2025-02-26@15:57:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 339
«tazaran haihuwa»:
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
A ɗaya bangaren, sojoji sun tabbatar da cewa suna ci gaba da neman Bello Turji, wanda ke jagorantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin. Turji ya tsere daga maɓoyarsa, amma jami’an tsaro sun ce ba za su daina nemansa ba har sai an kama shi. Sojojin sun tabbatar da cewa suna ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi...
Da yake jawabi a taron manema labarai ranar Talata a Yola a madadin Masarautar Fufore, Alkasum Abba, ya ce kafa sabbin Masarautu abu ne wanda sam bai da ce ba kuma an aiwatar da tsarin ba bisa ka’ida ba. Ya yi ikirarin cewa, sun yi iyakacin kokarinsu na neman tattaunawa da sulhu a kan...

Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...
Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar...
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Sha’aban na kalandar musulunci daga daren Laraba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a fadar, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya raba wa manema labarai a ranar Litinin....
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan Sha’aban a gobe Laraba 29 ga watan Janairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Rajab 1446AH. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare...
Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai...
Yanzu shekarar ta 2025 muke ciki, kuma matakin da duniya ke daukawa wajen gudanar da al’amura ya bambanta da shekaru goma da suka gabata. Amma abin takaici shi ne, wasu har yanzu sun nace ma tsoffin dabaru, suna ganin barazanar haraji da takunkumi na iya mamaye duniya, na san kun riga kun san inda na...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen...

Na’im Kassim Ya Dora Wa Amurka da Faransa da MDD alhakin Abinda Zai Faru Idan Isra’ila Ba Ta Janye Daga Labanon Ba
Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI. A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar...
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan...
A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP. ‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar...
Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a yankunansu domin samun ci gaba a jihar. Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin murnar cika shekaru 5 akan mulki da kuma murnar...
Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe. Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya,...
A kwanakin nan ne wani asibitin kula da dabbobi a kasar Turkiyya ya wallafa wani labari mai ratsa jiki na wata karya da ba ta da masauki ta ɗauki ɗanta da ya suma a bakinta ta ajiye shi a kofar asibitin kamar mai neman taimako. Idan ba don gajeran bidiyon da kyamarorin na’urar CCTV suka...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an...
Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar...
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da...
Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar. Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi,...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai...
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69...