2025-03-25@15:46:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2471

«kare hakkin dan Adam»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas? Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar. Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar. Tun bayan ɗaukar wannan mataki,...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara ta Farisa a yammacin wannan Alhamis. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada bukatar gwamnati da al’ummar kasar su ci gaba da zuba jari don karfafa azamarsu wajen tunkarar takunkumai na zalunci da masu girman kai na duniya suka kakaba ma kasar. Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa samar da kayayyaki na samun bunkasuwa ne idan aka ba da tallafin jari mai karfi. Jagoran ya kuma...
    Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...
    Dakarun Falasdinawa sun mayar da martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula bayan sake dawo da yakin Isra’ila a kan al’ummar Gaza, inda suka harba rokoki zuwa Tel Aviv. Al-Qassam Brigades, reshen soji na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas, ta sanar a wannan  Alhamis cewa, ta yi ruwan makamai masu linzami samfurin M90 a kan birnin Tel Aviv, a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi kan fararen hula a zirin Gaza. Sojojin mamaya na Isra’ila sun tabbatar da cewa sun gano wasu rokoki guda uku da aka harba daga Gaza zuwa tsakiyar Falasdinu da suka mamaye, tare da jin karar makamai a sararin samniyar Tel Aviv, Gush Dan, da...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
    Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki. Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro. ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal. Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan. A yanzu haka yana ganawar sirri...
    Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, rundunar ta yi matukar jimamin hatsarin motar da ya afku a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin karfe 6:58 na yamma kafin gadar Nyanya. Ta kuma ce, ofishin hukumar na Karu ya samu...
    Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta. Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja A matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar. Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Me Ya Sa Aka Ayyana Dokar Ta-ɓaci? Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas. Shugaba Tinubu ya yanke...
    A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su: Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul...
    A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su: Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul...
    Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
    Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis. Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun...
    Sojojin kasar Yeman sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tashar jiragen sama ta Bengerion a birnin Tel’aviv na HKI a daren jiya laraba don tallafawa falasdinawa a gaza wadanda sojojin HKI suke kashewa bayan yi masu kofar rago ta shigo da abinci da abinsha cikin yankin na kimani wata guda. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgedia Janar Yahya Saree, kakakin sojojin kasar na fadar haka a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa sojojin sun yi amfani da makami mai linzami samfurin Falasdin-2 mai saurin fiye da saurin sauti, wato Hypersonic don kai wannan harin. Tashar jiragen sama mafi girma a HKI dai ita ce ta Bengerion dake tazarar kilomita 20 daga...
    Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a  jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
    A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan.   Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka.   Bayan haka, sojojin sun ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza bakwai, mata 23, da kananan yara 54 da aka tsare a sansanonin ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
      Ƙungiyar bada agaji ta Civil defence a zirin Gaza ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai cikin dare sun yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 50 ciki harda yara ƙanana.   Hamas wadda zirin Gaza ke ƙarƙashin ikonta ta ce ta yi alla wadai da farmaki ta kasa na sojoji Isra’ila kuma ta bayyana shi a matsayin abinda ya saɓawa yajejeniyar tsagaita wuta na watanni biyu.   Rahotanni sun ce hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar Litinin wanda ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da Hamas, sun shafi wata makaranta da ake tsugunar da waɗanda suka rasa muhalansu.   Tun da farko Ministan tsaron Isra’ila, Isreal Katz ya gargaɗi almummar Gaza akan cewa za a lalata...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.   Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano.   A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na zurfafa kallon al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha.   Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta...
    Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Dokta Nuhu Koko, ya bayyana cewa a Gwandu ne aka fi samun waɗana suka rasu, inda mutum 25 suka rasu, sai Jega da ke 16, sannan Aliero ke da mutum 14 da suka mutu. Yawancin waɗanda suka rasu sun ɗauka cewa zazzaɓin cizon sauro ne ke damunsu, wanda hakan ya sa ba su garzaya...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin, da yadda ake gaggauta karewa da amfani da kayayyakin al’adu na tarihi da aiwatar da ra’ayin dunkulewar al’umomin Sinawa. Lambun renon furanni mai aiki da fasahar zamani na Lijiang na da fadin hekta 73.3, wanda ya hada aikin shuka da sufurin furanni da yawon bude ido tare, kuma ya habaka aikinsa zuwa harhada man furanni da samar da busassun furanni da sarrafa abinci mai hade...
    Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya sha alwashin yin aiki da gaskiya domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi.   CP Bakori ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai Kano.   CP Bakori, wanda kwanan nan ya karbi mukamin kwamishinan ‘yan sanda na 47 a jihar, ya ce daga cikin abubuwan da ya sa a gaba sun hada da magance ‘yan daba da kuma laifuka.   CP Bakori ya bayyana matsalar ‘yan daba, fadan daban, satar wayar hannu, da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.   Sabon Kwamishinan ya jaddada muhimmancin aikin ‘yan sandan al’umma, da nufin karfafa alaka tsakanin jami’an tsaro da jama’a.   Nadin na...
    Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025.   A cewar sanarwar mai Magana da aywun rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubukar Abdullahi ya bayyana cewa, a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda 10 a wata arangama da suka yi a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun.   Ta ce an fara kai farmakin ne a jihar Katsina, inda sojoji suka kai farmakin a kan ‘yan ta’addan a babbar filin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara.   “Hakan ya...
    Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.   A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13.   A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.   Sanarwar ta bayyana cewa...
    An dakile fashewar wata babbar tankar mai a Sokoto bayan da jami’an tsaro da jami’an kwana-kwana da masu bayar da agajin gaggawa suka yi gaggawar kai dauki bayan da tankar ta kife a hanyar Gagi-Nakasari a karamar hukumar Sokoto ta Kudu.   Wani shaidan gani da ido, Magaji Shanono ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa tankar mai dauke da lita dubu arba’in da biyar na man fetur, ta wuntsila ne a lokacin da take kokarin shiga shatatalen Nakasari, inda ta zubar da mai.   Duk da cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sakataren gwamnatin jihar Sokoto Muhammad Bello Sifawa ya halarci wurin da lamarin ya faru, domin ganin abin da...
    Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar.   Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar mutane 653 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi biyar da suka hada da Aliero, Jega, Gwandu, Birnin Kebbi da Bunza.   A cewarsa, samfurorin da aka aiko da kuma tabbatarwa daga cibiyar bincike, yanzu jihar ta san yadda take magance cututtukan sankarau.   Ya kara da cewa, an aika samfurori 17 zuwa dakin gwaje-gwaje na kasa da kasa da ke Abuja...
    Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu.   Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.”   A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen zurfafa wannan alaka ita ce ta haduwa irin wannan da za mu ji ta bakin juna.   “Ina sa ran jin ta bakinku kan abubuwan da kuke yi na karfafa hadin kan addini a tsakanin al’umma, damar ilimi da kuma damar yin aiki ga jama’ar ku.   “Abin da Amurka za ta iya yi don haɓaka ƙarin alaƙa da kuma matakan da...
    Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.   Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar.   “Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki...
    Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma  Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa. Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI. Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar...
    A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
    Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka. Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All… Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967. Inda yahudawan suka mamaye har da gabacin birnin Qudus sannan sun ginawa yahudawa...
    Asbitoci a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya wadanda suka hada da Asbitin kasa da kuma na Asokoro duk a ciki suke da wadanda suka ji rauni, ko sun mutu bayan da wata motar daukar gas ta yi hatsari a kan gadar Karu a tsakiyar birnin Abuja a jiya Laraba da misalign karfe 7:14 na yamma. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar muta ne 6 sannan wasu da dama sun ji rauni sanadiyyar hatsarin. Labarin ya nakalto Mr Mark Nyam mai kula da al-amuran gaggawa na hukumar NEMA ta kasa ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a lokacinda direban motar daukar gas ya burma cikin wasu ababen hawa a kan gadar Karu...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako. Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin. “Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe. “Sun tilasta Shugaban Kasuwa...
    Shugaban kwamiti na musamman dangane da yaki a Ukrai ya bayyana cewa kasar Rasha ta aikata laifukan yaki a yakin da take fafatawa a kasar Ukraine shekaru uku da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai, Africa News’ ya nakalto Erik Mose ya na fadar haka a taron kwamitin da yake jagoranra danagen da yaki a Ukraine a birnin Geneva a jiya Laraba. Mose a fadawa kwamitin mai mutane 47 kan cewa, ya sami shaidu wadanda suke tabbatar da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatin kasar Rasha ta azabtar da wasu yan kasar  Ukraine wadanda ta kama a yankuna guda 3 na Ukraine da ta kwace, kuma jami’an tsaron rasha sun azabtar da su, wasu kuma an...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyan sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari. Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi. Domin sauke...
    Alakar tattalin arziki da cinikayya bisa daidaito da aminci kuma mai dorewa tsakanin Sin da Amurka ta dace da muhimman muradun kasashen biyu, kuma za ta amfanar da kamfanoni a duk duniya, a cewar mataimakin ministan cinikayya Wang Shouwen yayin wata ganawa da Ramon Laguarta, shugaban kamfanin PepsiCo a ranar Talata. Da yake karin haske kan yadda kasar Sin ke da karfin gwiwar cimma burinta na bunkasa tattalin arzikinta na shekarar 2025 da aka gabatar a cikin rahoton aikin gwamnati, Wang, kuma wakilin harkokin cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin, ya bayyana cewa, wasu jerin tsare-tsare da kasar ta bullo da su na fadada bukatun cikin gida, da sa kaimi ga inganta tsare-tsaren yin sayayya za su samar...
    A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar. Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga. Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar...
    LEADERSHIP ta tattaro cewa, kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan. An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi. A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a hanyar Karu zuwa Nyanya dake birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da wata mummunar gobara da ta rutsa da motoci da dama, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yammacin ranar Laraba. Har zuwa yanzu  dai ba a tantance musabbabin fashewar tankar man ba. Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar. Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya. A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane 970 cikin sa’o’i 48. Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kaddamar a ranar Talata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 970. Wasu rahotanni na daban ce mutane 356 ne suka mutu a harin da aka kai ta sama, a cikin sa’a huda sannan akalla Falasdinawa 1,000 ne suka samu raunuka. Wani...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ta yi kakkausar suka ga sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai bayyana su a matsayin “ci gaba da kisan kiyashi da share wata al’umma a yankin da aka yi wa kawanya. Baghaei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i bayan harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara. Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ke da alhakin kashe-kashen da ake yi a Gaza, yana mai cewa, ana kai hare-haren na Isra’ila ne da tare da goyan bayan Washington. Baghaei ya kuma yi kira ga...
    Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan yankin Falasdinu. Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun karbe iko tare da fadada shi zuwa tsakiyar hanyar Netzarim, da nufin fadada yankin tsaro da samar da wani bangare na raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza. A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargadin karshe ga Falasdinawa a zirin Gaza, inda ya bukaci da su sako Isra’ilawa da suke garkuwa da su, su kuma kawar da kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa. “Idan ba a sako dukkan mutanen Isra’ila da aka yi...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma  “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network. Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa...
    Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF). Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar. Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.” Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantad da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar  Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman Shugaban Kasa sun halarci wannan gajeren bikin rantsuwar da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba. Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers a ranar Talata, 18 ga Maris, domin magance rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar, duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke. A yayin ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa halin rashin tsaro da matsin lamba...
    Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, har mun kawo ga goman ƙarshe wanda shi ne dama ta ƙarshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikon alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya. Ya ku masoya! Goman ƙarshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tserereniya a cikinta. Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa DAGA LARABA: Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al’ada Lokaci ne da wanda ya yi sakaci yake ƙara ƙwazo a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abota Lahira da ma’abota duniya. Da yawa masu huɗuba sun...
    Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira. “Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen...
    Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025. Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba. Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar. Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas. An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba. Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas  Naɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar. Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida. Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba,...
    Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi. Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana. Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas  Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka. “Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira. “Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar. Kamfanin Dangote...
    Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal. Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki. Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144 Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Wakilin Aminiya ya ziyarci Fadar Gwamnatin, inda ya lura cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin. Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar. “Gwamna ya fice daga ciki,...
    Wani mazaunin yankin ya koka da yadda ‘yan bindiga ke yawan kai hare-hare a waɗannan wurare, lamarin da ya sa jama’a ke cikin fargaba. A Farin-Shinge, mazauna yankin sun nuna koka kan hare-haren da ke ci gaba da faruwa, inda suka roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin kuma ya ce za su binciki lamarin. Sai dai, har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga ‘yansanda ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki. A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke  Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin.   A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba. Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na...
    Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa yake yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai yake yi. Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba. Ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba. Ban ce ina tarbiyyantarwa ba. “Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi ne....
    Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci ɗaukacin Masarautun Kano guda huɗu da su fara shirye-shiryen Hawan Sallah da bisa al’ada aka saba domin ganin jama’a da maziyarta sun nishaɗantu a yayin bukukuwan Sallah na bana. Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin wani taron buɗa-baki da sarakunan gargajiya da aka yi a ɗakin taro na Ante Chamber da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Talata. Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Abba ya jaddada cewa al’ummar jihar sun ƙagara don ganin wannan al’ada ta sanya sabbin tufafi a lokacin bukukuwan Sallah, tare da tsayawa a kan tituna domin kallon sarakunansu a kan doki...
    MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400.  Wakilin kasar Rasha a MDD  ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada cewa; “  Wajibi ne ga kwamitin tsaro ya yi duk abinda zai iya yi, domin sake tsayar da wutar yaki, bai kuma kamata a ce an sake maimaita kurakuren baya ba. Shi kuwa wakilin kasar Aljeriya a MDD, ya bayyana ya zargi HKI da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, yana mai jaddada cewa; Wannan lokaci ne da hukunta masu laifi, domin babu wanda...
     Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Sojojin Amurka suna da shirin kai hare-hare ta kasa a cikin yankin Gaza. Jaridar “Wall Street Journal” ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya za su ci gaba da zama a yankunan da su ka shiga a cikin Gaza, sannan kuma su kai wasu sabbin hare-hare ta kasa.
    Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai kuma wasu jiragen 13 da aka harba a yankin Oryol da kuma wasu 7 a samaniyar tekun Azorf. Sauran yankunan da sojojin Ukuraniya su ka harba wa makamai masu linzamin sun hada  Tola, da Biryansk. Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na...
    Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Yemen, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari. Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ne a garin Lerneb mai nisan kilo mita 50 daga birnin Timbuktu, a ranar Litinin da ta gabata kuma bayan mutane 18 da su ka kwanta dama, wasu 7 sun jikkata. Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana abinda ya faru da cewa; “Dabbanci” ne irin na zamanin jahiliyya. Sai dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali sun wallafa a shafinsu na X cewa; sun kai harin ne...
    Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar. Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar. An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar...
    Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka. Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar. ‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’ Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya...
    Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC. Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri. Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu...
    Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.   WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga fitaccen marubuci kuma masanin adabi, Farfesa Wole Soyinka, cibiya ce mai zaman kanta da ke amfani da binciken ƙwaƙwaf a aikin jarida domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta tsarin shugabanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Ya ƙara da cewa rikicin da ke faruwa a yankin Neja Delta a ƙarƙashin shugabancin Tinubu ya rusa zaman lafiyan da aka samu a zamanin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua. Atiku ya jaddada cewa wannan ba batun tsaro ba ne, illa dai wata hanyar wasa da siyasa tsakanin masu goyon bayan Tinubu da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara. Ya buƙaci ‘yan Nijeriya su yi Allah-wadai da wannan mataki da ya kira hari kan dimokuraɗiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban na kurdawa a Syira Hikmat al-Hijri ya soki halayyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar Syria, tare da nuna kin amincewa da sabon tsarin mulkin kasar da aka sanar kwanaki kadan da su ka gabata. Hikmata al-Hijri ya yi kira da gyara yadda ake tafiya a yanzu da kuma rubuta sabon tsarin mulki wanda zai zama yana wakiltar dukkanin bangarorin mutanen kasar. Shugaban na ‘yan Duruz ya bayyana cewa; sabon tsarin mulkin da aka gabatar yana nuni ne da mahangar wani bangare daya na al’ummar kasar, wanda kuma yake share fage na kafa tsarin kama-karya, maimakon kafa tsarin demokradiyya. Haka nan kuma ya ce, ko kadan ba a yi aiki da tsarin da zai kai ga kafa hukuma ba, sannan...
    A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri. A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, da kuma mayar da martani akan kisan kiyashin da abokan gaba ‘yan sahayoniya suke yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, sojojin Yemen sun kai hari da yardar Allah  akan sansanin sojan sama na Nivatim” da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri, mai suna “Falasdinu 2” sun bisa yardar Allah ya isa inda aka harba shi.” Sanarwar ta kuma ci gaba da...
    A jiya Talata ne dai kungiyar ta Jihadul-Islami ta kaddamarwa da al’ummar Musulmi  shahadar Naji Abu Saif, wanda ake yi wa lakbi da Abu Hamza, da ya kasance kakakin dakarun “Sarayal-Kudus” bayan da ‘yan sahayoniya su ka yi masa kisan gilla tare da iyalansa da iyalan dan’uwansa.  A bayanin da ta fitar, kungiyar ta Jihadul-Islami ta ce; Duniya ta yi sanayya da sautin shahidin wanda ya kasance sauti ne na gwagwarmaya da ba ya tsoron wani zargi akan tafarkin Allah, wanda kuma Allah ya yi wa baiwar fasahar zance da kuma jarunta da kare hakkokin al’ummarmu ta Falasdinu. Kungiyar ta kuma ci gaba da cewa,kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka yi wa Abu Hamza wani sashe ne na jerin...
    Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara na Jihar Ribas. Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa. An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau “Saboda haka duk wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin dimokuraɗiyya wanda kuma ya keta haddin cin gashin kan gwamnatocin jihohi,” in ji shi. A kan haka ne Ƙungiyar Lauyoyin ta buƙaci Majalisar Dokoki ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A karshe dai abin da wasu ke hasashen zai faru a Jihar Ribas ne ya faru inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar kuma ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa da kuma ’yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan wannan doka da shugaban kasar ya ayyana ne al’umma da dama ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyin kan wannan batu. A yayin da wasu ke bayyana cewa dama tuni abin da shugaban kasar yake bukata ke nan, wasu kuwa ke bayyana cewa shugaban kasar ma ba shi da ikon dakatar da zababben gwamna. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan DAGA LARABA: Asalin...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin da take mayar da martani ga tambayar da wani dan jarida ya yi mata a taron manema labaru na yau 18 ga wata cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra’ila,kuma tana fatan dukkan bangarorin za su sa kaimi ga ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata, da kaucewa daukar duk wani mataki da zai ta’azzara lamarin, da hana afkuwar bala’in jin kai a mataki mai girma. Hukumomin lafiya da ke Gaza sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare daban-daban a zirin Gaza da...
    Alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ko MIIT, sun nuna irin ci gaba bisa daidaito da sashen masana’antun dijital na kasar Sin ya samu a shekarar 2024 da ta gabata, inda a shekarar ta bara sashen ya samu karin kudin shiga da riba. Alkaluman da MIIT ta fitar a jiya Litinin, sun nuna a baran, sashen ya kudin da ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 35, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.9, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 5.5 bisa dari a shekara. Kazalika, jimillar ribar da sashen ya samar ta karu da kaso 3.5 bisa dari a shekara, inda ya kai yuan tiriliyan 2.7. Bugu da kari, a shekarar ta 2024, karin kimar hajoji da manyan...
    Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000.   A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba   A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram.   A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro.   Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya.   Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu   Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
    Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas. Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar. Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu. Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu....
    Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida. A wani jawabi da ya yi  ga alummar kasa ta kafafen yada labarai a ranar Talata, Shugaban kasan ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne sakamakon rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa  a jihar, ya kuma hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata kuma ya tauye wa jama’ar Jihar Rivers morar romon  dimokuradiyya. Shugaban kasan ya nuna damuwarsa kan “mummunan hali” da jihar ke ciki, wanda ya kara muni bayan rushewar ginin Majalisar Dokokin Jihar da gwamnan ya yi a ranar 13 ga watan Disambar...
    A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan. Idan ana batu na kirkira da amfani da fasahar zamani a duniya, to kowa ya san cewa kasar Sin ta yi zarra a wannan bangare. Haka kuma kowa ya san duk wani ci gaban da Sin take nema ko ta samu, tana yi ne domin jama’arta su kasance cikin walwala, shi ya sa ci gaban Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, ya game kowane bangare na...
    Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera ta hakimanci. Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani. Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi...
    Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar. Tinubu ya kuma ayyana Ete Ibas a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya
    Jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayyana cewa, masu zuba jari na kasashen waje suna kara “gano kasar Sin”, kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya samar da “kirkire-kirkire da damammaki” masu yawa a wasu fannoni. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Namibiya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, zai halarci bikin rantsar da shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Windhoek, a ranar 21 ga watan Maris. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wannan shi ne karo na biyu, a shekarar da ta gabata dukkanin ƙananan hukumomi a Nijeriya ta hannun jihohinsu sun samu tallafin buhun shinkafa miliyan ɗaya mai nauyin kilogiram 10. Don haka, a wannan shekarar ma muna sake yin makamancin na bara.”   Hashim ya yi tilawar cewa gidauniyar Dangote ta himmatu wajen samar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, tallafi a ɓangaren kiwon lafiya, gina ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i, da sauran tallafi ciki har da wanda gidauniyar ta yi a lokacin annobar Korona.   Ya ce tallafin dafawa ne kan ƙoƙarin da gwamnatocin jihohi ke yi wa al’ummarsu, ya yi fatan cewa shinkafar da suka kawo Bauchi ɗin za ta je kai tsaye ga waɗanda aka bayar domin...
    A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
    Ƙungiyar Hamas ta ɗora alhakin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar yau Talata a Zirin Gaza kan Amurka. A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce Amurka ce ke da “alhakin kisan gillar” da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai harin. Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza Sanarwar ta ce hakan ya “tona asirin ƙaryar da suke yi na iƙirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin. “Muna buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa na kama masu aikata laifukan yaƙi da masu goya musu baya,”...
    Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar. Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya. Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar. Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria...
    Kasar Sin na matukar adawa da haramta amfani da kirkirarriyar basira ta DeepSeek da gwamnatin Amurka ta yi a ranar Talata, biyo bayan rahoton da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar na cewa, ma’aikatar cinikayya ta Amurka ta haramtawa ma’aikata amfani da DeepSeek kan na’urorin da gwamnati ta samar musu. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana adawa da zuzuta batun tsaron kasa fiye da kima, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, cinikayya da fasaha. Mao ta kara da cewa, kasar Sin za ta kare hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze. Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara. Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen. Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a...
    Bayan shafe kwanaki 40 har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriy a(NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ba su sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa. Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan Fabrairun da ya gabata a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina. Wata 11 da tuɓe rawanin wasu sarakuna a Sakkwato Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata Wata majiya ta kusa da iyalansa ta ce bayan kai kuɗin, sai da aka shafe mako guda kafin ’yan bindigar...
    Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.” Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza. Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu. A lokacin yarjejeniyar, an yi musayar wasu fursunonin Isra’ila da Falsɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila. Sai dai har yanzu kimanin mutum 59 daga cikin fursunonin Isra’ila suna hannun Hamas, kuma ana zargin rabinsu sun mutu. Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta amince da harin da Isra’ila ta sake kai wa Gaza, inda ƙasashen biyu suka sha alwashin yaƙar Hamas, ‘yan tawayen Houthi...
    A yau Talata ce ake saran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump, kuma wannan shine zantawar shuwagabannin kasashen biyu tun shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kakakin Fadar Krimlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen zantawar shuwagabnnin biyu. Peskov ya kara da cewa tattaunawar tasu zai maida hankali ne kan yakin Ukraine da matsalolin da suke kewaye da yakin. Yau ita ce ranar da kasar Rasha ta hade yankin Cremear ga kasar Rasha, a shekara ta 2014. Kwace yankin dai ya jawo matsaloli da dama tsakanin Amurka da Rasha a lokacin.
    Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun ce sun  kaiwa wasu sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa duk a cikin sa’oi 48 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Yahyah Saree ya na fadar haka a safiyar yau talata, ya kuma kara da cewa sojojin kasar za su ci gaba da maida martani da kuma hana jiragen...
    Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar. Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya  Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma...
    HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne. Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujeru 54 na Hajj ga malamai da jami’an da za su jagoranci Alhazai don aikin Hajjin 2025. Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga wakilin Radio Nigeria a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujerun ne domin bai wa jami’ai  da malamai damar jagorantar Alhzan jihar a Najeriya da Saudiyya. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, wannan tsari da hukumar ta kirkiro shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar Jigawa.   Ya bayyana cewa, an zabi jami’an da malamai maza da mata daga  daga kananan hukumomi 27 na jihar...
    Tawagar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Nijeriya ta gayyaci sababbin ’yan kwallo takwas da za su wakilci kasar domin buga mata wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya na 2026. Tuni Super Eagles karkashin jagorancin sabon mai horaswa Eric Chelle, ta fitar da jadawalin ’yan wasa na farko da za su taka mata leda a wasannin neman gurbin da za ta take a watan Maris din nan da muke ciki. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza Daga cikin sababbin ’yan wasan da ta gayyato da ba su taba wakiltar Nijeriya ba, har da irin su Papa Mustapha da Ifeanyi Emmanuel Onyebuchi da...
    Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp