2025-04-09@22:34:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2564
«Kanwan»:
Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan. Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan...
Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa...
LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa...
Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya...
Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali. Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris....
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin...
A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi...
Hajiya Zainab ta kuma tuna da marigayi mijinta, Sam Nda-Isaiah, wanda ya kafa LEADERSHIP a shekarar 2004. “Tun shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya kafa wannan jarida ya shigo harkar wallafa da wani babban buri — Don Allah da kuma ƙasar nan. “Wannan buri har yanzu yana jagorantarmu, kuma da yardar Allah za mu...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin...
An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta....
Shugaban sojin ya ce za a kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’asa, kuma za a hukunta su. Haka kuma ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven, ya ce za su ƙarfafa haɗin...
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin....
Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu. Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U....
Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar. Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin...
Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar. Rahotanni sun ce...
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar...

Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin...
Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD...
A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine...
Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falaasidinawa mai yawa. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar ta mayar da martini ta hanyar...
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na...
Ambaliyar da aka samu sanadiyar mamakon ruwan sama ta kashe aƙalla mutum 33 a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. Ruwan saman kamar da bakin ƙwarya ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgar ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin...
Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China...

Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
Kazalika, a cewar kungiyar, matakin takaita fitar da nau’o’in sinadaran ba zai shafi kamfanoni masu bukatarsu ba, muddin ba sa gudanar da wasu ayyuka daka iya zama illa ga tsaron kasar Sin, da ikon mulkin kan kasar, ko moriyar ci gabanta. Har ila yau, matakan ba za su haifar da cikas ga daidaito da wanzuwar...
Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta...
Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar...
Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi. Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani....
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da...
Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi...
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari...
Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 —...
Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi...
Wani mamba na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya soki hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kai wa a kudancin kasar Lebanon da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai jaddada cewa Amurka ce ke da alhakin kai hare-haren wuce gona da iri na sahyoniyawan. A cewar Al-Mayadeen, mazauna kudancin...
Edwin Wagensfeld, mai tsattsauran ra’ayi mai tsattsauran ra’ayi kuma mai magana da yawun kungiyar Pegida ta kasar Holland, ya kona kur’ani a gaban zauren majalisa a birnin Amsterdam, a wani mataki na nuna kyama ga Musulunci, kuma wannan matakin ya haifar da fushin ‘yan siyasa da ‘yan kasar ta Holland. A cewar gidan talabijin na...
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da...
Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da...
Kwanan nan wani mai kiwon karnuka a Indiya ya biya Rupee miliyan 500 — kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 949 da dubu 481 da 589 domin sayen wani karen kerkeci na jinsin karen Shephard Caucasian, wanda hakan ya sa karen ya zama mafi tsada a duniya. Karen mai suna Cadabomb Okami, an bayar da...
Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac...
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren...
Aƙalla mutane 30 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun mutu a wani mummunan hari da kungiyar ‘yan sa kai ta cikin gari ta yi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru, jihar Zamfara. Kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana daga bayanan sirri, harin ya faru ne...
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama...
Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko....