2025-02-28@16:38:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 505
«Gajerun Labarai»:
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da...
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin...
A yau Jumma’a ne jirgin saman da kasar Sin ta kera samfurin AS700D mai amfani da makamashin lantarki ya kammala tashinsa na farko cikin nasara, wanda ya nuna sabon ci gaban da kasar ta samu a sashen samar da kayayyakin sufurin jiragen sama masu amfani da makamashi mai tsafta a fannin tattalin arzikin jirage masu...
Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin...
daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga. “A baya...
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan...
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta...
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar. Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba...
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci...
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man. “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma...
Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP,...
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza. Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito. Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin...
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan...
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram. An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis. ’Yan bindiga sun...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka...
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Lita 60,000
Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida. Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar. Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana...
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki...
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3 Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin...
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke...
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya yaba da irin hazakar da Ishiekwene ke da ita a fannin sharhi da nazari kan harkokin siyasa, tattalin arziki da halin da Nijeriya ke ciki. Shugaban ya yaba da gudummawar da ya ke bayarwa wajen bunkasa yanayin kafafen yada...
Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu. Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES). Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram...
Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an...
Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane...
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran. Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su...
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa...
Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar...
Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata. A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar. Ya kuma nuna jin...
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu...
’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu...