2025-02-28@16:57:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 505
«Gajerun Labarai»:
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu. Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana wa taron...
A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa....
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin...
Masu sharhi kan harkokin kudi a Cowry Asset Management suna tsammanin Naira za ta ci gaba da kasancewa kan yadda take a wannan makon, tare da hana matakan hana rugujewar ta a kasuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa...
Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi alkawarin horar da matasa da ke aikin noman alkama a karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba gonakin alkama a yankin. Ya yabawa Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr Muhammad Uba Builder bisa wannan shiri da ya bayyana a matsayin...
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta...
Ma’aikatar kula da muhallin halittu ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 24 ga wata, inda wani jami’inta ya nuna cewa, ingancin iska da muhallin kasar sun kyautatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta cimma burin magance gurbatar yanayi a shekara ta 2024....
Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci. Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta...

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan...
Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar. “Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita...
Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo....
Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin...
Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a...
A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da...
Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya...
Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda...
Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi. A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma...
Matakin Amurka Na Takaita Zuba Jari Zai Cutar Da Wasu Da Ita Karan Kanta

Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su
Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su
Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, Yunusa Umar, ya jagoranci mambobi fiye da 7,500 zuwa jam’iyyar PDP. Cikin waɗanda suka sauya sheka har da Shugaban Matasa na APC a yankin, Yusuf Inuwa Bora, da Sakatare mai kula da jin daɗin mambobi, Isah Zakaria. An karɓi waɗannan sabbin ‘yan jam’iyyar ne...
Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar...
Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
Amurka Ta Zama Jagorar Bata Ka’idoji Da Dokar Duniya Bisa Amfani Da Makamin Harajin Kwastam
Wata gobara ta tashi a ƙauyen Bukar da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno, ta yi ɓarna mai tarin yawa. Gobarar ta lalata gidaje, amfanin gona, da dabbobi na miliyoyin Naira, amma babu wanda ya rasa ransa. ’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano...
“Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.” Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa. Idris ya ƙara...
Shugaban Majalisar Wakilai, Dokta Abbas Tajudeen ya ce Kasafin Kuɗin Nijeriya na baɗi zai ba da damar kafa ƙarin makarantu na matakin Tarayya a mazaɓarsa ta Zariya. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara-shekara karo na 31 da 32 na ƙungiyar bunkasa ilimi ta Zariya, watau ZEDA da aka gudanar a Zariya....
Hukumomin da ke kula da wasannin kwallon kafa a kasar Ingila sun fara shirin fara amfani da fasahar tantance satar gida a karon farko a gasar cin kofin FA ta Ingila. A ranar Alhamis hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sanar da cewa za a yi amfani da fasahar a wasanni bakwai da za a...
Ma’aurata da ke da tazarar shekaru 45 sun shawo kan masu zolayarsu da batun kiwon lafiya don samun farin ciki na musamman a baya kuma sun ce sun ki jin kunyar waɗansu ba su fahimci alakar aurensu ba. Ma’auratan sun shawo kan matsalar da za ta iya shafan huldarsu da wadanda ke son raba aurensu...
Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar...
Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyar kafa karin makarantu a Zaria. Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya ce za a kafa karin makarantu a mazabar tarayya ta zaria a kasafin kudin shekarar 2026. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara karo na 31 da 32 na kungiyar bunkasa...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta...

Hamas, Da OIC Sun Yi Allawadai Da Dirar Mikiyan Da HKI Take Yi A Tulkaram Na Yankin Yamma Da Kogin Joirdan
Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da...

Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan
Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke...
Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla. Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda...
Saudiyya Za Ta Haramta Shan Giya Lokacin Gasar Kofin Duniya
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens (NSCDC), a Jihar Yobe, ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da satar kayayyakin lantarki, na’urorin sadarwa a jihar. Kwamandan rundunar, AS Dandaura, ya tabbatar da kamen a Damaturu, Babban Birnin jihar, inda ya ce an gano wuraren ajiya uku da ake amfani da su don ɓoye...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ƙarin kuɗin makarantar Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da kashi 120 cikin 100 ya zama dole domin tabbatar da ɗorewar ingancin ilimi a jami’ar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na manyan makarantu da hukumomin gwamnati, inda ya jaddada cewa kuɗaɗen makaranta na...
Kafin ya zama sanata, ya yi majalisar dokokin ta tarayya da ya wakilci mabazar Toro daga 2011 zuwa 2018. An shirya masa jana’iza da ƙarfe 1pm a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairum 2025 a Masallacin da ke kofar gidansa da ke Gwarimpa, Abuja. Cikakken labarin daga baya:
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki yankin. Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA. Taron ya samu halartar sarki Abdullah II...
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure. Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai...