2025-03-12@21:38:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 808

«jiragen sama da»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A lokacin ganawar ta su, Dantsoho ya shedawa Daraktar yin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ta Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa. Da take mayar da jawabi Daraktar Janar ta Cibiyar ta bayyana tawagar ta NPA shawarar ta kan yadda za a kara inganta ayyukan NPA, musamman a bangaren samar da saukin yin kasuwanci, domin a kara habaka gasar yin kasuwanci da kuma kara tara kudaden shiga. Kazalika, Hukumomin biyu, sun bayyana fatan kan hadakar a tsakaninsu, domin a samar da sauye-sauyen da a za su samar da sakamako mai kyau. Hukumar ta NPA, ita ce aka dorawa nauyin tafiyarwa da kuma tafiyar da ayyukan Tashoshin Jirgen Ruwan Kasar. Ana sa ran wannan hadakar a tsakanin NPA da PEBEC, za...
    Majalisar Wakilai na shirin kafa wata sabuwar hukuma da za ta karɓi ikon yin rajistar jam’iyyun siyasa daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta gabatar da wani sabon ƙudiri kan batun. Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, tare da Hon. Marcus Onobun daga Jihar Edo ne, suka gabatar da ƙudirin. Ƙudirin na neman kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta riƙa yi wa jam’iyyu rajista, kula da dokokinsu, da kuma tallafa musu. Har ila yau, ƙudirin na neman a kafa wata kotu ta musamman da za ta duba ƙorafe-ƙorafen da...
    Tsohon Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Dakta Doyin, Okupe, ya rasu. Dakta Doyin Okupe ya rasu ne bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Doyin Okupe ta wata sanarwa a safiyar Juma’a.  
    Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...
    Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada. A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”...
    Bangaren soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya ce a shirye yake kan komi ma, kuma zai ci gaba da kasancewa cikin “kyakyawan shiri”, yana mai jaddada cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake yaki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ba zai sa a sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su ba. Abu Ubaida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a faifan bidiyo a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa, abin da ‘yan mamaya suka kasa cimma ta hanyar “makamai da yaki” ba za a taba samun shi ba ta hanyar “barazana da yaudara ba.” Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da shugaban Amurka...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira. A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za a gudanar da taron a yammacin ranar Juma’a, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta bukaci taron ne domin jawo hankalin kungiyar OIC, a matsayinta na babbar kungiya a duniyar musulmi, kan batun da ya shafi al’ummar musulmi da kasashen musulmi. Shirin shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawan Gaza da kasarsu ta asali...
    Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Faransa biyo bayan kalaman Emmanuel Macron na baya-bayan nan game da kayyade makaman nukiliya. Moscow ta dauki wadannan kalamai a matsayin barazana kai tsaye, yayin da Paris ke kare matsayinta ta hanyar jaddada bukatar kare Turai, Wanda ya nuna yadda ake samun rashin jituwa sosai kan batun Ukraine. Moscow ta yi imanin cewa Emmanuel Macron, wanda ya yi Allah wadai da “tashin hankali” na Rasha yayin jawabinsa a yammacin Laraba, yana son “yakin (a Ukraine) ya ci gaba.” Ministan harkokin wajen Rasha ya yi la’akari da cewa kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya nuna yuwuwar kariyar Turai da laima ta nukiliya “barazana” ce ga Rasha. A sa’i daya kuma, Sergei...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya. A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi kan wannan zargi, yana mai cewa wannan maganar banza ce. A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, ya tunatar da cewa ita kanta kasar Birtaniya kwarariya ce wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe. A kwanakin baya ne sakataren tsaron Burtaniya Dan Jarvis ya gabatar da shawarar a gaban majalisar dokokin kasar cewa za a kara sa ido kan gwamnatin...
    Gwamnatin jihar Kebbi, ta kaddamar da rabon kayayyakin noman rani da kayan abinci na watan Ramadan ga manoma da al’ummar jihar, inda ta umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana sayar da kayan abinci da na aikin noma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon, gwamnan jihar, Kwamared Nasir Idris ya bayyana cewa, matsakaitan manoma 200,000 a fadin kananan hukumomin jihar 21 ne za su ci gajiyar shirin. Gwamnan ya bayyana cewa, samar da kayan aikin gona ga manoma zai taimaka wajen bunkasa samar da abinci a jihar. Ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da kuma jami’an gwamnati da ke da alhakin rabon kayayyakin, da su tabbatar da an yi adalcin wajen  rabon kayayyakin....
    Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar da amsa a nazarin, ya ragu. A cewar nazarin, kaso 62.9 na masu bayar da amsa sun yi Allah wadai da manufar sanya muradun Amurka gaba da komai, inda suka soki manufar suna cewa, ta yi watsi da hakkoki da muradun sauran kasashe. Adadin wadanda suka bayar da wannan amsa daga nahiyar Turai ya kai kaso 67.7. Baya ga haka, kaso 55.1 na masu bayar...
    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi. Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin...
    Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
    Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci jana’izar Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Hassan Jingir, a garin Jos. An gudanar da sallar jana’izar ne a ranar Alhamis a unguwar Anguwan Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 An sako ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Binuwai A cewar sakataren yaɗa labaran JIBWIS, Ahmad Ashiru, Sheikh Jingir ya rasu yana da shekara 70. Ya rasu a gidansa da ke Jos bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu ya bar mata biyu da yara sama da 40. Ga hotunan yadda aka yi jana’izar:
    Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.” Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy? Kwanakin baya...
    Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:55 na dare a ranar Laraba, inda rahotanni suka nuna cewa jami’an ‘yansanda sun kai ɗauki, suka kwashe ta zuwa Asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarta. NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Da Dillancin Ƙwayoyi A Kano Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Tiktok 2 Kan Yaɗa Kalaman Batsa A Kano An kama jami’an biyu, Nass Ridwan Usman mai shekaru 23 da Ismaila Yakubu mai shekaru 26, waɗanda ke aiki a shalƙwatar NDLEA a Kano. Har yanzu NDLEA ko ‘yansanda ba su fitar...
    Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya. Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida Wa Iqamatis Sunan (JIBWIS). Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani da makamin siyasa.
    Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya. Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida. Tun bayan da aka yi cacar baki a...
    Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba. Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Jami’ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih – Mahaifar shugaba Zelensky.   Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine.   Wannan hari na zuwa ne sa’o’i bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta daina musayar bayanan sirri da Ukraine — wanda haka zai kasance ƙalubale matuƙa ga Ukraine wajen iya daƙile hare-haren Rasha.   Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce masu aikin sa kai daga wata ƙungiyar bayar da agaji daga Amurka da Birtaniya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya.   Hakazalika, an kai wasu hare-haren...
    A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba. Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta...
    Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki.   Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi.     ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su.   Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
    An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki.   Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara.   Ya ce a lokacin azumi da ake tsananin zafi a hankali ruwan jiki yana raguwa.   A cewarsa karuwar cin ‘ya’yan itatuwa daban-daban zai yi matukar amfani ga musulmi mai azumi.   Farfesa Afolabi ya bayyana cewa a lokacin azumin watan Ramadan musulmi sun kaurace wa abinci da abin sha, tare da hana jikinsu cin abinci da suka saba.   Ya ba da shawarar a kara amfani...
    Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe.   Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin jihar kan rashin amincewa da rawar da gwamnatin tarayya ta taka, wanda hakan ya sanya ake yaudarar jama’a wajen ganin cewa tallafin na jiha ne kawai.   Jam’iyyar adawa ta ba da shawarar cewa yin shiru ya sa ayar tambaya game da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kayayyakin agaji.   Ta kuma yi zargin cewa sukar da Gwamnan ya yi a...
    An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna. Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe. Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata. Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024. An kama korarren jami’in tsaro da...
    Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar  a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya. Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika...
    Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia. Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar. Kafin haka dai masu fama da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai  har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai  ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Wani gini mai hawa biyu ya rufta a yankin Lekki da ke Jihar Legas wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu shida. Jami’an bayar da agaji daga hukumomin LASEMA da NEMA sun ceto waɗanda suka jikkata kuma an kai su Babban Asibitin Marina domin kula da lafiyarsu. Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Tun da farko, ’yan sanda sun ce an ceto mutum 14 daga wajen da ginin ya rufta. Sakataren hukumar LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa ana bincike don gano musabbabin rushewar ginin. “Zuwa yanzu mun gano gawarwakin mutum biyu daga...
    Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar. Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu...
    A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila (Shin Bet) ta amince da gazawarta wajen hana harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su. Ya ce, da hukumar ta Shin Bet ta yi wani abu daban a cikin shekarun da suka gabata kafin harin da kuma a daren da aka kai harin… da an kaucewa hakan. “A matsayina na shugaban hukumar, zan...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda  ba na son rai. A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta kan kaddamar da kiraye-kirayen bayar da tallafi don tara kudade da biyan Diya, ta yadda za a saki fursunonin da ake yanke musu hukunci bisa aikata laifukan da ba da gangan ba. Taron dai ya hada jami’ai da masu ba da agaji a Tehran babban birnin kasar da kuma garuruwa daban-daban na kasar duk shekara. Diya wani hakki ne da ake biya ga wanda aka...
    Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi. Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5. “Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da...
    Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi A ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba. Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci. Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu,...
    Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar. Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.” Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta. Martanin Akpabio Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa. A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata. Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru. Abin da Sanata Natasha...
    Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba. Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance. Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na siyasa ya samo asali ne daga yanayi da ya fi ƙarfinsu gaba ɗaya. “Gaskiya ni na yi imanin cewa ni da Kwankwaso ba mu da wata matsala ta zama tare a ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya. A duk abubuwan da suka faru, da ni da shi duk babu mai laifi,” inji shi. Da yake tsokaci kan lokacin da suka...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
    Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma  jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne. Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar...
    Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai  a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna. Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700. EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa. ’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan...
    Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ina mana lale barka da zuwan masoyi watan Ramadan. Da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan alheran da ke cikinsa kuma Ya sa mu zama daga cikin ’yantattun bayinsa, amin. Ramadan: Alherai goma ga Ma’aurata. 1. Gyaran aure: Ramadan lokaci ne na ibada da kyautata ibada. Aure da zamantakewar aure yana ɗaya daga cikin manyan ibadojin Addinin Musulunci. A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Yace, Aure rabin Addini ne. Don haka kamar yadda muke dagewa wajen ayyukan addini da gyaran alakar mu da Allah, to ya kamata ma’aurata suyi amfani...
    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana farin cikinsa akan wannan tarihi, inda yace abu mafi muhimmanci shi ne ganin cewar Arsenal na da babbar damar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe duk da cewar akwai jan aiki idan PSV ta ziyarci Arsenal a gidanta inji Arteta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
    Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”. Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran. Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayar da tallafin kudin da sun kai Riyal biliyan 40 ga kungiyoyin agaji da suke aiki domin ganin an saki frusunonin da su ka aikata laifuka ba cikin ganganci ba.  A kowace shekara  a cikin watan Ramadan mai alfarma kungiyoyin na agaji suna kaddamar da neman taimako saboda sakin fursunonin da su ka aikata laifuka ba a cikin ganganci ba. Ana amfani da kudaden ne wajen biyar  fansa da diyya ga wadanda fursunonin su ka yi wa illa. Biyan fansa din dai ana yinsa ne  maimakon zartar da hukunci na Kisasi. Watan azumin Ramadana da shi ne na 9 a  cikin kalandar musulunci yana da matsayin na musamman da ake...
    “Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”   Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma.   Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa.   Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar...
    A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
    Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.   “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal   Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”   A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin,  take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa  kuma...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green Horizon, Farfesa Muhammed Sabiu (SAN) ne ya jagoranci taron wanda shirin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta shirya. Tun da farko a jawabinsa na bude taron, Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Sarkin Fulani Hamceta Alhaji Aminu Lawal Bagiwa ya wakilta, ya ja hankalin mahalarta da su tsaya domin sanin abin da za a ilmantar da su kasancewarsu na shugabannin al’umma kuma na farko da ake kawo...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis. Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da...
      Yayin da al’ummar Musulmai  a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa.   A cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na gidauniyar, Abubakar Gambo Umar ya sanya wa hannu, ta jaddada bukatar kyautata dabi’u da wanzar da zaman lafiya da adalci a kasuwanci a lokacin azumi.   Gidauniyar ta yi kira ga malaman addini da su ci gaba da yada sakonnin tsoron Allah da hakuri da kaunar juna, domin karfafa darussan Ramadan na sabunta imani da hadin kan al’umma.   Hakazalika, gidauniyar ta...
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin  kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya  Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa;               “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83. Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.” Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi wannan kiran ne bayan wata maganan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya yi dangane da kasar Iran. Labarin ya kara da cewa, Hakan Fiddan ya bayyana cewa shirye-shiryen JMI a kasar Siriya masu rusa kasar ne, kafin juyin mulkin da Turkiyan ta dauki nauyinsa a baya-bayan nan a kasar Siriya. Ya ce: Fidan yana magana kan gagarumin taron Jana’izar Shahid Sayyid Hassan...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen  duniya. Volker Turk ya ce al-amura da suka shafi nuna wariya ne, mai yuwa su zama akasin haka nan gaba, bayan wadannan sauye sauye sun fara aiki. Wannan dai shi ne jawabi mai muhimmancin da wani jami'an MDD ya gabatar dangane da abubuwan da ke faruwa a sabuwar gwamnatin Amurka. Turk ya kuma...
    Haka kuma, an sake zaɓar Mojisola Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar bayan sauka daga matsayinta na kakakin majalisar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.” Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka”...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa. ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci. Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.  Amma daga bisanio ya zarge su da...
    Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kira matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin dake shiga Gaza a matsayin abin damuwa. Jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na katse taimakon da take baiwa Gaza, yana mai cewa abin takaici ne. A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya tuna cewa “Dokar kasa da kasa ta bayyana karara cewa dole ne a bar agajin jin kai ya shiga zirin Gaza.” Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da dama da kwararru kan kare hakkin bil adama sun yi gargadin cewa wannan mataki ya zama keta dokokin kasa da kasa da kuma...
    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin nasa, Macron ya ba da shawarar cewa kasashen Turai su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro da kashi 3 zuwa 3.5 na GDP don mayar da martani ga canje-canjen abubuwan da Washington ta sa a gaba. “Tsawon shekaru uku, Rashawa suna kashe kashi 10% na GDPn su a fannin tsaro; Don haka dole ne mu shirya don abin da ke gaba. »
    Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana. Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar. HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki Bayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana. Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa. Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta...
    A wani yunkuri na kawo karshen bautar da kananan yara a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO ) ta horas da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kuma yakar bautar da yara a aikin hakar ma’adanai. Kungiyar da ke kula da wurare hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta shirya taron ne da nufin ķarfafa guiwar masu ruwa da tsaki domin kawo karshen bautar da yara a wuraren hakar ma’adinai a jihohin Neja da Osun. Taron da ya gudanan daga ranar 18 zuwa 27 na watan Fabarirun 2025, wakilan gwamnati da kungiyoyin ma’aikata da shuwagabannin yankunan sun hallara, inda suka tattaun kan hanyoyin kawo karshen matsalar. Kazalika an bai wa mambobin kwamitin sanya ido kan ayyukan bautar da...
    Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne  na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma. A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do  tallafa wa kananan manoma...
    Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qais Al-Khaz’ali ya na karyata wannan labarin, ya kuma bayyana haka ne a wani shiri a tashar talabijin ta Al-Irakiyya na kasar ta Iraki a jiya Lahadi. Al-Khaz’ali ya kara da cewa makaman da suke karkashin kula na Hashdu sha’abi suna karkashin kula mai kyau, don haka babu tsaron cewa za’a yi amfani da su a inda bai dace ba. Ya kuma kara da cewa, tsarin tsaro na kasar ta Iraki yana da matukar muhimmanci garemu. Sannan ya kammala da cewa kwance damarar dakarun Hashdu Ashabi zagon kasa...
    Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa. Banda haka zai kyautata yanda jirage zasu sarrafa makamashin jirgin. Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da  injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin. Banda haka sabon...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar. Bayanan da ake buƙata sun hada da: Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan 1- Ƙasar mutum: Ta asali...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar. Bayanan da ake buƙata sun hada da: Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan 1- Ƙasar mutum: Ta asali...
    Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai. Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki. Rundunar ta bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida daga “TERROFOR ABUJA” wanda wakilinmu ya yi katarin samu a ranar Lahadi. Takardar ta fito a yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace. A kan haka ne Kwamitin Majalisar...
    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a ci gaba da yaki. Sergey Lavro ya kuma ce; tunanin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa Ukiraniya wauta ce. Lavrov ya bayyana shugaban kasar Ukiraniya Zelenskiy  da cewa dan Nazi ne, wanda ya ha’inci al’ummarsa.”
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya. Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.” Dukkanin wadannan bayanan suna cikin al’kur’ani mai girma. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan  zamanin da...
    ‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma faduwar darajar kudin kasar. Hemmati ya rasa kuri’ar amincewa a zaman majalisar na wannan Lahadi inda ‘yan majalisa 182 daga cikin 273 suka kada kuri’ar tsige shi. ‘Yan majalisa tamanin da tara ne suka bukaci ya ci gaba da zama a kan mukaminsa. A yayin Zaman ministan da kansa da shugaban kasar Masoud Pezeshkian sun halarci wurin, yayin da kuma ‘yan majalisar kan batun kudurin, amma dai kudirin ya wuce bayan samun rinjayen amincewa da shi. Shugaba Pezeshkian ya kare Hemmati, tsohon gwamnan babban bankin kasar Iran, ya kuma ce kasar na cikin yakin tattalin...
    Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila lamba da ta dakatar da matakin da ta dauka na yunkurin halaka mutane fiye da miliyan 2, inda ta kara da cewa, bayanin  Netanyahu dangane da tsawaita matakin farko wani yunkuri ne na kaucewa yarjejeniyar, da kuma kaucewa shiga tattaunawa a mataki na biyu. Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Isra’ila ta sanar da dakatar da duk...
    Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su. Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da...
    Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan kasar Burtania Keir Starmer, wanda ya yaba masa kan yadda ya tsayawa kasarsa da kuma kasashen turai a gaban shugaban Amurka Donal Trump da mataimakinsa a ranar jumma’an da ta gabata. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shuwagabannin biyu, wato Trump da kuma Zeleski don kwantar da hankali. A yau Lahadi ce za’a gudanar da taro na musamman...
    Rundunar Basij a yankin kudu maso gabacin kasar Iran ta bada sanarwan shahadar dakarunta guda biyu a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran, ya nakalto rundunar IRGC na yankin ya na bada sanarwan shahadar Hojjatoleslam Sadeq Mahmoudi da kuma Milad Damankesh a lokacinda suke komawa gida daga wurin aiki a cikin wata mota tasu. Labarin ya kara da cewa shahidan biyu sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda wasu yan ta’adda suka bude wuta a kan motarsu a lokacinda suke wucewa a wata unguwa zuwa gidajensu. Lardin Sitan Baluchistan wanda ke kan iyaka da kasar Pakistan dai ya dade yana fada da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke shigowa kasar daga kasar Pakistan, wadanda kuma suke samun taimako...
    A wani bidiyo mai ban mamaki da Hukumar Kashe Gobara ta yankin Tulsa da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna yadda wani kare ya yi sanadin tashin wuta a wani gida ta hanyar tauna fakitin batirin Lithium. Hukuma ta kama karen bayan gano hakan a bidiyon mai ban mamaki, wanda ya nuna shi yana tauna fakitin batirin lithium-ion wanda mai shi ya bari. Ban fitar da ran lashe Premier League na bana ba — Arteta Ta ina Kungiyar Hizbullah ke samun kuɗaɗenta? Bayan dan lokaci da fara taunawa, baturin ya fara tarwatsin wuta, sannan ya yi bindiga, lamarin da ya sa karen da wata kyanwa da ke kwana a kusa da gidan tserewa don tsira da rayukansu. An yi...
