2025-02-01@11:57:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 110

«birnin Tehran»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
    Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa. Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito. Jami’an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu. Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau’in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba,...
    Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025.   Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja, ya ce hakan ya nuna kwazon hukumar a karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na tallafa wa tattalin arzikin jihar.   Malam Saidu Bakuwai, ya ba da karin haske kan ayyukan hukumar da suka hada da alhakin duk wasu takardu da suka shafi filaye, tsarawa da bayar da takaddun kowane gida, sake tantancewa, daidaitawa, da kuma tsarin rajistar kadarorin.   Sauran su ne Gudanarwa da Rajista...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...
    Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.