2025-04-25@14:19:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 39
«gyaran zuciya»:
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi. An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da...
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci. Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki. An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta...
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama. Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata...
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023. Juyin mulkin da sojojin sukayi a Nijar ya haifar da takaddamar diflomasiyya sosai tsakanin Nijar da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta a wannan karon. Batun mayar da hambararen shugaban Nijar Bazoum da kin lamuncewa juyin mulkin daga gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar ta ECOWAS, shi ne a sahun gaba a...
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya. Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki. Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa. Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba. An...
Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
(3).sinadare gyaran jiki: to anan fa matsalar take don gaskiya awannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kinsha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda anfison aga amarya acike baza ki gane dagaske nake ba sai kin zauna nan awaje namiji yagama tsaraki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji. Saboda haka koda bayanshi ma akwai wasu supplement dazasu kara miki kyau lokacin aurenki yakamata kinemo asalin original kisha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul sumul kamar su sukayi kansu ki gansu kamar alashe yanzu duk su suke sha shikuma gaskiya beda wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta...
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba. Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas. Ta ce, sun...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya ya tube shugaban kamfanin man fetur ta kasa NNPC Mele Kyari, da majalisar gudanarwansa, ya kuma maye gurbinsa ta Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga a safiyar yau Asabar a shafinsa X. Onanuga shugaba ya tube shugaban kamfanin na NNPC da majalisar gudanarwan sa wadanda aka nada su a cikin watan Nuwamban shekara ta 2023. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Kyara a matsayin shugaban kamfanin sannan ya sake nada shi a shekara ta 2023. Banda haka shugaba Tinubu ya nada Engineer Bashir Bayo Ojulari, a matsayin sabon shugaban kamfanin sannan da wasu yan majalisar gudanarwa 11. Sannan majalisar tana da Ahmadu Musa Kida a...
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a. Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel Akwasi Amankwaah, ya ce wannan cibiya na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar wajen rage yawaitar shan ƙwayoyi da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga masu buƙata. Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano A yayin bikin miƙa cibiyar, Dokta Amankwaah, ya jaddada aniyar ECOWAS na yaƙi da matsalar shan...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, da hauhawar farashin kayan abinci da man fetur, da bala’in yanayi, da kuma matsugunan jama’a, ya sa miliyoyin mutane ke fafutukar samun abinci mai gina jiki. Rahoton UNICEF ya kara bayyana cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Nijeriya, kusan miliyan 11, na fama da matsanancin rashin abinci, wanda hakan ya sa kashi 50 cikin 100 na ka fuskantar barazana ga...
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da kayayyaki. Daga bisani me kasar Sin ta yi? Ta samar da tunanin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, inda aka nanata bukatar ba sauran mutane damar jin dadin zaman rayuwa, matukar wani mahaluki na son samun zaman rayuwa mai inganci. Bisa wannan tunani ne, kasar Sin ta samar da jerin shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar mabambantan...
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa. Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya kasar na kashe kudaden yaran kasar da ba a kai ga haihuwarsa ba. “Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kudaden yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kudin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce....
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna. A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fara aikin kyautata na’urorin aiki da kuma maye gurbin tsoffin kayayyaki da sabbabi a bara. A bana kuma, an habaka wannan aiki zuwa harkar noma, inda za a mai da hankali wajen gyara da kyautata tsoffin manyan rumfuna masu aiki da hasken rana, da rumfuna na roba, domin karfafa tsarin kiyaye tsaro, da kara yin amfani da gonaki. Haka kuma, bisa wannan shiri, za a...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Wannan mataki ya zo ne saboda yadda ayyukan hukumar ke jan hankali, inda sau da yawa ake samun saɓani tsakaninta da wasu. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala ne, ya bayyana cewa an yi wannan dokar gyara ne don daidaita harkokin ɗaukar fina-finai da kare addini da al’adu. Ya ce daga yanzu...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin da ke da nufin kusantar da jama’a ga gwamnati, zai kuma tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen da aka aiwatar sun dace da muradin al’umma. Don haka Namadi ya yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka rungumi ayyukan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa hannu bibbiyu, tare da yin alwashin ci gaba da samar da ingantattun ayyuka. Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, zai yi nazarin...
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya baki daya, wanda ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin bunkasa ayyukan da suka shafi kwamfutar quantum. A cewar cibiyar nazarin injiniyan kwamfutar quantum ta Anhui, masu amfani daga kasashe ko yankuna 139 sun samu damar shiga Origin Wukong, tare da Amurka, Rasha, Japan da Kanada a matsayin mafi yawan yin amfani da ita. A cikin wadannan kasashe, Amurka ce ke kan gaba a...
Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa. Kuma, kamfanonin kasashen biyu sun samu sabon ci gaba a bangaren makamashin gas da man fetur. Tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da asusun kasar Kazakhstan na Samruk Kayzana da kungiyar ‘yan kasuwar kasar ta Atamekeh a Astana hedkwatar kasar Kazakhstan, tare da gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin ‘yan kasuwar kasashen biyu da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa 8, wadanda ke shafar bangaren makamashin...
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya. Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi. Yawancin ’yan majalisar...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a fara yi wa gwajin. A watan da ya gabata, gwamnatin mista Prabowo ta fara bai wa miliyoyin yara ƴan makaranta da kuma mata masu ciki abinci kyauta domin rage rashin abinci mai gina jiki da ke shafar yaro ɗaya cikin biyar a Indonesia.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da likitoci da malaman kimiyya ke bayarwa a makarantu. Sin Ta Yi Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Hallaka Yayin Kisan Kiyashin Birnin Nanjing Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA). Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo. Jami’ar Jihar Kano mai kula da ofishin PCN Kano Pharmacist Hasiya Abubakar Ladan ce ta jagoranci tawagar da suka kai ziyarar. Wannan ziyarar wani mafari ne na tantancewa da wata tawagar kwararru daga hedikwatar PCN ta kasa da ke Abuja. Ta bayyana cewa ziyarar na da nufin tantance yadda DMCSA ke bin ka’idoji, don ba da Takaddar Rijistar wuraren sayarda magunguna. Pharmacist Ladan ta yabawa shugabannin DMCSA bisa...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya. Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu. NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa Daraktan cibiyar Salama Centre da ke Asibitin Gambo Sawaba ƙofar Gayan Zariya, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa Wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne hukumar ‘yan sanda da ke Kasuwar Mata a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025. Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin. Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...