2025-02-26@16:20:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 339

«tazaran haihuwa»:

    Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar. Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan...
    Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna...
    Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a...
    A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar...
    Mai yiwuwa Atletico Madrid za ta fara wasa da wannan zubin: Musso, Llorente, Gimenez, Witsel, Azpilicueta, Correa, Gallagher, Koke, Lino, Sorloth, Griezmann. Mai yiwuwa Getafe zata fara da wannan zubin: Letacek, Iglesias, Duarte, Alderete, Rico, Alena, Dakonam, Arambarri, Sola, Uche, Mayoral.
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar das shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa. Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar. Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...
    Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai  rabi da rabi, a wasu...
    Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin...
    Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan...
    A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin. Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su...
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin...
    Kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid ta zargi Manchester City da karfafa gwiwa ga daya daga cikin ‘yan wasanta, Juma Bah domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga Premier League da buga wasa. Dan wasan mai tsaron baya, ya sanar da kungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma...
    Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa...
    An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf...
    Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar. Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa,...
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan...
    Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
    Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
    Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu. A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya...
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu....
    A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen...
    ’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa  da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum...
    Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga...
    “Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai...
    Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
    Karamar Hukumar Birnin kudu ta jihar Jigawa ta bada tabbacin hada kai da duk wata hukuma ko kamfani dake da muradin cigaban yankin. Shugaban karamar hukumar, Dr. Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin lokacin da wakilan rukunin kamfanonin kasar Sin wato China suka ziyarce shi a ofishinsa. Yace karamar hukumar Birnin kudu tana sahun...
    Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
    Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi...
    Masu ɗibar man fetur daga wata tankar mai da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara da ke hana su farmaki. Bayan faduwar tankar a cikin dare man cikinta ya fara tsiyaya, inda motar ta kama da wuta a kan babbar hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a ranar Laraba. Faɗuwar motar ke da wuya wasu...
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa...
    An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce,...
    Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air...