    Mikel Arteta ya ce, Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar bana, ba kamar yadda ake hasashen Liverpool ba. A ranar Laraba Gunners, wadda take da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool za ta fafata da Nottingham Forest a wasan mako na 27 a Premier League. Ta ina Kungiyar Hizbullah ke samun kuɗaɗenta? An kama ɓarayin waya a Kano A ranar Lahadin makon da ya gabata, Liverpool ta yi nasara a kan Manchester City da 2-0 a Etihad, bayan Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 ranar Asabar a Emirates ta hannun West Ham. Bayan wasan na West Ham Mikel Arteta ya zargi ‘yan wasan da rashin sa ƙwazo a fafatawar, bayan Gunners shafe kaka 21 rabon ta...
    Hanyar da ƙungiyar mayakan Hizbulla ta Lebanon ke samun kuɗaɗenta na sake fuskantar sabbin nazari, bayan wani harin sama da Israi’la ta kai a ƙarshen shekarar da ta gabata kan wata ƙungiyar hada-hadar kuɗi da ke da alaƙa da ƙungiyar. Ƙungiyar Hizbulla ita ce runduna mafi karfi a Lebanon, kuma jam’iyyar siyasa ce na musulmai ’yan Shia mai karfin faɗa a ji. An kama ɓarayin waya a Kano Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa Ƙungiyar na da karfi a majalisar Lebanon da gwamnati. Isra’ila da wasu ƙasashen Yamma da dama sun ayyana Hizbulla a matsayin kungiyar ta’addanci. Ƙungiyar ta shahara ne a shekarun 1980 domin adawa da Isra’ila, wanda dakarunta su ka mamaye Kudancin Lebanon...
    Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira. Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa. Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967. A ranar Talata...
    Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu’o’i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna. Malaman sun gudanar da addu’o’in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin Malaman yankin. Sakatariyar ilimi ta karamar hukumar Zaria, Dr Hassana Lawal ta shedawa manema labaru lokacin addu’o’in a zaria cewa a kalla Malaman makarantun firamare 2,225 ne suka amfana da tallafin kayan abinci domin gudanar da azumin watan Ramadan. A cewar ta,kayan abincin sun hada da kilo 25 na shinkafa da lita 4 na man gyada da fakitin tafiya da kuma kilo 10 na buhun...
    Wani jami’in ya ce yarjejejeniyar za ta ba da dama ga Zelenskyy da Trump su tattauna batun ci gaba da bayar da tallafin soji ga Ukraine, dalilin da ya sa Kyib ke son kammala yarjejeniyar. Trump ya kwatanta wannan matsaya da aka cimma a matsayin “babbar yarjejeniyar,” wacce za ta kai ta tiriliyan na daloli. A wani labarin kuma, Kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kai wa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutum 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi mara matuki kusa da birnin Kyib. Gagarumin ruwan wutar da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai cikin dare sun hallaka mutum 2 a...
    Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in ji shi kamar yadda ya bayyana a hirarsa da Fox News. Sai dai ya bayyana cewa musayar yawun ba ta dace ba, sannan ya kara da cewa dangantakar da ke tsakaninsa da Trump za ta gyaru. Tunda farko dai an soke taron manema labarai da aka shirya yi a fadar White House a jiya Juma’a, inda shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza. Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da...
    Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. » Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga...
    Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza. “Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da kayan aikin soji zuwa Isra’ila amfani da tashoshin jiragen ruwanmu; kamar yadda,” Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Firayim Ministan Malaysia Anwar Ibrahim da Shugaban Colombia Gustavo Petro suka rubuta a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mujallar harkokin waje ta buga a wannan makon. Sun jaddada cewa yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya fallasa gazawar tsarin kasa da kasa, tare da yin...
    Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya. Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma. HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Bayanin rasuwar Sarkin Sasa yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ɗan Masanin Sasa, Alhaji Kasim Ado Yaro ya raba wa manema labarai a ranar Asabar. Ɗan Masanin na Sasa ya ce Alhaji Maiyasin ya rasu ne a yau Asabar bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Ibadan. Sarkin Sasa wanda kuma yake riƙe da muƙamin...