653 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi biyar da suka hada da Aliero, Jega, Gwandu, Birnin Kebbi da Bunza. A cewarsa, samfurorin da aka aiko da kuma tabbatarwa daga cibiyar bincike, yanzu jihar ta san yadda take magance cututtukan sankarau. Ya kara da cewa, an aika samfurori 17 zuwa dakin gwaje-gwaje na kasa da kasa da ke Abuja...
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu. Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.” A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen zurfafa wannan alaka ita ce ta haduwa irin wannan da za mu ji ta bakin juna. “Ina sa ran jin ta bakinku kan abubuwan da kuke yi na karfafa hadin kan addini a tsakanin al’umma, damar ilimi da kuma damar yin aiki ga jama’ar ku. “Abin da Amurka za ta iya yi don haɓaka ƙarin alaƙa da kuma matakan da...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...

A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...

An Gudanar Da Tarukan Tattaunawa Na Kasa Da Kasa Masu Jigon “Sin A Yanayin Bazara” A Turkiya Da Colombia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar. Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya. A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF). Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar. Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.” Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa...
Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira. “Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen...
Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025. Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba. Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar. Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa...
Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal. Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki. Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144 Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Wakilin Aminiya ya ziyarci Fadar Gwamnatin, inda ya lura cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin. Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar. “Gwamna ya fice daga ciki,...
“Gwamna ya fice daga gidan, kuma muna jiran sabon shugaban riko ya iso. “An sauya duka jami’an tsaro, amma komai yana tafiya cikin kwanciyar hankali a yanzu,” in ji majiyar. A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu ba tare da wata matsala ba. A ranar Talata ne, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas, sakamakon rikicin siyasa da addabi jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki. A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin. A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba. Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na...
“Sun zo da tsakar dare ɗauke da bindigogi, suka tafi da mu, suka ɗaure mu, tare da barazana cewa idan ba mu bi umarninsu ba za su kashe mu,” in ji shi. Adamu, wanda yake fama da ciwo saboda dukan da aka yi masa, ya roƙi gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga. Samamen da aka kai ya biyo bayan wani hari da aka kai garin Yelwa a ranar 15 ga watan Maris, inda aka kashe mutane biyu, aka kuma sace wasu uku. Shugaban ayyuka na ‘yan bangar, Muniru Bello Abubakar, ya tabbatar da cewa ’yan bindiga na amfani da bayanan sirri daga mutanen cikin gari don samun bayani kan waɗanda za su sace...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci ɗaukacin Masarautun Kano guda huɗu da su fara shirye-shiryen Hawan Sallah da bisa al’ada aka saba domin ganin jama’a da maziyarta sun nishaɗantu a yayin bukukuwan Sallah na bana. Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin wani taron buɗa-baki da sarakunan gargajiya da aka yi a ɗakin taro na Ante Chamber da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Talata. Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Abba ya jaddada cewa al’ummar jihar sun ƙagara don ganin wannan al’ada ta sanya sabbin tufafi a lokacin bukukuwan Sallah, tare da tsayawa a kan tituna domin kallon sarakunansu a kan doki...
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai kuma wasu jiragen 13 da aka harba a yankin Oryol da kuma wasu 7 a samaniyar tekun Azorf. Sauran yankunan da sojojin Ukuraniya su ka harba wa makamai masu linzamin sun hada Tola, da Biryansk. Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na...
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar. Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar. An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar. ‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’ Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya...
Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC. Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri. Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu...
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara na Jihar Ribas. Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa. An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau “Saboda haka duk wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin dimokuraɗiyya wanda kuma ya keta haddin cin gashin kan gwamnatocin jihohi,” in ji shi. A kan haka ne Ƙungiyar Lauyoyin ta buƙaci Majalisar Dokoki ta...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin da take mayar da martani ga tambayar da wani dan jarida ya yi mata a taron manema labaru na yau 18 ga wata cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra’ila,kuma tana fatan dukkan bangarorin za su sa kaimi ga ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata, da kaucewa daukar duk wani mataki da zai ta’azzara lamarin, da hana afkuwar bala’in jin kai a mataki mai girma. Hukumomin lafiya da ke Gaza sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare daban-daban a zirin Gaza da...
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera ta hakimanci. Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani. Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi...
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar. Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya. Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar. Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria...
Kasar Sin na matukar adawa da haramta amfani da kirkirarriyar basira ta DeepSeek da gwamnatin Amurka ta yi a ranar Talata, biyo bayan rahoton da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar na cewa, ma’aikatar cinikayya ta Amurka ta haramtawa ma’aikata amfani da DeepSeek kan na’urorin da gwamnati ta samar musu. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana adawa da zuzuta batun tsaron kasa fiye da kima, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, cinikayya da fasaha. Mao ta kara da cewa, kasar Sin za ta kare hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
A yau Talata ce ake saran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump, kuma wannan shine zantawar shuwagabannin kasashen biyu tun shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kakakin Fadar Krimlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen zantawar shuwagabnnin biyu. Peskov ya kara da cewa tattaunawar tasu zai maida hankali ne kan yakin Ukraine da matsalolin da suke kewaye da yakin. Yau ita ce ranar da kasar Rasha ta hade yankin Cremear ga kasar Rasha, a shekara ta 2014. Kwace yankin dai ya jawo matsaloli da dama tsakanin Amurka da Rasha a lokacin.
HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne. Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren...
An shiga wata 11 da Gwamnatin Jihar Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmad Aliyu ta tuɓe rawanin wasu sarakuna da take ganin sun yi abin da bai dace ba na shiga siyasa. Tun bayan cire sarakunan, mutane sun yi tsammanin gwamnati za ta nada wadanda take muradi ne kai-tsaye domin su maye gurbin tubabbun sarakunan, amma shiru kamar ba wasu da ke jiran hukunci da sakayyar gwamnati mai ci. Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu Har yanzu gwamnati ba ta fito ta fadi dalilin rashin sake nada sababbin sarakunan ba domin ci gaba da wakilcin jama’a, ganin an bar garin kufai ba cikakken basarake. A baya da ma...
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya zuwa yanzu dai, Gwamna Fubara bai ce komai ba kan lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin San’aa da kuma sauran biranen kasar domin raya da tunawa da rana da aka yi yakin Badar, yana mai cea; hakan yana a matsayin wani sako ne zuwa Amurka da Isra’ila, kuma tabbas idan su ka ci gaba da kai wa Yemen hari, to muna da zabi na hanyoyin da za mu yi amfani da su domin dandana musu kudarsu. Sayyid Husi wanda ya gabatar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mallakar Muhalli na ɗaya daga cikin burin kowanne ɗan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Ƙananan ma’aikata da mafi ƙarancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar da su, ko tufatar da su ba, ballantana har su yi tunanin mallakar muhalli nasu na ƙashin kansu. Sai dai masana na bayyana cewa marasa karfin ma na iya mallakan nasu muhallin daidai ruwa daidai tsaki. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da mai ƙaramin ƙarfi zai...
Kakakin hukumar raya hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin (CIDCA), Li Ming, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau Litinin cewa, rage yawan tallafin kasashen waje da Amurka ta yi, da rage fiye da kashi 90 cikin 100 na ayyukan da take yi, sun sabawa alkawuran da ta dauka, da kuma nauyin da ke bisa wuyanta a karkashin tsarin MDD, kuma hakan wani yunkuri ne na ja da baya, wanda kasashen duniya ba sa goyon baya. Li Ming ya jaddada cewa, alkawarin da kasar Sin ta yi na kara yawan albarkatu ga hadin gwiwar ci gaban duniya, ba zai canza ba. Ya kara da cewa, ka’idojin kasar Sin na kin tsoma baki cikin...
“Dole ne mu ci gaba da bunkasa jiharmu, kuma an gina wadannan gidajen ne don habaka jiharmu. “Ga dukkan masu gidaje da ke wadannan jerin gidaje, ina sanar da su a fili, ko dai su koma wuraren da zama ko kuma a kwace,” in ji Gwamna Yusuf. Ya kuma bukaci wadanda ba za su iya komawa wuraren ba da su yi tunanin yiwuwar bayar da hayar gidajensu, yana mai jaddada kudirin gwamnati na ganin wuraren sun ci gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu na bana, masana’antar samar da kayayyaki na samun saurin bunkasa, inda ribar da kamfanoni da masana’antu da ke iya samun ribar da ta zarce dala miliyan 2.7 a duk shekara, ta karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, masana’antar ba da hidima ta fi samun bunkasuwa, inda alkaluman ci gabanta suka karu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin bara, kuma...
Al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin ganganmi a fadin kasar, inda suka lashi takobin tinkarar ta’addancin Amurka ta hanyar kara karfin soji, da hada karfi da karfe, da kuma abokan gaba shakat. Gangamin ya zo ne bayan da jagoran gwagwarmayar kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa kasar a shirye ta ke duk wata barazanar Amurka. “Ba mu tsoron kowa, kuma ba mu rusuna wa kowa sai Allah. Za mu fuskanci duk wani tashin hankali. ” inji shi “A shirye muke mu tunkari dukkan azzaluman duniya ba tare da wata fargaba ko tsoro ba. Abdul Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadi, kwana guda bayan da Amurka ta kai...
Ofishin kwamitin kolin JKS da na majalisar gudanarwar kasar Sin, sun sanar da kaddamar da sabon shiri game da tsare-tsaren musamman na bunkasa sayayya a kasar Sin, a gabar da kasar wadda ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya ke kara karkata ga mayar da kasuwannin gida ginshiki, kuma babban karfi na ingiza ci gaban tattalin arzikinta. Shirin wanda ofisoshin biyu suka yi hadakar sanar da shi a jiya Lahadi, ya kunshi dabarun bunkasa sayayya, da ingiza bukatun cikin gida a dukkanin sassa, da fadada karfin sayayya ta hanyar kara yawan kudaden shiga, da rage nauyin da al’umma ke fuskanta ta fuskar bukatun kudi. Kazalika, shirin na fatan ingiza karin bukatu ta hanyar samar da ingantattun hidimomin...
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa. Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu. Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi A cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi, ’yan majalisar sun zargin Gwamna Fubara da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma, wasiƙar ta ce Gwamna Fubara ya hana majalisar gudanar da aikinta, da kuma naɗa mutane a muƙaman gwamnati ba tare da tantancewa ba. Kazalika, tana tuhumar Gwamnan da ƙin biyan albashi da wasu alawus...
Wasa wasa dai Musulunci na dawowa gidansa wato Nijeriya ta Arewa ta hanyoyi iri-iri. Ba dai sai an nanata ba. Arewacin Nijeriya da ma sassa da dama a jamhuriyar Nijar da Ghana har ya zawa Senegal sassa ne na Musulunci inda ƴan mulkin mallaka na Ingila da Faransa suka yi iyakar ƙoƙarin su rusa shi. Ya ƙi ya bace, duk da yake an yi masa rotse. Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya Tarihi ya bayyana yadda wata ƙungiyar musulmi daga Mali ta zo Kano a ƙarni na sha biyar ta zauna ta fasa wucewa zuwa aikin Hajjin da ta fito yi. Waɗannan mutane da ake kira...
Shugaban kasar ta Amurka Donald Ttump ya kara yawan kasashen da ya sa wa takunkumin shiga cikin Amurka zuwa kasashe 43. Daga cikin kasashen da ya sa wa sharuddan shiga cikin kasar Amurka sun hada guda 11 da su ne; Somaliya, Sudan, da Libya. Sai kuma Afghanistan, Cuba, Iran, Korea Ta Arewa, Syria, Venezuela da kuma Yemen. A lokacin zangonsa na farko Trump matakin nasa ya ja hankalin duniya saboda yadda ya hana ‘yan hijira daga kasashen Iraki, Libya, Somaliya, Sudan da Yemen shiga cikin kasar. An kalubalanci matakin na shugaban kasar Amurka a wancan lokacin a kotu saboda yadda ya shafi mafi yawancin kasashen musulmi. Bayan da Joe Biden ya zama shugaban kasa ya soke wancan matakin na Donald...
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz ta kammala karatu a Makarantar Hartford Public High School da ke Hartford, a Jihar Connecticut, inda aka karama ta, har ma ta samu gurbin karatu a kwaleji, amma yanzu ta kai karar tsohuwar makarantarta saboda sakacinta. Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira Matashiyar mai shekara 19 tana zargin makarantar da ta...
Sojojin HKI sun ci gaba da keta hurumin yarjeniyan tsagaita budewa juna wata tsakaninta da Gaza inda a jiya Lahadi kadai ta kashe Falasdinwa 14 a wurare daban daban a yankin. Tashar talabijin ta Almayadden ta kasar Lebanon ta bayyana cewa yawan shahidai a kan tafarkin Kudus a Gaza ya kai 48,872 da kuma wadanda suka ji rauni tun fara yakin ya karu zuwa 112,032. Dan rahoton tashar al-mayadeen ya bayyana cewa a jiya Lahadi bafalasdiniya guda ta yi shahada a cikin gidanta a sansanin yan gudun hijira na Nusairat a lokacinda sojojin yahudawan suka bude wuta a kan gidanta. Rahoton ya kara da cewa wani jirgin yakin da ake sarrafa shi daga nesa ya bude wuta kan wasu Falasdinawa...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfani da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu. Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki daki kamar yadda...
Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika wato CORET, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, sun bayyana shirinsu na samar da ayyuka guda dubu uku ga matasa ta hanyar sarrafa madara a sarkar darajar madara a Jahohin Kaduna da Jigawa. Shugaban Shirin na CORET, Dr. Umar Hardo, ne ya bayyana hakan yayin taron horaswa da ƙungiyoyin haɗin kai Sha biyu da aka zaɓo wanda ya gudanar a yankin Ladduga dake ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Taron horaswar na tsawon kwanaki biyu ya haɗa shugabanni daga ƙungiyoyin kiwo na madara guda goma sha biyu, masu tara madara, da shugabannin al’umma. Wannan shiri da ECOWAS ta ɗauki nauyi, zai fara aiki gwaje...
Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan bukatun kiwon lafiya na kasashen nahiyar gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto Abiy Ahmed yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da daraktan hukumar ta CDC a birnin Adis Ababa a ranar Jumma’an da ta gabata. An kafa cibiyar yaki da cututtuka ta kungiyar tarayyar Afirka (CDC) ne, a shekara 2016, sannan ta fara aiki a shekara ta 2017 don kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar a nahiyar Afirka. Gwamnatin kasar China ce ta taimaka aka gina gine-gine cibiyar, aka kuma fara amfani da su a shekara ta 2023....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama. Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”...
Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke karkashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba. Haka kuma tuni Trump din ya soma daukar wasu matakai wadanda suka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
Mai Martaba Sarkin Kauru dake Jihar Kaduna Alhaji Zakari Ya’u Usman ya bukaci samun hadin kai da aiki tare kana da hakuri da juna tare da ɗaukar banbance banbance dake tsakanin al’umma a matsayin wata baiwa. Alhaji Zakari Ya’u II yayi wannan horonne lokacin da aka taru a fadarsa dake Kauru domin shan ruwan azumin Ramadan. Mai martaban ya bayyanawa wadanda suka taru domin wannan aikin lada na shekara shekara cewa, akwai bukatar yafiya da ‘yan uwantaka a wannan lokaci na Ramadan tare da godiya ga Allah da ya sake nuna mana wannan watan mai albarka. Alhaji Zakaria Ya’u Usman yace akwai bukatar sadaukarwa da mika wuya ga Allah da kankantar da kai tare da fahimtar cewa wannan banbanci...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibinta Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta. Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza. A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a...
12.Yadda a zahiranci abubuwa suke A shekarar 2006,Carol Dweck wani masanin yadda mutum mai hankali yake,ya san yadda halin mutum yace a cikin littafinsa mai suna “rayuwar mutum da yadda hankalinsa yake” da wasu halayen da aka sa suke a littafinta.” mai suna:The Psychology of Success ko kuma hanyoyin da ake bi ko amfani da su domin a samu dama ta cimma nasara.Kamar dai yadda tunanin Dweck ya ke,mutane wadanda suke da mabambantan halaye suna yi wa kaddarori a matsayin wani hazikanci ne ta bangaren ilim wato kokari wanda akan gane a farkon rayuwa,wanda irin hakan na sa a fuskanci wadansu tarnakai ko matsaloli da za a ga kamar ba za a iya maganinsu ba.Sai dai kuma ta wani hasashen...
Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X. Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi. Ministan ya kara da...
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci. Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara. Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata...
An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa An kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023, a cewar ’yan sandan Riverbank. Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016. Haka kuma a cewar shafinta na...
Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida. A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da...
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara atisayen tantance gwanintar harbi na shekarar 2025 daga ranar Litinin 17 zuwa 19 ga watan Maris a Barikin Yar Gaba da ke Dutse, Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 26 Armoured Brigade, Laftanar Uzoma Egwu-Ukpai, ya sanyawa hannu aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen tantance gwanintar harbi ana yi ne domin auna ƙwarewar jami’an soji wajen sarrafa makamai da ingancin harbinsu. Laftanar Uzoma Ukpai ya shawarci al’umma da kada su firgita yayin atisayen idan suka ga sojoji suna kai-komo ko suka ji karar harbi, musamman mutanen da ke zaune...
Ya kara bayanin cewar Jami’ar za ta dauki sahun dalibanta na farko wato shekarar karatu ta 2025, inda ya kara jaddada aniyar gwamnati ta bada damar samun yin karatu na ilimi mai zurfi tare da bunkasa shi. Ministan har ila yau ya ce zai taimaka wajen tabbatar da cewar Jami’ar ta samu nata kason daga Hukumar kula da ilimin manyan makaratun ta kasa, domin hakan zai taimakawa bunkasa Jami’ar cikin wani lokaci nan gaba. Ya ci gaban da bayanin “Zan tabbatar da cewar Jami’ar ta samu taimako na gidauniya kula da ilimi mai zurfi ta lamurran manyan makarantu ta samun kudade daga wurinta wannan shekarar. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga al’ummar Kudancin Kaduna, al’ummar Jihar Kaduna,...

Tsohon Firaministan Lebanon: Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba
Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya. A cikin...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci ta Falasdinu da ke da alaka da kungiyar gwagwarmayar. Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na toshe muryar Falasdinawa. Sanarwar da Hamas ta fitar ta kara da cewa, wannan shawarar toshe ‘yancin watsa labaru ne da kuma hakki na al’ummar Falasdinu na a ji muryarsu a duniya.” Hamas ta yi kira ga cibiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su yi Allah wadai da wannan shawarar, kuma kada su yi shiru dangane da cin zarafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai. Bisa shawarar...
’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya. Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata. ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Kudin hatsi irin su shinkafa da...
A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace. Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala. A ‘yan kwanakin nan, magoya bayan Manchester United sun ci gaba da nuna fushinsu kan iyalan Glazer, masu mallakar sama da kashi 70 na kulob ɗin. Har ila yau, Ratcliffe bai samu cikakken goyon baya daga ma’aikatan ƙungiyar ba tun bayan zuwansa a shekarar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ci gaba a ƙasar. Tinubu ya ce duk da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce, amma yana so a ƙara haƙuri domin akwai haske nan gaba. Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ruwaito Tinubu yana wannan furuci ne a ranar Juma’a, yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu...
Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi ta nuna rashin jin dadinta da wasu manufofi na Gwamnatin tarayya musamman ma irin nau’oin harajin da ake cirewa duk wata ya maida albashinsu ya kasance tamkar miyar da babu Gishiri bare Maggi ko kuma Daddawa, shi yasa karin da aka yi na mafi karancin albashi na Naira 70,000 ya zama tamkar tafiyar Kura ne inda take yin Gaba ta kuma koma Baya. Wannan bayanin ya fito ne bayan da aka kammala taron kwamitin zartarwa na kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi na 50 wanda aka yiu a Jami’ar Gwamnatin tarayya ta Otuoke, Jihar Bayelsa, inda kungiyar ta nuna damuwarta kan manyan lamurra wadanda suke damuwar jin dadin ‘yan kungiyarta,kamar yadda ake samun toge a albashi inda bai...
Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7. Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru. Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000. Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400. Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka....
Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
“ Zuba hannun jari a bangaren da ake sauke kaya a Tashohin Jiragen Ruwa da kara fadada hanyoyin layin Jiragen kasa, za su iya taimakawa wajen bunkasa aiki da kuma kara sanya gasa a ayyukan tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwa. A cewar Dantsoho Ya sanar da cewa, samar da kyakaywan yanayin kasuwanci a kasar nan na da alaka da kokari da kuma yanayin gasar da aka samar na kasa a Tashishin Jiragen Ruwan, inda ya yi nuni da cewa, wadannan abubuwan sun taimaka wajen samun musayar kudade, daidaita tattalin ardikin kasar, kara habaka kauswanci da kuma samun masu zuwa zuba hannun jari. Dantsoho ya godewa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola, bisa goyon bayan ada yake ci gaba...
Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani ɗan majalisar Amurka, Chris Smith, ya yi cewa ana tauye wa Kiristoci ’yancin addini a Najeriya. Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba su da alaƙa da addini, domin hare-haren ’yan ta’adda na shafar dukkanin Musulmi da Kiristoci. Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu Tuggar ya ce hare-haren da ake kai wa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ba sa ware mabiyan wani addini. Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake yaɗa rahotannin da ba su dace ba, waɗanda ka iya haddasa rarrabuwar kawuna a...
Ya kara da cewa bisa sashin 10.7 da aka sake nazarinsa a 2019, ya rage cajin daga N65 zuwa N35 kan kowace hada-hada. Sai dai ya bayyana cewa za a biya Naira 100 ga duk wanda aka cire na Naira 20,000 ga kwastomomi daga wasu bankunan da ke yin mu’amala da ATM a harabar bankin. Onobun ya jaddada cewa abokan hulda daga sauran bankunan da ke yin mu’amala da ATMs a wajen harabar bankin, manyan kantuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a, za a rika biyan su Naira 100 da karin N500. Majalisar a cikin kudurorin ta ta bukaci CBN da ya gaggauta dakatar da aiwatar da wannan manufa, har sai an yi huldar da ta dace da kwamitocin da...

Jumhuriyar Najer Ta Bukaci Tarayyar Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi A Kasar
Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Najer tana fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yemai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar. Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar. Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300. Wasu wadanda suka...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja Ya jaddada cewa kawai Kotun Ƙoli ce ke da ikon sauya hukuncin mayar da Sanusi kan karagar mulki. “Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke hukuncinta na baya ba. Kawai dai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe,” in ji Dederi yayin da yake magana...
Kudirin ya kuma nemi kafa wata hanyar warware takaddama don magance rikice-rikicen da suka shafi jam’iyyun siyasa, mambobinsu, ‘yan takara masu zaman kansu, da kuma kawance. Bugu da kari, ta tanadi hukunci kan keta haddi da bayar da shawarar gyara ga dokar zabe ta 2022 don cire rajistar jam’iyyun siyasa daga hukumar INEC. Bayan gabatar da shawarwari, an mika kudirin ga kwamitin majalisa mai kula da harkokin zabe da kwamitin jam’iyyun siyasa domin ci gaba da tattaunawa a kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja. Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa. “Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za...
Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan a harabar masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka na hana Falasdinawa shiga wurin mai tsarki. Sashen kula da masallacin da ke birnin al-Quds ya ce kimanin masu ibada 80,000 ne suka taru A daidai lokacin da ake fargabar ci gaba da tashin hankalin da gwamnatin Isra’ila ke yi ga mazauna yankin. Duk da wannan takunkumin, masu ibada sun yi ta tururuwa daga yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan don shiga wurin mai tsarki. Sojojin Isra’ila sun hana matasan Falasdinawa shiga daga Jenin da Tulkarm. Hamas ta yi Allah wadai da takunkumin Isra’ila a Masallacin Al-Aqsa
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci. Ya shigar da Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar NSCDC, da sauran hukumomin tsaro ƙara. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatar Dan Agundi, inda ta ce akwai hurumin shari’a a cikin ƙarar. Mai shari’a Abang ya bayyana cewa kotu dole ne ta yi adalci wajen yanke hukunci. Wannan hukunci yana nufin cewa dole ne dukkan ɓangarorin su ci gaba da zama yadda suke kafin Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci. Bugu da ƙari, kotu ta umarci Dan...
Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta dauki nauyin dalibai sama da 500 a wani mataki na tsara makomar matasa a fannin fasahar zamani. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin da kuma mika takardun shaidar karatu ga wadanda suka ci gajiyar shirin fasahar zamani na Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) a Jihar Jigawa. Malam Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafawa matasa ta hanyar kirkire-kirkire a fannin fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki. “A yau, mun kammala horar da dalibai 240 da suka koyi yadda za su bunkasa harkokinsu na kasuwanci don tabbatar da ci gaba mai dorewa,” in ji gwamnan. “Haka...
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci. Sanarwar da Kabiru Isah Jaafar ya fitar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ta bayyana cewa kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 50.3 sun lalace sakamakon gobara, yayin da aka ceto wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 180.3. Haka kuma, an ceto rayuwa mutane bakwai da daga gobarar. Sabon Kwamishinan ‘Yansanda Ya Kama Aiki A Kano ‘Yansanda Sun...